Bushewar al'aurar mata: Abubuwan da ka iya haddasa bushewar gaban mata

Ọtụ nwaanyị

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Uche Akolisa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Igbo, Lagos

Bayan shafa ta tsanaki, al'aurar mace na fara kumbura domin nuna shiryawa ko amincewa da sabon sakon da aka aike mata, hakan na sanya mahaifa ta share hanya yayin da miji da mata ke karasa sauran aikin.

Sai dai a rayuwar wasu matan, namiji na sama da kasa, yayin da macen ke tunanin bai ma fara jima'in ba, saboda jikin matar ya bushe, babu sakewa kamar yadda ya kamata, bare kuma gamsuwa.

Kamar yadda Dakta Jospeh Akinde, wani kwararren likitan mata a Najeriya ya shaida wa BBC, cikin abubuwan da ke janyo hadarin kamuwa da cutar mantuwa akwai: rashin lafiya, yawan fargaba, gazawar zuciya, aikin karfi, da kuma rashin shawa'ar jima'i da sauransu.

A wannan makala, mun yi nazari kan abubuwan da ka iya haddasa bushewar al'aurar mata:

1. Cututtuka, ko yadda za a magance su

Dakta Akinde, mamallakin asibitin Livingspring da ke Ejigbo, a birnin Lagos, ya ce ta yiwu mutum ya kamu da cutar da ake samu ta hanyar jima'i wadda ake kira 'sexually transmitted infections' a turance, ma'ana 'Cutar da ake dauka yayin jima'i''.

Ya kara da cewa amfani ko shan magungunan kamar na cutar Kansa ko maganin tsananin damuwa, ka iya janyowa mace bushewar gaba.

2. Ko yana da wata illa?

Matar da aka yi wa fyade, ko wadda aka yi wa kaciya, za ta fuskanci matsalar bushewar gaba idan tana tasawa.

Dakta Akinde ya yi karin bayani, "Idan ta fuskanci wata matsala ta cin zarafi kamar fyade, ko kaciya, zai yi wuya ta daina fitar da wani ruwa a lokacin da ake saduwa da ita."

3. Zuciya ba ta farin ciki

Nwoke na nwaanyí

Asalin hoton, Getty Images

" Mace na iya shiga damuwa da rashin farin ciki idan ba ta son a yi jima'i da ita, amma babu yadda ta iya sai ta mika wuya ga mijinta saboda alhakin gamsar da sha'awarta ya rayata a wuyan matarsa ta aure."

3. Karfin amfani da wata hanya domin magani

Da yake bayani kan batun yadda mata ke samun kansu cikin wahala, Dakta Akinde ya ce, "Zai iya kasancewa ya gaji, dawowarsa kenan daga wurin aiki, ya kuma dade a cunkoson ababen hawa na tsawon sa'o'i, ko kuma ba shi da lafiya."

4. Babu ' lokacin daukar ciki '

Wannan shi ne lokacin da kwayayen mace ke budewa su fito daga cikin mahaifar mace, tana jiran fadawar ruwan maniyyi, wanda ke faruwa a rana ta 14 gabannin fara jinin al'ada.

Amma a wasu lokutan, wasu matan ba su cika gane lokacin da mahaifar ke shirin karbar ajiya ba, A nan Dakta Akinde ya ce hakan zai iya sanyawa gaban mace ya bushe a lokacin da namiji ke saduwa da ita.

Sannan cutuka kamar wadanda ke shafar kwayayen mace da ake kira polycystic ovary syndrome ko (PCOS) a turance, ka iya janyowa mace shiga halin kila-wa-kala na rasa lokacin daukar ciki.

5. 'Daukewar jinin al'ada'

Úmúnwaanyí

Asalin hoton, Getty Images

Kafar sadarwa ta inter Webmd mai bayani kan fannin kiwon lafiya, ta yi bayanin daukewar jinin al'ada ga mace da kaciya na haddasa wa matan bushewar gaba.

"Bushewar gaban mace alamomi ne na daukewar jinin al'ada, kuma yawancin mata na samun wannan matsalar da zarar lokaci ya yi, wanda ya fi zuwa a shekarun girma.''

6. Ban san yadda zan yi ba

Kwararru sun bayyana cewa a wasu lokutan, yawancin maza ba sa bukatar taba al'aurarsu saboda a zahiri lafiya kalau suke suna kuma yin jima'in yadda ya kamata, wasu kuma ba su san yadda za su fahimci karbar da jikinsu ya yi wa lamarin ba.

7. Lokacin shayarwa

Nwaanyí na-enye nwa ara

Asalin hoton, Getty Images

Matar da ba ta jima da haihuwa ba, kuma take shayar da jaririnta, ka iya fuskantar matsalar bushewar gaba a tsawon lokacin da ta dauka na shayarwa.

Sannan yawancin matan da ke shayarwa suna samun kansu a cikin tunanin ko dai sun fara shiga lokacin da jinin al'adarsu zai dauke.

Wannan yana da nasaba da ruwan nonon ne yake dauke sinadarin estrogen da ke aikawa da sako tare da sanyawa gaban mace laima-laima.

Tserewa

Dr Joseph Akinde

Asalin hoton, Dr Joseph Akinde

Kamar yadda likitocin mata suka bayyana, yana da muhimmanci a yi bincike domin gano matsalolin da ke haddasawa mata bushewar gaba, da magance ta.

"Idan cuta ce, yana da muhimmanci a magance ta," in ji Dakta Akinde.

A cewarsa: "ian tashin hankali ne ke haddasawa, lallai ya kamata a gana da likitan sanin halin dan adam domin neman shawarwari."

"Idan kuwa an yi wa mutum kaciya ne, babu wata mafita face sayan man nan mai yauki da ke sanya sulbin gaba a lokacin jima'i, wato 'lubricant' a turance."

Ya ce idan an yi wa mace kaciya, za ta iya amfani da itrin man domin saukaka mata domin magance matsalar bushewar gaban.

Har wa yau, kwararru suna bai wa maza shawarar su tabbatar matansu sun yi fitsari kafin jima'i, sannan su tsawaita lokacin wasa da su domin saukaka wa gabansu da kaucewar bushewarsa.