Najeriya: Yawan rundunonin soja da ke yaƙi da ƴan bindiga

Asalin hoton, Getty Images
Yawan rundunonin soji da ke yaƙi da masu ɗauke da makamai a Najeriya ya nuna girman matsalar tsaro a ƙasar.
Najeriya ta shafe shekaru tana fama da rikicin Boko Haram a arewa maso gabashi da matsalar ƴan bindiga masu fashin daji da satar mutane a arewa maso yammaci da arewa ta tsakiya.
Akwai kuma matsalar masu fasa bututu a kudancin ƙasar musamman yankin kudu maso kudu.
Girman matsalolin tsaron a sassan ƙasar ya raba rundunar sojin Najeriya, inda ta kafa rundunoni a yankunan ƙasar domin kawo ƙarshen matsalolin.
Dubban mutane aka kashe tare da raba miliyoya da gidajensu a hare-haren Boko Haram da ƴan bindiga masu satar mutane a arewacin Najeriya.
Tun kafin hawan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ɗaya daga cikin manyan alƙawura uku da ya yi shi ne na kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa musamman a arewa maso gabashin ƙasar.
Ko da yake gwamnatin Buhari ta APC na cewa tana iya ƙoƙarinta na kawo ƙarshen matsalolin tsaron musamman a yankin arewacin ƙasar.
Yawan rundunonin soji

- Operation TURA TAKAIBANGO
- Operation LAFIYA DOLE
- Operation Hail Storm
- Operations SAFE HAVEN
- Operation WHIRL STROKE
- Operation THUNDER STRIKE
- Operation Hadarin Daji
- Operation SAHEL SANITY
- Operation DELTA SAFE
Arewa Maso Gabas
A Kwanan nan rundunar sojin Najeriya ta kafa sabuwar rundunar Operation TURA TAKAIBANGO a yankin arewa maso gabashi domin kakkabe mayaƙan Boko Haram
Rundunonin Operation Lafiya Dole da kuma Operation Hail Storm sun da daɗe suna yaƙi da 'yan ƙungiyar Boko Haram da kuma na ISWAP a arewa maso gabashin Najeriya.
Operation Lafiya Dole runduna ce ta sojin ƙasa da ke faɗa da Boko Haram inda kuma take samun taimako daga rundunar Operation Hail Storm da ke kai hare-hare ta sama.
Arewa Maso Yamma
A arewa maso yammacin Najeriya, akwai Rundunonin Operation Hadarin Daji da kuma Operation Sahel Sanity.
An kafa rundunonin ne a yankin musamman jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna domin yaƙi da ƴan bindiga masu fashin daji da satar mutane domin kuɗin fansa da kuma satar shanu.
Aikin rundunonin ya shafi yaki da ƴan bindiga da suka addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya, inda satar mutane ta zama ruwan dare.
Arewa Ta Tsakiya
A arewa ta tsakiya, akwai rundunonin Operation Safe Haven da Operation Thunder Strike da Operation Whirl Stroke da ke yaƙi ƴan bindiga da ɓarayi a yankin.
Aikin rundunonin ya shafi kai hare-hare ta ƙasa da kuma sama.

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shin kwaliyya tana biyan kuɗin sabulu?
Watanni kaɗan bayan da Shugaba Buhari ya hau kan karagar mulki a 2015, mutanen ƙasar musamman na arewa maso gabashi suka fara shewa da nuna jin daɗinsu sakamakon ganin alamun kwaliyya ta fara biyan kuɗin sabulu, ganin cewa an ɗauki tsawon lokaci babu tashin bama-bamai, da kuma shingaye kan hanya da aka cire.
An kuma daina samun tashin bama-bamai a jihohin Kaduna da Kano da Filato da sauran jihohin arewa maso yammacin ƙasar.
Wannan dalili ne ya sa wasu 'yan ƙasar ke ganin kamar shugaban ya kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar.
Amma shekaru kaɗan bayan hakan, wasu 'yan ƙasar da ƙungiyoyi masu zaman kansu suka fara kiran gwara jiya da yau, sakamakon yadda matsalar tsaron ke ƙara ƙamari a faɗin ƙasar.
Satar ɗaliban makarantar sakandaren Kankara a jihar Katsina a watan Disamba kafin a kuɓutar da su ya tayar da hankali a Najeriya tare da kara fito da girman matsalar tsaro a ƙasar
A kwanakin baya, ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta bayar da rahoton cewa an kashe kimanin mutum 1,126 a jihohin arewacin Najeriya tsakanin watan Janairu zuwa Yuni.
A kwanakin baya ma sai da wani uban ƙasa a jihar Katsina ya shaida wa BBC cewa 'yan bindiga sun mayar da mata 600 zawarawa a yankin Batsari da kuma mayar da yara sama da 2,000 marayu.
Wasu na ganin irin yawan rundunonin da aka kafa a arewacin ƙasar, ya kamata a ce an kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.
Ko da yake sojojin cewa suna samun nasarori a yakin da suke yi da ƴan bindiga
An ruwaito cewa sama da mutum 3,000 aka kashe a jihar Zamfara tun daga 2011 tare da garkuwa da sama da mutum 500.
Ita ma ƙungiyar nan mai bincike kan tashe-tashen hankula a kasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe mutane fiye da dubu takwas a rikicin arewa maso yammacin Najeriya cikin shekaru 10, kamar yadda ta fitar a wani rahotonta a watan Mayun bara.











