Shekarar 2021: Saƙon Shugaba Buhari na sabuwar shekarar 2021 ga ƴan Najeriya

2020 be one of our most try years as a nation

Asalin hoton, Twitter/BashirAhmaad

A yayin da Najeriya ma ta shiga sabuwar shekarar 2021, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa ƴan ƙasa jawabi.

A jawabin nasa mai tsawon minti 19, Shugaba Buhari ya ce a gaskiyar magana shekarar da ta wuce ta 2020 na daga cikin mafi wahala da tsanani da ƴan Najeriya suka gani sakamakon mummunan tasirin da annobar cutar korona ta yi wa tattalin arziƙi.

Shugaban ƙasar ya kuma yi magana kan ikon cin gashin kai na kasa da rashin tsaro da cin hanci da tattalin arziƙi.

"Kamar yadda muka, sani 2020 shekara ce mai tsanani, wannan shekara ta nuna jajircewarmu da ƙoƙarinmu na mu rayu a kowane hali, sannan ta ba mu sabon fata na fuskantar duk wani ƙalubale da ke gabanmu a shekarar 2021 da ma bayanta."

Ya kuma tuna tare da jimamin mutanen da ba su samu kai wa wannan shekara ta 2021 ba da suka mutu a 2020.

Sannan shugaban ya taɓo batun haɗin kan ƙasa inda ya ce Najeriya za ta ci gaba da wanzuwa da kasancewa dunƙulalliyar ƙasa ɗaya.

"Za mu iya tuna cewa a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 2020 ne muka yi bikin cikar ƙasar shekara 60 da samun ƴancin kai a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.

Shugaba Buhari ya kuma taɓo batun zanga-zangar EndSars, inda ya ce ya duƙufa wajen cika buƙatu biyar na matasa - waɗanda suka miƙa a yayin gudanar da zanga-zangar #EndSARS, wacce aka yi a shekarar da ta gabata.

Protesters hold banners as they walk along a road during a protest against the Nigeria rogue police, otherwise know as Special Anti-Robbery Squad (SARS), in Ikeja district of Lagos, Nigeria, 09 October 2020.

Asalin hoton, EPA

"Wannan gwamnatin tana ji, wannan gwamnatin mai sauraro ce kuma wannan gwamnatin a shirye take ta biya wa matasa buƙatun nan biyar da suka gabatar, tun da dukkanmu mun fahimci cewa muna yi wa Najeriya fatan alheri."

Ga dai ƙarin wasu abubuwan da Buharin ya fada a yayin jawabin nasa na sabuwar shekara ga al'ummar ƙasar.

  • Matasanmu su ne albarkar ƙasa mafi muhimmanci da muke da, a gida da kuma ƙasashen wajen. Fasaharsu da ƙwazonsu da son yin sana'o'insu a bayyane yake ga kowa.
  • Ta fannin matsalar tsaro da muke fama da shi a ƙasar nan, ina so na sake maimaita alƙwarin da na ɗauka kwanan nan, a lokacin da jami'an tsaro suka ceto yaranmu fiye da 300 da aka sace a makarantar sakandaren Kimiyya ta Ƙanƙara. Iya aikin da dakarun tsaro suka nuna da kuma haɗin kan da aka samu tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki a jihohi da gwamnatin tarayya tabbaci ne na cewa Najeriya za ta iya daƙile hare-haren ta'addancin da ake kai wa ƴan ƙasa.
  • Abin da muka sa a gaba shi ne mu farfarɗo da tattalin arziƙi ta hanyar bin tsarin faɗaɗa hanyoyin tattalin arziƙi wanda babban burin shi ne ƙasar ta wadatu da abincin da take samarwa.
  • Sauye-sauyen da muke a fannin wutar lantarki zai tabbatar da burinmu na samun isasshiyar wutar lantarki da mutane za su samu a gidajensu da masana'antu. Gwamnatinmu tana samar da shirye-shirye na musamman don samar da ayyukan yi da taimakon matasanmu a fannin sana'o'i.
  • A yayin da muke aiki da Majalisar Dokoki don tsara dokokin da za su ƙarfafa yaƙi da cin hanci, za mu sa ido mu sabunta dokokinmu don tabbatar da cewa wannan yaƙin ya ƙara ƙarfi sosai.
  • Ciyar da ƙasarmu gaba aiki ne na kowa da kowa a tare. Don albarkacin haka, kowane ɗan ƙasa na buƙatar ya bi dokokin kare yaɗuwar cutar Covid-19, ta yadda ƙasar za ta zama cikin aminci, a yayin da muke ta shirye-shiryen sayo da wadatar da kowa da allurar riga-kafin cutar korona.