Labaran Karya: Yadda labarin karya ya hada Osinbajo da matarsa

Asalin hoton, Getty Images
Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa matarsa Dolapo Osinbaje ta zarge shi da neman mata bayan da wani hotonsa ya bayyana a kafofin sada zumunta tare da wasu mata sanye da kaya masu nuna surar jiki.
Ya ce "mako 3 da suka gabata, matata ta kira ni ta ce, "Yemi, ashe matan banza ka ke bi yanzu"."
Sai dai ya ce abun mamakin shi ne, a zahiri matan da ya dauki hoto da su a wajen wani taro sanye su ke da tufafi na mutunci.
Amma wata kafar yada labarai ta shafin intanet ta yi amfani da hanyoyin sauya hotuna na zamani inda aka sauya kayan da ke jikin matan don ta bata masa suna.
Ya ce kafar yada labaran sun buga hoton tare da labarin da ke cewa 'an kama Osinbajo da matan banza'.
Osinbajo ya bayyana haka ne a wani taro da BBC ta shirya don yaki da labaran karya a Abuja, babban birnin Najeriya.
Taron na BBC dai ya tattara masu ruwa da tsaki don yaki da labaran karya a lokacin da manyan zabuka ke karatowa a Najeriya.

Ana sa ran tattauna yadda rashin amincewa tsakanin kafofin watsa labaran Najeriya da hukumomin gwamnati da 'yan siyasa da kuma 'yan kasar ke rura yaduwar labaran karya musamman a wannan lokaci na shafukan sada zumunta.

Taron ya samu halartar Farfesa Yemi Osinbajo da marubuci kuma mai tsokaci kan siyasar Najeriya Farfesa Wole Soyinka da Darekta BBC Jamie Angus.











