Abin da ya sa allurar riga-kafin korona miliyan 241 za su yi kwantai

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Biden na masaukin baki a wani taron koli kan cutar korona ranar Laraba inda zai bukaci shugabannin kasashen duniya su dau alwashin yi wa kashi 70 cikin dari na mutanen duniya riga-kafin cutar nan da watan Satumbar shekara mai zuwa.
Sai dai bincike ya nuna cewa kasashe masu arziki na da rarar riga-kafin, kuma karshenta sai zubar da su za a yi yayin da wasu kasashen ba su yi wa ko kashi 2 cikin dari na al'ummarsu riga-kafin ba.
Da za ta hau jirgi zuwa Iran a wannan bazarar, Bahar ta zaku ta ga mahaifinta a karon farko cikin shekaru hudu.
Ba ta da masaniyar cewa cutar korona na daf da kai wa kasar farmaki - da iyalinta - a karo na biyu da cutar ta bullo.
Da farko, wata kawarsu ce, wadda ke shirin bikin danta lokacin da ta fara rashin lafiya. Ba a jima ba ta rasu.
Sai kuma kawun mahaifinta, da goggonta. Bahar ta damu matuka kan kakarta wadda aka yi wa allurar farko kawai kuma tana jira a yi mata ta biyun.
Bahar mai shekaru 20 kuma ta ke zaune a Amurka ta yi riga-kafinta a Afrilu.
Duk da cewa tana da 'yar kariya, ta kebe kanta a ranakun karshe kafin tafiyarta a gidan mahaifinta cikin damuwa kan wa cutar za ta kuma kamawa.
Wasu daga cikin 'yan gidansu sun yi allurar a kasar da riga- kafin ba ta da yawa.

Asalin hoton, Bahar
Lokacin kadan bayan ta koma Amurka, ta gano cewa mahaifinta ba shi da lafiya. Ga shi ta yi nisa, sai ta shiga fargaba.
Mahaifin nata ya warke amma da yawa daga 'yan uwanta masu shekaru ba su warke ba.
Rashin daidaiton samar da allurar ya yi yawa. Kusan rabin mutanen duniya ba su riga sun yi ko da allurar farko ta riga-kafin ba.
A cewar kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch, kashi 75 na riga-kafin korona sun isa kasashe 10.
Cibiyar bincike ta Economist Intelligence Unit ta bayyana cewa rabin duka rigakafin da aka samar ya zuwa yanzu an bai wa kashi 15 cikin dari na mutanen duniya, mutanen da ake yi wa rigakafin a kasashe masu arziqi sun ninka yawan mutanen da ake yi wa a kasashe masu tasowa.
A watan Yuni ne kasashe masu karfin tattalin arziki na G7- Kanada, da Jamani, da Faransa, da Itali, da Japan, da Birtaniya, da kuma Amurka sun yi alkawarin ba da allurar riga-kafi biliyan daya ga kasashe masu fama da talauci a cikin shekara me zuwa.
"Na yi murmushi da na ga hakan," in ji Agathe Demarais, jagorar tawagar wani rahoto na baya-bayan nan kan allurar riga-kafin cutar cibiyar bincike ta Economist Intelligence Unit kuma tsohuwar jami'ar diflomasiyya.
"Na sha ganin irin wannan dayawa. Kun san ba zai taba faruwa ba."
Burtaniya ta yi alkawarin miliyan 100 na riga-kafin, ya zuwa yanzu ta ba da gudummuwar kasa da miliyan 9.
Shugaba Biden ya yi alkawarin miliyan 580 wanda daga ciki Amurka ta bayar da miliyan 140 zuwa yanzu.
Kuma kungiyar EU ta yi alkawarin riga-kafin miliyan 250 zuwa karshen wannan shekarar - ta aika kimanin kaso 8 cikin dari na wannan.
Kamar sauran kasashe masu tasowa, Iran ta saya alluran rigakafi daga Covax, shirin duniya wanda Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ke tallafa wa don samun allurai a inda aka fi bukata.
Shirin Covax na sayen allurar sannan ya sayar da ita kan farashi mai sauki ga kashashe masu tasowa sannan su ba da gudummowarta ga kasashe masu fama da talauci.
Amma shirin Covax din ya fuskanci babbar matsalar wadata.
Shirin ya tsara rarraba allurai biliyan biyu a cikin 2021 inda mafi yawansu za a samar da su ne daga wani kamfani na Indiya, sai dai lokacin da annobar ta sake bulla a karo na biyu ta gurgunta Indiya a watan Mayu, gwamnati ta sanya dokar hana fitar da kaya.
Tun daga wannan lokacin Covax ya dogara da alluran da kasashe masu arziqi suka bayar.
Sannan kuma samar da kayan ya samu jinkiri, har yanzu wasu daga cikin kasashen da ke karbar ba su yi wa kaso 2 na yawan mutanen su allurar rigakafin ba.
Ba matsalar samarwa a duniya ba ce. Kasashe masu arziki su na ta tara allurar rigakafin, a cewar Airfinity, kamfanin nazarin kimiyya da ke binciken samar da allurar a fadin duniya.
Masu samar da allurar suna samar da guda miliyan 1.5 a kowane wata, za su samar da biliyan a karshen shekara.
"Suna samar da adadi mai yawa. Adadin ya karu sosai cikin watanni uku zuwa hudu da suka gabata," a cewar Dokta Matt Linley babban mai bincike a Airfinity.
Kasashe masu arziki na iya samun allurar biliyan 1.2 da ba sa bukata, ko da kuwa sun fara yi wa mutane allurar da za ta inganta ta farkon.
Kashi biyar na wadannan alluran rigakafin miliyan 241 na iya yin kwantai idan ba a ba da su da wuri ba.
Watakila kasashe masu fama da talauci ba za su iya karbar allurar ba, sai idan saura a kalla wata biyu kafin su lalace.

Asalin hoton, Getty Images
"Ba na tunanin kasashen masu arziqi sun yi hadama ne, na fi ganin cewa kawai don ba su san wadanne alluran ne za su yi aiki ba," in ji Dr Linley. "Don haka sai suka sayi da yawa."
Cikin sabon binciken da ya gudanar, kamfanin Airfinity ya na fatan ya nuna wa gwamnatoci cewa akwai wadataccen allurar rigakafi kuma ba sa bukatar tarawa da yawa.
Maimakon haka za su iya ba da gudummawar abin da ba sa bukata, sannan kuma su kasance da kwarin gwiwa cewar za a samar da karin allurai a cikin watanni masu zuwa.
Gwamnatin Birtaniya ta ce ba ta da tarin allurar riga-kafi kuma ta kulla yarjejeniya da Austreliya don raba allurai miliyan hudu wanda za a dawo da su daga kason da aka ware wa Austreliyar a karshen shekara.
Ga Bahar da iyalinta, wadannan babban al'amari ne. Bayan ko wadanne 'yan kwanaki, ta kan ji labarin wani da ya rasa ransa.
Lokacin da abokanta na jami'a su ka ce ba sa so su yi allurar riga-kafin, ta kan yi musu da su amma a yanzu ta daina, saboda ranta na baci.










