Sace-sace da harbe-harbe a 'filin dagar' Afirka Ta Kudu

Wani jami'an Hukumar 'Yansandan Afirka ta Kudu na harba harsasan roba kan masu zanga-zanga da ke sace-sace a rukunan shaguna na Jabulani a birnin Soweto, kudu maso yammacin birnin Johannesburg, ranar 12 ga watan Yulin shekarar 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Zanga-zangar ta fara a lardin Natal , amma ta bazu zuwa Gauteng a cikin karshen mako
    • Marubuci, Daga Flora Drury
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Zanga-zangar da aka fara bayan da tsohon shugaban kasar Afirka Ta Kudu Jacob Zuma ya miƙa wuya ga 'yan sanda don zaman gidan kaso na watanni 15, ta ƙara zafafa zuwa tashin hankali da sace-sace a cikin 'yan kwanaki.

BBC ta tattauna da kadan daga cikin mutanen da suka samu kan su a tsakiyar tashin hankalin.

"Muna cikin tsaka mai wuya,'' Ian - ba sanansa na gaskiya ba - ya shaida wa BBC daga birnin Durban da ke lardin KwaZulu-Natal na kasar Afirka Ta Kudu inda rikicin ya rincaɓe.

A cikin kwanaki uku da suka gabata, ya bayyana cewa da kyar ya samu ya yi barcin sa'a daya zuwa sa'io biyu a lokaci guda. Shi da 'yan abokan aikinsa - da suke aiki a wani kamfanin samar da tsaro mai zaman kan sa - na rayuwa ne kan shan abubuwan sha na kara kuzari a yayin da suke zaman jira su gani.

Sun yanke kauna ga kokarin da suke yi na hana sace-sacen wanda ya haddasa lalata gine-gine da dama tun bayan da aka fara zanga-zangar kiran da a sako tsohon shugaban kasar Jacob Zuma daga gidan yari a cikin karshen makon jiya.

Yanzu suna kokarin kare unguwar da suke ciki.

"Mun je wurin da za mu rika kallon su suna sace-sace, ba ma iya hana su - kada su cutar damu.''

Hayaki ya turnuke daga ginin Makro da aka bankawa wuta a Umhlanga, arewacin birnin Durban,ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata mai zaune a birnin Durban ta ce daga gidanta tana jin kaurin hayaki daga wutar da ke tashi

A wani bangare na birnin Durban, wata mata na shirin tuka motarta na tsawon minti 20 daga gidanta zuwa wurin iyalanta a unguwar da rikicin ya yi muni.

Ba ta da tabbaci kan ko za ta iya kai wa , ko kuma daya daga cikin shingayen da ke kan titinan birnin su hana ta.

Amma kuma tana yakinin cewa ba za ta iya jure sake sahfe dare tana kwance tare da jin karan bindigogi ba.

"Ina jin tsoro matuka,'' matar - wacce ta ce kada ambaci sunata - ta shaida wa BBC.

Bayanan bidiyo, Wata uwa a birnin Durban na jefa jaririyarta ta taga daga wani gini bayan da aka banka masa wuta

"Tamkar kana zaune cikin fage yaki ne da karar harbe-harbe, tashin wuta da kuma turnukewar hayaki a ko ina a ciki kwanaki biyu da suka gabata.''

A lokacin da hayakin ya washe, abin da kawai za ka iya gani game da abinda ke faruwa a birnin Durban daga sama ne.

Jayshree Parasuramen, wata mai bayar da rahoto daga cikin jirgi mai saukar angulu na gidan rediyon East Coast, na iya ganin komai.

Masana'antu na cin wuta, an toshe hanyoyi da manyan motocin daukar kaya kana ''dubban'' mutane na ta sace-sace a shaguna da manyan rumbunan ajiyar kaya, ana kuma iya ganin motoci na jiran a jiƙa musu kayan da aka sacen.

"Sun kafa wata garkuwa a yankunan da suke sace-sacen,'' ta bayyana. "Don haka an toshe wauraren shiga da fita a toshe suke, kuma mutane da dama da suka cunkusu a yankin don hada masu ababen hawa wucewa.''

Mutanen, in ji ta, su ma '' na dauke da manyan makamai''.

"Adadin karar bindigogin da ka ke iya ji na da ban mamaki da fargaba - har da bama-baman da ake hadawa da fetur.

Ba ma iya zagayawa ta saman yankin saboda suna buɗe wuta, kuma daga ƙarshe dole muka sauka saboda irin makamai da suke amfani da su.''

Wasu da ake zargi da sace-sacen sun mika wuya ga jami'an tsaro yayin da ake tasa keyarsu waje, a cikin rukunin shaguna, ranar 13 ga watan Yulin shekarar 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shagunan sayar da kayan abinci - akasari da aka kai wa hari - sun kasance kusan babu muhimman abubuwa ciki

Mahukunta - kama daga shugaba Cyril Ramaphosa - duka sun bayyana cewa bata-gari ne suka kwace zanga-zangar.

