Twitter: Labaran ƙarya da ake yaɗawa kan rikicin shafin sada zumunta da Buhari

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da dakatar da amfani da shafin Twitter a ƙasar a makon da ya gabata, ƴan ƙasar ke ta tofa albarkacin bakinsu kan lamarin.
Haka ma jami'an diflomasiyya da gwamnatocin wasu ƙasashen da kungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam.
Gwamnatin Najeriyar dai ta dakatar da amfani da shafin ne kan abin da ta ce "amfani da shafin wajen gudanar da ayyukan da ka iya yi raba kawunan ƴan ƙasar", kamar yadda sanarwar da ta fitar ta ce.
Kuma dama a makon da ya gabatan dai, shafin Twitter ɗin ya cire wani saƙo da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa inda ya ja kunnen ƴan IPOB masu ƙoƙarin ɓallewa daga Najeriya kan hare-haren da suke kaiwa a Kudu maso gabashin ƙasar.
Twitter ta ce saƙonnin nasa sun saɓa wa dokokinta.
Sai dai wani abu da ya biyo bayan matakin gwamnatin Najeriya na dakatar da Twitter su ne labaran ƙarya da ake ta ci gaba da yaɗawa a wasu shafukan sada zumunta musamman Whatsapp da Facebook.

Ana ci gaba da yaɗa wani hoto mai ɗauke da tambarin BBC Hausa, da rubutu da ke alamta cewa kalaman Shugaba Muhammadu Buhari ne: "Narufe. Twitter. Saura Whastapp Da Facebook".
Sai dai wannan labarin ƙarya ne, ma'ana Shugaban bai yi waɗannan kalaman ba kazalika BBC Hausa ba ta wallafa wannan sako ba.
Wasu ne suka yi amfani da tambarin BBC da salon hotunan da BBC ke amfani da su wajen wallafa saƙonni.
Idan aka yi la'akari za a ga cewa akwai kurakurai a rubutun - a maimakon 'Na rufe' a jikin hoton an rubuta 'Narufe' sannan aka biyo kalmar da aya, wanda kuma bai kamata ta kasance a nan ba.
Sannan a wajen rubuta 'Whatsapp' idan aka lura sosai, an rubuta Whastapp, wato 's' ta zo kafin 't'. Abu ne mawuyaci kafar yaɗa labarai mai martaba kamar BBC ta yi irin waɗannan kurakuran.
Haka kuma, ba a ga wata sanarwar gwamnati mai kunshe da wannan sako ko kalamai ba.
Shugaba Buhari bai ce zai ce rufe Facebook da Whatsapp ba kuma BBC Hausa ba ta ruwaito ya ce hakan ba.

Asalin hoton, OTHERS
Haka kuma, ƴan kwanaki bayan sanarwar gwamnatin Najeriyar an fara yaɗa wani sako da ke nuna cewa ya fito ne daga kamfanin Twitter inda wai suka ce suna bitar matakinsu na cire saƙonnin Shugaba Buhari.
Haka kuma, saƙon ya ce wai Twitter na tattaunawa da gwamnatin Najejeriya kuma ta yi alƙawarin mutunta dokokin Najeriya, sannan aka biyo sakon da #KeepItOn.
Binciken BBC ya gano cewa Twitter bai wallafa wannan saƙon a shafinsa ba. Kuma idan aka yi la'akari sosai za a ga cewa babu alamar '@' da ke zuwa kafin suna ko username a shafin Twitter wato maimakon @Policy, Policy ne kawai a rubuce a wannan sakon.
Tun bayan sanar da dakatarwar an kirkiri maudu'in #KeepItOn don nuna ƙin jinin matakin na gwamnati kuma idan aka yi amfani da shi a shafin ya kan fito tare da wata alamar layuka launin ja. Wannan sakon ba ya ɗauke da wannan alamar ta jikin maudu'in.

