BBC ta gano labarin karya da aka wallafa da sunanta kan Maryam Sanda

Bayanan bidiyo, Yadda za ku gane shafukanmu na BBC hausa na ainihi

BBC Hausa ta bankado wasu shafukan sada zumunta da ke amfani da sunanta wajen yada labaran karya game da shari'ar Maryam Sanda.

Labarin karyar da ake yadawa da sunan BBC Hausa ya nada alaka da shari'ar Maryam Sanda da kuma kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International.

A

Asalin hoton, Facebook

Sai dai BBC ba ta wallafa wani labari makamancin haka ba a dukkan shafukanta, sannan kuma kungiyar Amnesty International ba ta aike mata da sanarwa kan duk wani abu da ya danganci Maryam ba tun bayan da aka yanke hukuncin a ranar .

Mai magana da yawun Amnesty International a Najeriya Isa Sunusi shi ma ya tabbatar wa BBC cewa ba su aike wa kowace irin kafar yada labarai wata sanarwa ko magana da ita kan batun Maryam Sanda ba.

Hakan na nufin baya ga yin amfani da sunan BBC wajen yada wannan labari mara tushe balle makama, batun cewa Amnesty International ta yi magana kan hukuncin da aka yanke wa Maryam Sanda ma karya ne.

Labarin ya yadu kamar wutar daji

Amma duk da kasancewar labarin na bogi ne kuma daga kafar da ba ta da sahihanci, jama'a sun yi ta yada labarin musamman a shafukan Facebook da Whatsapp, sun kuma yi ta bayyana ra'ayoyinsu game da labarin da shafin ya wallafa.

A shafin bogin dai kimanin mutum 1,600 ne suka sake wallafa labarin a shafinsu na Facebook yayin da wasu sama da 600 suka bayyana ra'ayoyinsu kan labarin.

Sannan mutane da dama sun yi ta kiran ma'aikatan BBC don tabbatar da gaskiyar labarin, yayin da wasu kuwa suka yarda da shi har suka dinga tafka muhawara a kansa.

Wannan layi ne

Shafukan bogi

Binciken da BBC ta gudanar ya gano cewa ba wannan ne karon farko ba da wani shafin bogi yake wallafa labarai da sunan BBC ba.

Baya ga wannan shafin akwai wasu da dama da suma suke amfani da sunan BBC wajen wallafa bayanan karya wadanda ba su da asali, sai dai mutane da dama ba sa iya bambance shafin BBC da na bogi.

Shafin BBC dai na da wata alama mai kamar an ja maki da shudiyar kala a jikinsa. Kuma yana da mabiya fiye da miliyan biyu da dubu dari uku, (2.3).

Amma a wasu lokutan mu kan sauya hoton da ke kan shafin.

shafin BBC Hausa na Facebook

Asalin hoton, BBC Facebook

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Wannan layi ne

Menene labaran karya?

Sun kunshi bayanai na karya da hotuna da na bidiyo da ake kirkira a yada domin a harzuka mutane.

Ko kuma yada tsoffin hotuna, ko hotunan da ba ma a kasar aka dauka ba.

Irin wadannan labaran karyar da kuma hotunan karyar da ake yadawa, na taimaka wa wajen rura rikici musamman a tsakanin kabilu.

A wasu lokuta rashin samun bayanai daga bangaren gwamnati ko mutanen da abin ya shafa, na haifar da yada jita-jita da kuma zaman dar-dar.

Irin wadannan labaran karya kan haifar da illoli masu yawa, kamar tayar da fitina, da kulla kiyayya tsakanin al'umma da kuma yada bayanan da ba su da tushe.

Binciken da BBC ta yi a kwanakin baya ya gano cewa labaran karya na sahun gaba wurin yada rikicin da ake fama da shi a Najeriya tsakanin makiyaya da manoma.

Hakan ne kuma ya sa ma'aikatar sadarwa ta kasar kaddamar da wani shiri na musamman domin yaki da wannan dabi'a, wacce ke kara samun gindin zama a kasar, musamman a shafukan sada zumunta.

Wannan layi ne

Yadda ake gane labaran karya

Akwai yiwuwar cigaba da samun labaran karya kan wannan rikici, musamman a lokacin da ake tunkarar zaban shugaban kasa a badi.

Kamfanonin sada zumunta kamar Twitter da Facebook sun bayyana shirinsu na yakar sana'ar yada labaran karya a duk fadin duniya, amma ga wasu hanyoyi biyar da za ka iya kawar da yada bayanan da ba su da tushe:

Rikici na baya bayan nan shine na jihar Filato

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mutane da dama aka kashe a rikicin manoma da makiyaya wanda aka ce labaran karya na kara zuzutawa

Mutane da dama aka kashe a rikicin manoma da makiyaya wanda aka ce labaran karya na kara zuzutawa

Binciki asalin labarin: Shafukan sada zumunta na karya kan yi kokarin bayyana kansu a matsayin cewa sun fito ne daga manyan kafofin watsa labarai, a don haka ka duba shafi sosai kafin ka watsa bayanan da suka wallafa. Shafukan da aka tabbatar da halaccinsu suna dauke da alamar shudi a Facebook, da Twitter da kuma Instagram.

Duba wasu karin hanyoyin: Duk da cewa wannan wani lokaci ba zai gamsar ba amma yana da kyau a duba abin da wasu kafofin watsa labarai masu inganci ke cewa kan labari domin tabbatar da gaskiyar batu. Tambayi kanka, shin ingantattun kafafan yada labarai na bada rahoton wannan labarin?

Hanyoyin bincika labari: Akwai hanyoyi da dama da za su taimaka maka wurin tabbatar da sahihancin hoto ko bidiyo. Google, da Bing da kuma Tin Eye duk suna duba asalin hoto, wanda kan iya gaya maka inda aka dauki hoto da kuma asalinsa. Tabbatar da bidiyo ya fi wahala amma shafuka kamar InVid na bada damar gano inda aka yi amfani da bidiyon da aka wallafa a Facebook da YouTube a baya.

Duba asalin abin: Idan kana da ainahin hoton ko bidiyo, za ka iya samun bayanai masu muhimmanci game da su, ciki har da wuri da kuma lokacin da aka dauka da kuma na'urar da aka yi amfani da ita. Abin takaicin shi ne da zarar an wallafa hotuna a shafukan sada zumunta to bayanansu na sali sai su bace.

Yi tunani kafin ka wallafa: Dole a yi taka-tsan-tsan saboda ka da a kara jefa mutane cikin rudani. Kafin ka wallafa, ka tambayi kanka ko bayanan da ka ke da su sun inganta kuma ya karfin sahihancinsu ya ke.