Wasu sun yi amanna cewa mummunan tasirin da annobar korona ta haifar wani makamashin da kawai je jiran tartsatsin da wuta za ta tashi.

A wannan abu da ke faruwa, tartsatsin shi ne kullewa a gidan yari da aka yi wa wanda Mista Ramaphosa ya gada a kan aikata laifin rena umarnin kotu.

"Mun san cewa, muddin aka sake kafa dokar kulle, hakan ka iya faruwa, saboda da zarar ka bar mutane cikin yunwa, irin wadannan abubuwa za su faru,'' Eldrin Naidoo ya shaida wa BBC daga birnin Johannesburg.

Amma kuma, yayin da Mosetlhi ya yi nuni da cewa, daga karshe zai fi shafar wadanda dama ke fama da matsaloli na rayuwa.

"Ganin ana banka wa shagunan mutan wuta - kwarai, mutane suna fama da yunwa a yanzu, amma kuma bayan nan za a samu karin matsalar rashin aikin yi, karin damuwa, karin ukuba a kasar da ke kokarin farfado da kanta.''

Mutane na kallon wani mutum a kan keken guragu yayin da yake wucewa ta gaban rukunin shagunan Lotsoho a cikin garin Katlehong, Gabashin birnin Johannesburg , ranar 12 ga watan Yulin shekarar 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sace-sacen daidai yake da zagon-kasa ga tattalin arziki,'' in ji Jayshree Parasuramen

A halin da ake ciki, wadanda ke zaune a yankunan da ke tsakiyar tashin hankalin ba za su iya tunanin watamakoma ba.

"Ba ka san ko za ka kai gobe ba - wannan shi ne tunaninsua yanzu,'' Jayshree Parasuramen ta ce.

Ian abokan aikinsa, sun yanke kaunar sauraron bayanan da ke fitowa daga gidan rediyo, kuma yanzu suna duba yadda za su tinkari gungun ɓata-garin.

"Saps [Hukumar 'yansanda ta Afirka Ta Kudu] na shan faman samun kiran wayoyi kuma sun riga sun daina daukar ko wane kira,'' ya ce.

"Don haka muna yin kira ga maza mazauna yankin da su fito su kare lafiyar iyalansa.''

Wani mai shago rike da adda ya tsaya cikin tsawon dare don kare dukiyarsa a lokacin da ak tsakiya wawason kayan shaguna da zanga-zangar a birnin Durban, Afirka ta Kudu ranar 12 ga watan Yulin shekarar 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masu shaguna da dama sun ce suna kokarin kare dukiyoyinsu

Amma babu abinda za su iya yi idan abubuwa suka rincabe. Jita-jitar cewa mutane na ta cika gwangwanaye da man fetur a kusa da yankin na kara bazuwa.

"Muna dauke da kululai (a cikin bindigogin mu) ," Ian ya bayyana. "Don ka san za mu rika kare kan mu daga bama-baman da aka hada da man fetur da wadannan kululai.''

A ranar Litinin ne, gwamnati ta sanar da cewa za ta aike da sojoji don taimakawa hukumar 'yan sandan da aiki ya rincabe wa, amma wadanda BBC ta tattauna da su alama kadan suka gani ta dakarun soji a yankunan.

Amma mahukunta har yanz ba su ayyana dokar- ta-baci ba, kuma mutane na ganin an yi musu ba daidai ba.

'Yanuwam daya daga cikin masu wawaso da suka mutu na alhini a kusa da gawarsa baya da ya saci kayayyaki daga shaguna a yankin, birnin Johannesburg, Afirka ta Kudu, ranar 13 ga watan Yulin shekarar 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mutane akalla 72 ne suka mutu a tashin hankalin - akasarinsu lokacin turmutsutsu

"Sojoji sun iso nan ne a lokacin da hayaki ya rika ya turnuke,'' in ji Ian.

"Ya kamata a ce sun je wuraren da ke tsakiyar rikicin amma suna zuwa ne wuraren da rikicin bai shafa ba tukuna. Mun rasa ta cewa.''

"Ya kamata a ce sojojin sun mayar da hankali wajen kare lafiyar fararen hula,'' in ji matar da ke fatan isa ga 'yaruwarta

"Ba daidai bane a ce fararen hula ne ake sa ran za su fatattaki masu zanga-zanga,'' ta ce.

''Ta yaya za a ce bai kasance lokacin doka-ta-baci ba? Ta yaya mutum zai samu rayuwa cikin sauki a Afirka Ta Kudu?"

Dukkan hotunan suna da haƙƙin mallaka.