Likitan da ke yi wa mata tiyata ba da izininsu ba a Amurka

Dr Javaid Perwaiz

Asalin hoton, Western Tidewater Regional Jail

Bayanan hoto, Ana tuhumar Dr Perwaiz da laifin yin bayanan karya da almundahana a harkar lafiya

Wani likita da ake zargi da yi wa mata tiyata ba gaira balle dalili, ya bayyana a gaban kotu da ke Virginia a Amurka.

Hukumar tsaro ta FBI ta ce Dr Javaid Perwaiz, likitan mata ne da yake shara musu karya kan yanayin lafiyarsu daga nan ya janyo musu jin mummunan rauni wajen aikin tiyata.

Sama da mata 126 ne suka shigar da korafi akan likitan tun daga ranar 8 ga watan Nuwamba da aka cafke shi.

A ranar Alhamis alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Dr Perwaiz a gidan kaso, har sai an kammala shari'ar.

Ana tuhumar Dr Perwaiz mai shekara 69, da laifin yi wa marasa lafiya bayanan karya da almundahana a harkar lafiya.

Kamar yadda takardar sammacin kama shi da hukumar FBI ta aike ta bayyana, yana yi wa marasa lafiya tiyata ba tare da izininsu ba, inda daga bisani yake janyo musu mummunan rauni.

Cikin tiyatar da yake musu ta hada da wadda ta shafi mafitsara, da mahaifa da sauransu, kuma likitan yana aiki a asibitoci biyu a Chesapeake da Virginia, yana kuma da damar kwantar da marasa lafiya a wasu karin asibitocin a kasar Amurka.

Kamar yadda korafin ya nuna, daga shekarar 2014 zuwa 2018, Dr Perwaiz ya yi wa kashi 40 cikin 100 na matan da ya ke dubawa tiyata a asibitin gwamnati karkashin inshorar lafiya.

Cikin wadannan mata 510, kashi 42 cikin 100 ya yi musu a kalla tiyata sau biyu.

Hukumar FBI ta fara samun korafin ne a watan Satumbar bara, a lokacin da ma'aikatan asibitin da likitan ke aiki suka samu korafi daga marasa lafiya.

Wata maras lafiya ta yi korafin ya cire mata kwayayen haihuwa, tare da taba mata mafitsara, lamarin da ya sanya ba lallai ta kara daukar ciki ba.

Ita ma wata matar ta daban, ta yi wa hukumar FBI korafin likitan ya yi mata tiyatar da ta taba mata mahaifa, alhalin ba ita ce ainahin tiyatar da ya ce zai mata ba kuma sai da ta dauki makwanni uku a asibiti kafin aka sallameta.

Jami'in hukumar FBI Desiree Maxwell da ya rubuta sammacin ya ce "Ganau sun zargi Perwaiz da amfani da cutar kansa wajen tsorata marasa lafiyar, cikin firgici suke amincewa da yi musu tiyatar.''

BBC ta tuntubi lauyan Dr Perwaiz, Lawrence Woodward Jr sai dai bai ce komai uffan ba kan batun.

Dr Perwaiz dai ya yi karatun zama likita ne a kasarsa ta gado wato Pakistan, ya kuma samu izinin aikin lkita a Virgina a shekarar 1980, masu gabatar da kara sun ce an sha gurfanar da shi gaban kwamitin ladaftarwa kan zargin rashin da'a.

Ko a shekarar 1982 an haramta masa shiga asibitin Maryland, kan laifin da ya shafi rashin gaskiya kan lafiya. A baya kungiyar likitocin Virgina sun taba tuhumarsa da yi wa marasa lafiya tiyata ba tare da yin binciken da ya dace da kuma amincewar wadanda lamarin ya shafa.

Har ila yau, a shekarar 1996 an karbe masa lasisin aiki sakamakon laifin kaucewa biyan haraji amma bayan shekara biyu ya koma ya ci gaba da aiki.