Zaɓen Anambra: Abu biyar da suka sa yake da muhimmanci

    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja

Al'ummar Jihar Anambra sun shirya tsaf domin kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen gwamna ranar Asabar 6 ga Nuwamban 2021. Sai dai abubuwan da suka biyo bayan shirin zaɓen sun sha bamban da abin da aka saba gani.

Ɗaya daga cikin abubuwan da ake tattaunawa a kansu shi ne ko masu zaɓe da yawa za su fito kaɗa ƙuri'a saboda matsalolin tsaron da ke addabar yankin baki ɗaya sakamakon barazanar da ƙungiyar IPOB mai fafutikar kafa ƙasar Biafra ta yi na hana gudanar da zaɓen.

Duk da cewa IPOB ta janye barazanar hana gudanar da zaɓen, ta yi barazanar ce tun farko tana mai neman har sai an sako jagoranta Nnamdi Kanu da ke fuskantar shari'a bisa zargin haddasa fitina da cin amanar ƙasa.

Muhimmancin zaɓen ya sa idon duniya ya karkata kan jihar da ke kudu maso gabashin Najeriya, ciki har da Amurka wadda ta yi barazanar ɗaukar mataki kan "duk wanda ya tayar da fitina ko saka fararen hula cikin tashin hankali a lokacin zaɓen da kuma bayan zaɓen".

Hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC, ta jaddada aniyarta cewa "dole ne a gudanar da zaɓe a ranar Asabar".

APC da PDP na kokawar ƙwace mulki

Jam'iyyun siyasa mafiya girma a Najeriya su ne APC mai mulki da kuma PDP, sai dai ba su ne ke mulkin Jihar Anambra ba.

Jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta shafe shekara 19 tana mulkin Anambra, inda ta fara a 2005.

A ranar 23 ga watan Yuni ne aka bayyana tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Charles Soludo a matsayin ɗan takarar APGA sannan kuma gwamna mai-ci Willie Obiano ya ba shi tutar takara ranar 25 ga Satumba.

Hakan na nufin zai fafata da Valentine Ozigbo na Jam'iyyar PDP da Andy Uba na Jam'iyyar APC. Kazalika, akwai wasu da ake ganin za su taɓuka a zaɓen kamar Obiora Okonkwo na Zenith Labour Party (ZLP), da Ifeanyi Uba na YPP.

Ana ganin APC da PDP za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun ƙarfafa ikonsu a yankin na kudu maso gabas mai fama da rikici ta hanyar lashe zaɓen Anambra.

Idan PDP ta yi nasara za ta samu iko da jiha 12 a faɗin Najeriya, yayin da APC za ta samu 17 idan ta yi ci zaɓen.

An tura dubun-dubatar 'yan sanda

Kamar yadda aka saba gani a zaɓukan gwamna a Najeriya, rundunar 'ya sandan ƙasar ta tura dubban jami'an tsaro Jihar Anambra.

Jumullar 'yan sanda 34,000 rundunar ta yi alƙawarin turawa, kamar yadda Babban Sufeto IGP Usman Alkali Baba ya bayyana a watan Oktoba.

Adadin ya zarta na wanda aka tura Jihar Edo na 'yan sanda 31,000 a zaɓen gwamna na 19 ga Satumban 2020 da kuma 33,783 da aka tura Jihar Ondo a zaɓen ranar 10 ga Oktoban 2020.

Kazalika rundunar za ta kasance ƙarƙashin Muƙaddashin Babban Sufeto (DIG) biyu da Mataimakin Babban Sufeto (AIG) biyar da su ma aka tura Anambra ɗin. Sa'annan, akwai kwamashinan 'yan sanda 14 da mataimakan kwamashina 31.

IPOB ta hana 'yan siyasa da mutane sakat

Tuni tashe-tashen hankali ya sa mazauna Anambra suka shiga fargaba game da zaɓen na Asabar.

Cikin wata shida da suka gabata, jihar ta fuskanci tashin hankali iri-iri da suka haɗa da kisan manyan mutane ciki har da 'yan siyasar da ke shirin fafatawa a zaɓen.

A watan Oktoba ne ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) ta ayyana cewa za ta saka dokar zama a gida daga 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba, abin da ke nufin ba za ta bari a yi zaɓen na 6 ga wata ba. Sai dai a ranar Alhamis ta bayar da sanarwar janye umarnin.

"Wannan (janye umarnin) ba shi da alaƙa da jamia'n tsaro da aka kawo Anambra, kawai dai mun yi abin da manyanmu suka buƙaci mu yi ne," kamar yadda ƙanin Nnamdi Kanu mai suna Emanuel Kanu ya shaida wa BBC Hausa.

Kafin haka, ƙungiyar ta ayyana kowace Litinin a matsayin ranar zaman gida da zummar girmama jagoran nasu Nnamdi Kanu har sai an sako shi. Hakan ya tilasta wa gwamnatin jihar mayar da Asabar cikin ranakun karatu ga ɗalibai a jihar a madadin Litinin ɗin.

Kazalika 'yan siyasa sun guji fita tarukan yaƙin neman zaɓe don gudun kai musu hari.

Bayanai kan masu jefa ƙuri'a

  • Akwai ƙaramar hukuma 21
  • Anambra na da rumfunan zaɓe 5,720
  • Mutum 2,525,471 ne ke da rajistar zaɓe

Gwamna mace ta farko

Anambra ce jiha ɗaya tilo a Najeriya da ta taɓa samun mace a matsayin gwamna.

A watan Maris ne 2006 ne Mataimakiyar Gwamna Dame Virginia Ngozi Etiaba mai shekara 64 a lokacin ta zama gwamnan Anambra biyo bayan tsige Gwamna Peter Obi.

Duk da cewa jam'iyyunsu ba sa cikin na gaba-gaba a zaɓen, 'yan takara shida daga cikin 18 mata ne da ke fafatawa. Saboda haka, idan ɗaya daga cikinsu ta yi nasara ba za a yi mamaki ba.

Cibiyar gwagwarmayar Biafra

An fara gwagwarmayar kafa ƙasar Biafra tun shekarar 1967, abin da ya jawo yaƙin basasa na shekara uku ƙarƙashin jagorancin Odumegwu Ojukwu.

Tun daga wancan lokaci, Anambra ta samar da 'yan siyasa da 'yan boko da ke gwagwarmayar kafa Biafra da dama, ciki har da Mista Ojukwu wanda ya fito daga garin Nnewi.

Daga cikin shugabannin da jihar ta samar a siyasar Najeriya akwai Nnamdi Azikiwe a matsayin shugaban Najeriya na farko daga 1963 zuwa 1966.

Kazalika akwai Alex Ekwueme, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa daga 1979 zuwa 1983.