Abin da ya sa mata suka fi fuskantar haɗarin mutuwa idan likitoci maza suka yi musu tiyata

Tam Duc Cardiology Hospital in Vietnam.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Cagil Kasapoglu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Ku yi tunanin likita a zuciyarku, ya ko ta shirya tsaf domin yi muku tiyata.

Shin kuna tunanin namiji ne ko mace?

Idan ke mace ce, ya kamata ki yi tunanin wata likitar da kika saba da ita sosai. Wataƙila hakan ya ceci rayuwarki.

Hakan kuwa da na alaƙa da cewa kashi 32 na mata sun fi fuskantar hadarin mutuwa idan likitoci maza suka yi musu tiyata, saɓanin a ce idan mata ne suka yi musu tiyata, kamar yadda wani rahoto na baya-bayan nan ya gano.

Duk da cewa jinsin mai yin tiyatar ba shi da wani tasiri na a-zo a-gani, binciken ya gano cewa, mata sun fi haɗarin fuskantar matsaloli bayan tiyata, har ma a sake kwantar da su a asibiti cikin kwanaki 30 idan namiji ne ya yi musu tiyata. To amma me ya sa hakan?

Mutumin da ya jagoranci binciken (wanda aka buga a mujallar lafiya ta JAMA Surgery), Dokta Christopher Wallis ba shi da tabbacin me ke kawo hakan.

Ya shaida wa BBC cewa har yanzu ba su da gamsassun bayanai kan sakamakon binciken, amma suna aiki a kai.

Hakan ta sa muka tambayi likitoci mata da dama don jin ra'ayinsu kan abin da zai sa mata su fi tsira a hannunsu.

Tunanin jin raɗaɗi

Binciken ya yi nazari kan marasa lafiya fiye da miliyan ɗaya da dubu ɗari uku da likitoci 2,937 a birnin Ontario na Canada, daga 2007 zuwa 2019.

An yi da'awar cewa shi ne "bincike na farko da ya duba dangantaka tsakanin jinsin likita da fahimtar juna da ake samu tsakanin likita da mara lafiya da kuma sakamakon tiyata".

Dr Oneeka Williams

Asalin hoton, EMERSON HOSPITAL

Bayanan hoto, "Maza suna ganin mata sun fi zumudi don haka ba sa mayar d hankali sosai a kan korafe-korafen da ake yi bayan an yi tiyata," a cewar Dr Oneeka Williams

Wani dalili da ke cikin binciken da kuma zai iya bayani kan sakamakon binciken shi ne cewa, akwai bambanci mai yawa kan yadda - likitoci maza ke ɗaukar jin raɗaɗi - ta yadda suke ganin mata sun fiye raki.

Dokta Oneeka Williams, wata likitar mafitsara ce a jami'ar Tufts bangaren koyar da likitanci a Boston da ke Amurka na da wannan ra'ayi.

"Ina tunanin akwai halayyar maza ta yin watsi da ƙorafin mata. Suna da tunanin cewa mata sun fiye ragwanta da raki da zuzuta abin da bai kai ya kawo ba, don haka ba su fiya mayar da hankali kan ƙorafe-ƙorafensu ba. Sai a yi watsi da ƙorafi, su ce ba wani zafi na a zo a gani sannan su ce ba wani raɗaɗi," kamar yadda ta shaida wa BBC.

Halayya

Dr Nancy Baxter, wata ƙwararriyar likitar hanji da uwar-kashi a asibitin koyarwa na Michael dake jami'ar Toronto na da ra'ayin cewa "mutane ba su fiya mai da hankali da raɗaɗi a jikin maza ba kamar yadda suke mayar da hankali kan raɗaɗi da jikin maza, " amma ta ce watakila akwai wasu dalilan kuma.

Dr Nancy Baxter

Asalin hoton, Unity Health Toronto

Bayanan hoto, "Idan mutane suka yi tunani a kan tiyata, suna tunanin maza ne," a cewar Dr Nancy Baxter daga Jami'ar Toronto

"Idan ka ga mara lafiya, wane irin mataki za ka ɗauka a matsayinka na likita? wa za ka kai ɗakin tiyata? Akwai yiwuwar cewa a samu bambanci tsakanin jinsin likitoci wajen yadda suke mu'amala da marasa lafiya maza da mata," kamar yadda ta shaida wa BBC.