Asalin hoton, OTHERS
Akwai wani hoto mai ɗauke da wani saƙo da aka ce ya fito ne daga shafin Twitter inda kamfanin wai ya aika wa Shugaba Muhammadu Buhari @MBuhari wani saƙo da ke cewa kamfanin bai da masaniyar waye Buhari kuma bai san ƙasar da ya ke jagoranta ba.
Kuma sakon na sanar da Buhari cewa ya ga wasu saƙonni da shugaban wallafa kuma sun saɓa wa dokokin kamfanin mai lamba 4 don haka an cire shi. Hoton ya nuna cewa an wallafa sakon ne ran 4 ga watan Yunin 2021.
Binciken BBC ya gano cewa wannan saƙon na ƙarya ne kuma Twitter ba ta wallafa shi ba. Asali ma, Twitter ta cire saƙo ɗaya ne kawai cikin jerin saƙonnin da Buhari ya wallafa inda ya yi magana kan yaƙin basasar Najeriya na 1967 zuwa 1970.
Saƙon na Buhari ya ce "matasan yanzu ba su san girman ɓarna da hasarar rayukan da aka yi ba a yaƙin basasa ba. Mu da muka shafe wata 30 a fagen daga, muka ga bala'in yaƙin, za mu bi da su da salon da suka fi ganewa."
Twitter ta sa alamar cewa ta cire tweet ɗin ne kawai amma ba ta wallafa wani saƙo ba bayan haka.
Haka kuma, idan aka duba hoton da kyau za a ga cewa a kan tambarin Twitter da ke kusa da sunan shafin, akwai jurwayen fari-fari a jikinsa wanda ke nuna cewa an yi amfani da fasahar 'photoshop' wajen sauyawa ko ƙirƙirar hoton.
Sannan, jimlar turancin ma na da gyara a cikinsa.

Asalin hoton, OTHERS
Akwai wani hoto shi ma mai ɗauke da wani saƙo da ke nuna sunan shugaban kamfanin Facebook da Whatsapp da Instagram, Mark Zuckerberg da ke cewa Shugaban Najeriya na buƙatar likita ya duba shi saboda ba ya tunani yadda ya dace.
Hoton ya nuna sunan mai shafin Mark Zuckerberg da hotonsa kuma yana ɗauke da alamar nan da ke nuna cewa Twitter ta amince da shafinsa wato 'verified' sannna ya nuna cewa an wallafa saƙon ne ranar 2 ga watan Yunin 2021.
Ko a wajen rubuta sunan watan, ana iya ganin kuskure inda aka rubuta hrafin 'J' da ƙaramin baƙi maimakon da babban baƙi. Ba haka rubutun ke fitowa ba a Twitter.
Sai dai binciken BBC ya gano cewa Mark Zuckerberg ba ya da shafin Twitter. Akwai wani shafi da ake tunanin nasa ne mai suna @Finkd kuma rabon da a wallafa saƙo a shafin tun shekarar 2012.
Hoton shafin da ake ta yaɗawa mai ɗauke da sunan Zuckerberg ba nasa ba ne, kuma a halin yanzu ma Twitter ya dakatar da shi.
Wannan ma dai wani salo ne na amfani da komfuta wajen ƙirƙirar hotuna don yaɗa labarin ƙarya.

Labaran ƙarya sun daɗe da zama barazana a faɗin duniya kuma sun sha haddasa fititinu da dama.
Gwamnatoci da kamfanonin sada zumunta na ci gaba da kamfe kan yaɗa labar ƙarya a shafukan.
Gwamnatin Najeriya ta ce tana shirin sanya doka kan amfani da shafukan sada zumunta inda ta ce ana amfani da shafukan wurin yaɗa labaran ƙarya masu ta'zzarawa.
Wasu na ganin wannan hana ƴancin tofa albarkacin baki ne, amma gwamnati na ganin shafukan sada zumunta babbar barazana ce ga ci gaba ƙasa da al'umma baki ɗaya.













