US Capitol: Tarihin hare-haren da aka kai Majalisar Dokokin Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Hotunan yadda aka ga masu tayar d hargitsi sun abka wa ginin majalisar dokokin Amurka na US Capitol, a aniyarsu ta neman lalata sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar, ya matuƙar girgiza duniya.
Mutum hudu sun mutu sakamakon farmakin, wanda magoya bayan Shugaba Trump suka ƙaddamar bayan da ya kammala jawabi ga wani taron gangami a birnin Washington.
Shugaba mai jiran gado Joe Biden ya kira hakan a matsayin "yin fito-na-fito da hukuma da tawaye", yayin da mataimakin shugaban ƙasa Mike Pence ya ce tashe-tashen hankula ''wani mummunan abu ne a tarihin majalisar Amurka''.
Amma wannan ba shi ne karon farko da ginin majalisar - wanda ake dauka a matsayin wata cibiyar dimokaraɗiyyar Amurka - ya gamu da irin waɗannan tashe-tashen hankula ba.
Daga hare-haren bama-bamai zuwa kutsen 'yan kasashen waje, ga sauran lokuta hudu da aka taɓa kai wa majalisar dokokin hari.
Dakarun Birtaniya sun yi ƙoƙarin kone shi ƙurmus - shekarar 1814
Watakila za a iya cewa shi ne harin da ya fi ƙaurin suna wanda dakarun Birtaniya suka kai a lokacin yaƙin shekarar 1812.
Sojojin Birtaniya, ƙarƙashin jagorancin Vice Admiral Sir Alexander Cockburn da Manjo Janar Robert Ross - sun banka wa ginin wuta wanda a lokacin ana kan aikin gina shi, bayan da suka kutsa cikin birnin Washington DC a watan Agustan shekarar 1814 (ko da yake ginin ya tsira sakamakon saukar ruwan sama).

Asalin hoton, Getty Images
A wani martani kan Amurkawa kan 'ƙone babban lardin Upper Canada a birnin York shekara guda kafin kai harin, dakarun Birtaniya sun kuma banka wa sauran yankunan birnin da muhimman gine-gine wuta, da suka hada da Fadar White House.
Harin shekarar 1814 shi ne kawai lokacin da Birtaniyar ta ƙwace da kuma mamaye birnin na Washington.
A shekarar 2014, ofishin hulɗar jakadancin Birtaniya a Washington ya nemi afuwa bayan da a shafinsa na Twitter ya wallafa hoton ''ket'' na Fadar White House kewaye da abubuwan ƙyalƙyali, ''ana nuna murnar'' ƙone ginin shekara 200 a baya.
Harin nakiya na watan Yuli - shekarar 1915
Ƙarni daya bayan harin na Birtaniya, Erich Muenter, tsohon farfesan na Jamus a Jami'ar Harvard, ya tayar da sanduna uku na nakiya a dakin shakatawa na 'yan majalisar dattawa.
Fashewar ta lalata ginin, amma babu wanda ya hallaka.
Daga bisani Muenter ya ce harin wani martani ne kan masu tallafawa Amurka da kuɗi don ƙara wa Birtaniya ƙarfin gwiwar kai wa kasar Jamus farmaki a lokacin Yakin Duniya na daya.
Yayin da yake rubuce-rubuce ta hanyar amfani da sunan da na ainihin nasa ba a jaridar ''Washington Evening Star'', Muenter ya bayyana cewa yana fatan harin ''zai aike da saƙo mai ƙarfi ga wadanda ke son a yi yaƙi''.
Ya ƙara da cewa: ''Wannan fashewa wata manuniya ce kan saƙon da nake so in isar game da roƙon da nake na neman zaman lafiya.''
Kwana guda bayan harin, Muenter ya yi harbi tare da jikkata mai bayar da tallafin kudi JP Morgan Jr, kafin mai tsaron lafiyar Morgan ya yi masa ƙarfa-ƙarfa ya cafke shi. Daga bisani ya kashe kansa.
Harin da masu kishin kasar Puerto Rica suka kaddamar- shekarar 1954
A ranar 1 ga watan Maris na shekarar 1954, 'yan kasar Puerto Rico masu kishin kasa suka janye tutar tsibirin zuwa kasa, kana suka riƙa ihun "Yanci ga kasar Puerto Rico" yayin da suka bude wuta daga wuraren saukar baƙi na majalisar wakilai, tare da jikkata 'yan majalisa biyar.
"Ban zo don in kashe kowa ba, na zo ne in mutu saboda kasar Puerto Rico!" in ji shugabar, Lolita Lebron ta faɗa tana kuka, lokacin da aka cafke ta.

Asalin hoton, Getty Images
An yanke wa Lebron hukuncin daurin shekara 50, yayin da sauran mazan uku aka yanke musu hukuncin daurin shekara 75.
Daga bisani Shugaba Jimmy Carter ya soke duka hukuncin. Gwamnatinsa ta ce sakinsu ''zai kasance wani jin ƙai mai muhimmanci, kuma haka sauran ƙasashen duniya za su kalla''.
'Harin bam na kungiyar 'Resistance Conspiracy' - shekarar 1983
A ranar 7 ga watan Nuwambar shekarar 1983, wani bam ya fada ta ciki hawa na biyu na majalisar dokokin.
Minti daya kacal kafin fashewar, wani ya fito ya yi ikirari daga wata kungiya da ake kira 'Armed Resistance Unit', ya kira layin wayar cikin majalisar dokokin yana mai gargadin cewa akwai sauran wani harin da ke tafe, kuma ya ce wani martani ne kan matakin sojojin Amurka a kasashen Grenada da Lebanon.

Asalin hoton, Getty Images
Babu wadanda suka jikkata, amma akwai wata mummunar ɓarna da harin ya haifar.
A shekarar 1988, jami'an hukumar binciken masu aikata laifuka ta Amurka FBI sun cafke kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta 'Resistance Conspiracy' kan harin na majalisar dokokin da kuma wani harin bam na daban da aka kai a sansanonin rundunar sojin Amurka na 'Fort McNair' da na 'Washington Navy Yard' a shakarar 1983 da kuma 1984.
An ɗaure Linda Evans da Laura Whitehorn a gidan yari saboda hannu wajen kitsa lalata kadarorin gwamnati a shekarar 1991.
Amma yanzu an sake su.