Ta ambato wasu bayanin da ke nazari kan marasa lafiyar da ke fama da matsalolin zuciya da ke nuna cewa likitocin zuciya mata sun fi tarairayar mata masu matsalar zuciya, abin da ke sa a samu ingantaccen sakamako.

Tattaunawa

Wani muhimmin dalilin shi ne yiwuwar irin "kaifin basirar tarairayar mara lafiya, da tausayawa da kuma dabarun tattaunawa da mata ke da su", kamar yadda Dokta Williams ta bayyana.

Dokta Kim Templeton, kwararriyar likitar ƙashi ce da ke aiki a jamui'ar koyar da aikin likita ta Kansas ta amince cewa yadda likitoci mata suke tunkarar marasa lafiya maza zai iya taimakawa wajen bayyana bambancin.

Binciken da aka yi a baya sun nuna cewa dangantaka tsakanin marasa lafiya da likita da kuma tattaunawa tsakaninsu za ta iya samun matsala idan mara lafiyar mace ce, sannan likitan kuma namiji ne.

Dr Jennifer Svahn

Asalin hoton, Dr Jennifer Svahn

Bayanan hoto, Dr Jennifer Svahn, likitar hanji da uwar-kashi, ta ce likitoci maza da ke tiyata ba su cika mayar da hankali kan korafe-korafen mata marasa lafiya ba

'An jima ana fuskantar nuna wariyar jinsi a fannin'

An jima ana fuskantar nuna wariyar jinsi a fannin - likitanci - da da maza suka mamaye kuma yana iya zama wani dalili da ya sa mata ke barin aikin na likita.

A shekarar 2015, mata likitoci sun shiga Tuwita don kalubalantar matakin, ta hanyar ƙaddamar da wani maudu'i mai taken "#ILookLikeaSurgeon". Har yau ana tura saƙwanni da dama kan yadda ake kuskuren ɗaukar cewa mata suna wani aikin ne na kula da lafiya amma ba likitanci ba.

Dokta Williams ta ce ana yawan tunawa mata likitoci cewa su mata ne fa.

"Mafi yawan marasa lafiya da ma'aikata na ɗaukar cewa ni ba likita ba ce," kamar yadda ta bayyana. "Abin da aka fi ɗauka shi ne mai taimakawa likitoci ce, ko sakatariya, ko mai kula da harkar abinci, idan kuma na yi sa'a a ɗauke ni a matsayin malamar jinya."

Two surgeons in an operating theatre during a hysterectomy.

Asalin hoton, Getty Images

Rashin daidaito na jinsi

Yayin da jagoran binciken Dokta Wallis ya jaddada cewa binciken na Ontario ya nuna abin da ke faruwa a cikin al'umma, amma ba yana nuna cewa mace mara lafiya za ta fuskanci matsala ba idan likita namiji ya duba ta, binciken ya kuma nuna ainihin abin da ke faruwa a ɓangaren kula da lafiya.

Karancin mata a fannin kula da lafiya shi ma wani abu ne mai zaman kanasa, kamar yadda Dokta Svahn ta bayyana.

"Idan da gaske ne cewa mata marasa lafiya sun fi gamsuwa idan likitoci mata suka duba su, to akwai buƙatar samar da ƙarin mata likitoci a duka ɓangarorin kula da lafiya kuma ya zama matan za su iya samun kai wa gare su."

Fiona Myint, mataimakiyar shugabar kwalejin kula da lafiya ta Royal College of Surgeons of England ta ce akwai buƙatar ƙara ƙoƙari wajen daidaiton jinsi tsakanin likitoci.

A Birtaniya maza sun fi mata zaɓar samun horo a matsayin ƙwararrun likitocin tiyata. A karon farko matan da ke neman ƙwarewa a likitancin fiɗa suna kai wa kashi 41, amma kashi 30 kawai suke kai wa manyan masu samun horo, sannan kashi 14 kuma suka zama ƙwararru," kamar yadda ta faɗa.

Irin waɗannan matan da ba tsayawa mai yiwuwa suna fuskantar wariyar jinsi a wajen aiki - Dokta Williams ta ce kusan haka ta ringa fuskanta a kowace rana.

Magance matsalar wariyar jinsi zai zama babban mataki mai muhimmanci wajen samun ƙarin mata dake zama likitocin tiyata, da kuma gamsar da su cewa su tsaya.

A yanzu dai, alamu na nuna cewa Dokta Baxter ta yi daidai da ta ce "idan mutane suka yi tunanin likitoaicn fiɗa, to suna tunanin maza ne."