Rashin Tsaro: Jerin sace-sacen dalibai da aka yi a wasu makarantu a Najeriya

Hare-haren da ake kai wa makarantu ana sace dalibai a arewacin Najeriya ya fara zama ruwan dare a kasar.

Hari na baya-bayan nan da aka kai shi ne na wata makaranta a Maradun da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriyar.

Sai dai a yayin da aka ceto da yawa daga daliban makarantun da aka yi sace-sacen, har yanzu akwai na wasu makarantun da ke hannun 'yan bindigar.

Ga dai jerin sace-sacen daliban da aka yi a kasar.