Afghanistan: Amurka ta kashe wani ƙusa a ƙungiyar ISIS-K

Rundunar sojin Amurka ta ce wani hari ta sama da ta kai ya kashe wani ƙusa a ƙungiyar ISIS-K da ta kai harin kunar bakin wake a filin jirgin saman Kabul da ke kasar Afghanistan ranar Alhamis.

Rundunar ta ce harin da ta kai ta sama a gundumar Nangahar, ya kashe mutumin da Amurka ta ce shi ke kitsa wa ƙungiyar ISIS-K yadda za ta kai hare hare.

Wakiliyar BBC ta ce "rundunar ta tabbatar da kashe mutumin da take haƙo ta amfani da jirgi marar matuƙi" kuma kawo yanzu babu labarin cewa harin ya rutsa da fararen hula.

Amurka ta kuma ƙara jan kunnen yan ƙasarta da su guji zuwa filin jirgin na Kabul, don ba abun mamaki bane a sake kai wani harin.

Harin ƙunar baƙin waken na ranar Alhamis ya kashe mutun 170 da suka hada da sojojin Amurka 13.

Dubban masu son ficewa sun yi dafifi a wuraren da aka kai harin, duk da gargadin da Amurka da Burtaniya suka yi na hadarin fuskantar harin kunar bakin-wake daga wata kungiya mai alaka da ISIS, wato ISIS-K.

Ƙungiyar ta masu iƙirarin jihadi daga bisani ta fitar da sanarwar daukar alhakin hare-haren na Alhamis.

Mutuwar ita ce ta farko ga sojojin Amurka a Afghanistan tun watan Fabrairu na shekarar 2020.

Bayan harin Shugaba Biden ya jinjina wa dakarun da suka mutu, wadanda ya bayyana da cewa gwaraza ne da ke kan aikin sadaukar da kai don ceto rayuwar wasu.

Babban hafsan da ke jagorantar dakarun Amurkar a kasar, Janar Frank McKenzie ya ce har yanzu akwai barazana sosai ta hare-hare daga kungiyar ta ISIS-K.

A yanzu ƙungiyar Taliban ta ce ta girke dakarun ta a ciki da wajen filin jirgin, yayin da take jiran Amurka ta kammala kwashe mutanenta daga nan zuwa ranar 31 ga watan da muke ciki na Agusta.