Afghanistan: Za a sake kai hari a filin jirgin saman Kabul - Joe Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar sake kai wani hari a filin jirgin saman Kabul na kasar Afghanistan.

Ya ce kwamandojinsa sun sanar da shi cewa an kitsa kai wani hari wataƙila ma yau Lahadi.

Duk da haka Amurka na ci gaba da aikin kwashe mutanenta kafin wa'adin da aka aminta da ƙungiyar Taliban ya cika ranar Talata.

Tun da farko Birtaniya ta bayyana kammala jigilar sojojinta daga Kabul da ma sauran ma'aikatan diflomasiyyarta.

Ana fargabar sake faruwar irin harin ƙunar baƙin wake da aka kai ranar Alhamis a filin jirgin na Kabul, wanda ya kashe mutum 170 da suka haɗa da sojojin Amurka 13.

Ƙungiyar IS-K mai mubaya'a ga uwar ƙungiyar IS da ke adawa da Taliban ce ta ɗauki alhakin kai harin.

Sai dai a martanin da ta mayar, Amurka ta kai hari da jirgi marar matuƙi gundumar Nangahar da ke gabashin Afghanistan ranar Juma'a, inda ta kashe wasu ƙusoshin IS-K da ta ce su ke kitsa wa ƙungiyar yadda za ta kai hare-hare.

A cewar Mr Biden "harin da muka kai ba shine na ƙarshe ba, kuma za mu ci gaba da farautar duk wanda ke da hannu a wannan mummunan hari."

Sai dai babu bayanai da suka tabbatar da cewa ƙusoshin na da hannu a harin na ranar Alhamis.

Fadar White House ta ce ƴan kwanakin da suka rage a kammala jigilar su ne mafiya haɗari tun bayan fara aikin.

Kawo yanzu an kwashe sama da mutun 110,000 da suka haɗa da Afghanistawa da kuma ƴan ƙasashen waje a cikin mako biyu.

Lura da cewa damar ficewa ta jirgin sama na ƙara kuɓucewa, da dama sun fara yunƙurin ficewa Afghanistan ta kan iyakar ƙasar da Pakistan.