Sauyin yanayi: Me ya sa matsalolinsa ke ƙara ta'azzara a duniya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Fernando Duarte
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Matsalar sauyin yanayi za ta kara ta'azzara nan da shekaru 20 masu zuwa, in ji wani masana. Bayanan da aka tattara game da yanayi na ƙara yin kasa a yayin da gobarar daji, da tsananin zafi, da kuma ambaliyar ruwa ke haifar da mummunar ɓarna a fadin duniya.
Masana kimiyya sun bayyana cewa wasu daga cikin waɗannan abubuwa sun nuna alaƙa da sauyin yanayin da mutane ke haddasawa - kuma akwai babbar damuwa cewa suna kara ta'azzara fiye da yadda za a iya hasashe.
Idan aka yi batun cewar guguwa ta afka wa birnin Zhengzhou na ƙasar China a ranar 19 ga watan Yuli tamkar rage girman matsalar ne.
Cikin kwana ɗaya kacal, an samu saukar ruwan sama na ma'aunin milimita 624 - kusan na tsawon shekara daya - kuma ya kwashe mutane 200,000 gidaje da kuma mutuwar 33.
A cikin makon baya, mummunan ambaliyar ruwa a arewacin Jamus tare ta haddasa ɓarna, hallaka mutane 177 da kuma wasu 100 da ba a gano ba, yayin da ambaliyar ruwa a ƙasar Belgium makwabciyarta ta haddasa mutuwar mutum 37.

Asalin hoton, Getty Images
Kamar ƙasar China, ƙasashen Turai biyu sun gamu da saukar mamakon ruwan sama. Kuma ba manyan 'yan siyasa irinsu shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ce kadai ta ɗora alhakin sauyin yanayi da haddasa aukuwar wannan bala'in ba.
"Ganin adadin mace-mace a ƙasashen da suka ci gaba kamar Jamus akwai damuwa kan raunin shiryawar kasashe wajen tunkarar dumamar yanayi,'' in ji Veerabhadan Ramathan, wani masani kan sauyin yanayi a ƙasar India kuma farfesa a Jami'ar jihar California a birnin San Diego, wanda ya yi amanna yanayi mai tsanani zai ''kara ta'azzara'' nan da shekaru 20 masu zuwa.
"Waɗannan matsaloli na yanayi mai tsanani sun ƙaru da kuma yawan aukuwa akai-akai da yake da matukar wahala a danganta su da dumamar duniya da sauyin yanayi,'' ya yi gargadi.
Shin ya kamata a dora wa sauyin yanayi alhakin aukuwar hakan?
A cikin shekaru 20, masana kimiyya sun yi gudanar da bincike kan yiwuwar dangantaka tsakanin yanayi mai tsanani da kuma dumamar duniya da fitar da gurbatacciyar iskar masana'antu da mutane ke yi.
Yayin da akwai sasantawa a tsakanin masana kimiyyar cewa yanayi mai tsanani ka iya haddasa aukuwar bala'o'in, akwai ƙaruwar shaidu da suka nuna cewa sauyin yanayin da ɗan adam ke haddasawa ka iya haifar da yawan faruwar waɗannan matsaloli kuma masu tsanani.
A fili take cewa ana ta yawan samun bayyanar afkuwar yanayi mai tsanani a faɗin duniya a shekarar 2021.
A watan da ya gabata, Amurka da Canada sun fuskanci watan Yuni mai dumama saboda tsananin zafi - iska mai zafin da ke saukowa kasa a fadin manyan yankuna.
An samu adadin yanayin zafi fiye da 1,200 na tsawon rana da 1,500 na lokacin dare a biranen Amurka ta Arewa tsakanin 24 zuwa 30 ga watan Yuni, kamar yadda bayanan da aka tattara daga Hukumar Lura da Yanayin Teku suka nuna.

