Afghanistan: Hotunan rayuwa a Kabul ƙarƙashin mulkin Taliban

Taliban suna ci gaba da kafa kansu bayan ƙwace Kabul a ranar Lahadi.

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya tsere daga ƙasar, wasu rahotannin sun ce yana Uzbekistan.

Ga wasu hotuna na yadda rayuwa ta kasance a babban birnin a ranar Litinin.

Ga alamu komai ya kasance lafiya a tsakiyar birnin, a cewar wakilin BBC Malik Mudassir.

Babu cunkoson ababen hawa sosai, kantuna da dama sun kasance a kulle. Amma ga alama mutane na cikin kwanciyar hankali.

Sai dai an shiga yanayi na tashin hankali a babban filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa, a cewar wakilin BBC.

A ranar Litinin kawai akwai dakarun Amurka 2,5000 a filin jirgin sama, sannan wasu 500 ne na hanyar zuwa, a cewar mai magana da yawun ma'aikatar tsaro ta Pentagon John Kirby.

Dakarun Amurka kamar yadda ake gani a hoton da ke ƙasa har yanzu suna aiki don tabbatar da tsaro, in ji kakakin na Pentagon.

Bidiyon da ya yaɗu a shafukan sada zumunta sun nuna fararen hular Afghanistan sun ɗane jirgin yaƙin Amurka a lokacin da yake shirin tashi.

Ƙungiyar Amnesty International ta yi kira ga ƙasashen duniya su ɗauki mataki don hana lamarin yin muni.

"Abin da ke faruwa a Afghanistan wata masifa ce da ya kamata a ce an hango faruwarta kuma an daƙile ta," a cewar sakatare janar na ƙungiyar Agnes Callamard.

Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka.