'Yan bindiga sun kashe mutum 937 a Jihar Kaduna a 2020

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufa'i
Bayanan hoto, Gwamnati na nan a kan bakanta na yanke kauna da 'yan fashin daji a jihar

Hukumomi a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun fitar da sakamakon binciken shekara kan batun tsaro da ya nuna cewa mutane a kalla 937 ne suka mutu a hare-haren 'yan bindiga da satar mutane a jihar a shekarar 2020.

Hukumomin sun bayyana cewa a cikin mutane 937 da 'yan bindigar suka kashe da ba su ji ba basu gani ba kimanin 468 daga ciki sun fito ne daga kananan hukumomin Birnin Gwari, da Igabi, da Chikun, da kuma Giwa.

Kwamishinan harkokin tsaro da al'amuran cikin gida na jihar, Mista Samuel Aruwan ya shaida wa BBC cewa, idan aka hada gaba daya za a ga cewa mutum 617 da suka rasa rayukansu daga mazabar Kaduna ta Tsakiya ne.

Sannan kuma yankin Kudanci akwai mutane 286 da suka rasa rayukansu.

Ya ce 'yan bindigar sun sace tare da yin garkuwa da mutane kimanin 1,972 a cikin shekarar da ta gabata a fadin jihar ta Kaduna.

''A mazabar dan majalisar dattawa ta Kaduna ta Tsakiya nan ne matsalar ta fi kamari, saboda a nan ne aka yi garkuwa da mutane 1,561 cikin 1,972, har ila yau 1, 461 daga cikin sun fito daga kananan hukumomin Giwa, da Birnin Gwari, da Chikun da kuma Igabi,'' in ji kwamishinan.

Ya kuma ce gwamnatin ta tattara wadannan alkaluma ne ta hanyar bayanan da suka samu daga sojoji da sauran jami'an tsaro da kuma wasu bayanan sirri daga majiyoyi kwarara daga wasu jama'a.

'Yan fashin dajin kuma in ji kwamishina Aruwan sun sace shanu kimanin 7,195 a fadin jihar a wannan lokacin.

''Mazabar Kaduna ta tsakiyar kamar yadda na fada a baya, nan ne inda matsalar ta fi muni, domin kusan cikin dabbobin 7,195 da aka sace, kimanin 5,614 daga yankin ne aka fi sacewa a kuma kananan humomin Birnin Gwari, da Igabi da Giwa da kuma Chikun,'' ya ce.

Ta bangaren wadanda suka rasa matsugunai da dukiyoyi kuwa kwamishina Samuel Aruwan ya bayyana cewa akwai ma'aikata ta musamman waddae aikinta shi ne kula da ayyukan da suka shafi gaggawa na muhalli.

Ya kuma ce amma duk wani abu da ya shafi rasa rayuka shi ya fi jan hankulan al'umma baki daya, amma kuma abinda gwamnati ta fi magana a kai shi ne yawan mutane da suka rasa rayukansu a sakamakon hare-haren 'yan fashin dajin.

Ya ce wannan matsala ce da ta fi ci wa mutane da hukumomi tuwo a kwarya.

Short presentational grey line

Me gwamnati ke yi game da karuwar hare-haren cikin wannan shekarar?

Gwamnatin jihar Kadunan ta bakin kwamishinan harkokin tsaro da al'amuran cikin gida Mista Samuel Aruwan ta ce har yanzu tana kan bakanta na ci gaba da farautar 'yan fashin dajin babu kama hannun yaro.

''Har yanzu ba barinsu muka yi ba, jami'an tsaro suna maida martani, ana nan ana aiki babu kakkautawa,'' in ji kwamishina Aruwan.

Ya kuma ce: ''Mun zo wani irin yanayi a Najeriya da ya zama wajibi mutane su fahimci abinda ke faruwa a kan tsaro, kuma wannan rahoto bayan alkaluman da ya fitar ya kuma yi magana a kan hanyoyin da ya kamata idan aka bi za a kai ga nasara.''

Don haka ya ce, ya zama wajibi a cigaba da aiki babu kama hannun yaro kan abinda ya shafi tsaro, kama zamanto an gano tare dakai farmaki a duk matattarar wadannan 'yan bindiga.

''Ya zama wajibi gwamnatocin jihohi da na tarayya su hada hannu don tabbatar an ga bayan wadannan mutane ta hanyar kai musu farmaki ta ko ina,'' ya ce.

Gwamnati na nan kan bakanta na yanke kauna da 'yan fashin daji?

Har yanzu gwamnatin jihar Kaduna na nan a kan bakanta na cewa ba za ta taba yin zaman sulhu ko sasantawa da 'yan fashin dajin da suka addabi jihar ba in ji cewar kwamishina Samuel Aruwan a cigaban hirarsu da BBC.

''Idam mutum yana wannan harkar ya fahimci abin da yake yi ba daidai bane yana da zabi, amma abinda muke magana a nan shi ne, 'yan fashin daji wadanda babu abinda talakawan jihar Kaduna suka yi musu su shigo su yi fashi su sace tare da kashe mutane, su aikata fyade, su kona garuruwa su karyar tattalin arzkin al'ummar da ba su ji ba basu gani ba, gwamnati ba za ta yi sulhu da su ba,'' in ji Aruwan.

Duk wadann mutane gwamnatin jihar kadun ta yanke kauna da su.

''Wanda zai dau makami ya ya kashe mutane ai ka ga babu kauna tsakanin su da gwamnati ko kadan,'' amma idan mutm ya ce ya tuba ya yi nadama, gwamnatin jihar Kaduna dai ta bayyana matsayinta babu maganar sulhu tsakaninta da 'yan fashin daji da ke cigaba da aikata ta'asa, ya ce''

Kana kuma ya karkare da cewa ai ko sauran jihohin da suke daukar wannan matakin babu abinda ya sauya, kamar ana tufka da warwara ne.