Asalin hoton, Reuters
Yayin da a ƙasar Canada, yanayin zafi ya karu har na tsawon kwanki uku a jere a Lytton, da yankin British Columbia, da ya kai ma'aunin zafi na 49.6C (121.3F) kafin wutar daji ta kona kauyen kusan kurumus.
Duka ƙasashen biyu na ci gaba da fuskantar mummunar gobarar daji da ake dangantawa da tsananin zafi da yawan aukuwar fari. Jihar California ta riga ta shaida gobarar daji fiye da sau 4,900 cikin wannan shekarar - karin fiye da 700 a shekarar 2020.
A wasu ƙasashen duniya, Moscow a watan Yuni ta fuskanci tsananin zafi mafi muni a cikin shekaru 120, yayin da wutar daji a Siberia - ɗaya daga cikin yankuna mafi sanyi a duniya - na shirin kafa nata tarihin na fuskantar yanayin zafin a cikin watan Yuli, kamar yadda mahukuntan ƙasar Russia suka bayyana, a yayin da wasu yankuna ke fuskantar lokacin bazara mafi bushewa a cikin shekaru 150.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Lura da yanayi ta ƙasar India ta bayar da rahoton cewa a cikin watan Mayu, New Delhi babban birnin kasar ya fuskanci akalla yanayi daya a kowane wata tun daga watan Agustan shekarar 2020, saboda yanayi mai tsananin na saukar ruwan sama.
A shekarar 2019, binciken da cibiyar nazari kan yanayi mai mazauni a California ta gudanar ya gano cewa kusan bayanan duka lokuta 400 na tsananin zafi suka nuna sun faru a ƙasashen 29 na kusurwar duniya tsakanin watan Mayu zuwa Agusta na shekarar.
Masani kimiyya da tarihin yanayi Maximiliano Herrera ya yi ikirarin cewa daga shekarar 2021, an samu adadin alkaluman yanayin zafi mai tsanani fiye da 260 a ƙasashe 26.
"Adadin alkaluman akwai matuƙar fargaba, ba mu yi tsammanin za su kai yawan haka ba,'' in ji Geert Jan van Oldenborgh, wani mai bincike kan yanayi a Cibiyar Royal Netherlands Meteorological Institute, ɗaya daga cikin cibiyoyi mafiya girma a duniya da ke nazari kan sauyin yanayi.
"Babbar matsalar ita ce, ba mu hangi faruwar hakan cikin sauri da kuma ƙarfi ba."
Masana sun gaza ne?

Asalin hoton, Getty Images
Masana kimiyyar yanayi sun yi daidai da suka shafe shekaru suna gargadin cewa karuwar dumamar yanayi zai haifar da saukar mamakon ruwan sama da kuma ƙaruwar yanayin zafi mai tsanani, kamar yadda Roger Harrabin wakilin BBC mai sharhi kan al'amuran muhalli.
Misali, a shekarar 2004 masana kimiyya sun gudanar da bincike kan tsananin zafin da ya haddasa mutuwar mutane 30,000 a fadin Turai a shekarar da ta gabata, kana sun karkare da cewa fitar da iskar gas da mutane ke yi a cikin karni na 20 ya ninka damar samun yanayi mai tsanani irin wannan.
Amma kuma masana sun ce yana kara zama da matukar wahala a iya yin hasashe kan yanayi mai tsananin, kana sun tabbatar da cewa sun gaza yin hasashe game da girman matsalar ambaliyar ruwan da ta afku a ƙasashen Jamus da Belgium da kuma tsananin zafin Amurka ta Arewa.
Sun yi amanna cewa bincike kan yanayi da ake gudanarwa na gazawa saboda na'urori masu ƙwaƙwalwa ba su da karfin da za su iya hango girman matsalar.
Ba ko wane afkuwar bala'o'i ne za a danganta da sauyin yanayi ba

Asalin hoton, Reuters
Yana da matukar muhimmanci a yi la'akari da cewa ba ko wanne tsaninin zafi ko yanayi ne za a danganta da sauyin yanayi ba. Wani sashi na kimiyyar yanayi ya kira wani ƙwararre wajen duba musabbabin aukuwar matsalolin yanayin.
A 2013, misali, binciken masana a Burtaniya ya gano cewa halayen bil adama kusan su ne tushen duk matsalolin da ake gani a yanzu da ke kai wa ga fari da wutar daji da dai sauransu.
Akwai bukatar bijiro da sabbin tsare-tsare kan yada mutane za su takaita wasu dabi'un da ke buɗe kafa wajen ta'azzara matsalolin sauyin yanayi.
'Me ake bukatar duniya ta yi? '

Asalin hoton, Getty Images
Domin neman hanyar tsira a watan Nuwamba mai zuwa ake saran wakilai za su yi taro a birnin Scotland kan sauyin yanayin karkashin jagoranci Majalisar Dinkin Duniya.
Ana saran mahalarta taron su gabatar da bayanai da tsare-tsare kan rage turiri da iskar da ke gurbata muhalli.
Masana kimiya da dama da ƴan siyasa na ganin jajircewa da sadaukarwa zai taimaka wajen rage dumamar yanayi kuma wannan shi ne abin da ake sa ran taron ya cimma.
Majalisar Dinkin Duniya dai tace ba zata gaza ba wajen ci gaba da gargadi da fitar da bayanai da za su taimaka wajen cimma muradan kare muhalli.











