Majalisar Amurka ta ci gaba da zama bayan harin magoya bayan Trump

Asalin hoton, Reuters
Jami'an tsaro a Washington DC, babban birnin Amurka sun ce wata mata ta mutu bayan da suka harbe ta yayin da ta kutsa cikin ginin majalisar kasar tare da masu zanga-zanga da suka mamaye majalisar.
A sanadiyyar abubuwan ban mamakin da suka faru wadanda suka ba Amurkawa da ma duniya mamaki, Magajin Garin birnin Washington Muriel Bowser ta kafa dokar hana fita har zuwa safiyar ranar Alhamis.
Ta kuma gayyaci dakarun National Guard domin su taimaka wa 'yan sanda mai do da doka da oda a babban birnin na Amurka.
An kwashe dukkan 'yan majalisar kasar da ke cikin manyan zauruka biyu na majalisar dattawa da na majalisar wakilai, inda aka boye su a wasu dakuna da ke karkashin ginin domin kare lafiyarsu.
Michael McCaul, dan jam'iyyar Republican, wanda dan majalisar wakilai ne daga jihar Texas ya sanar da BBC yadda gungun masu zanga-zangar suka tsare shi a ofishinsa bayan ya garkame kofa.
Ya ce: "yayin da suka yi ta dukan kokar ofishina, na yi fargabar cewa za su balle ta, su shigo su yi ma na barna".
Ya kuma ce jami'an 'yan sanda sun yi nasarar tayar da wasu bama-bamai biyu, kuma an yi sa'a babu wanda ya sami rauni.
Masu zanga-zangar sun fasa kofofi da tagogin ginin majalisar, kuma 'yan sanda sun bude wuta domin hana daruruwan masu zanga-zanga mamaye ginin majalisar.
Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, wanda wannan harin ya rutsa da shi ya yi kira ga masu zanga-zangar da su janye daga titunan birnin domin zaman lafiya da kwanciyar hankali ya komo.
Tsofaffin shugabannin Amurka ma sun yi suka da kakkausar murya kan wannan abin da suka kira "abin takaicin da abin kunya" da ke aukuwa a yau a Amurka, ciki har da Barack Obama da George Bush.

Asalin hoton, Getty Images
A wani labarin mai alaka da abin da yake faruwa a Amurka, kamfanin Twitter ya sanar da cewa ya dakatar da shafin Mista Trump @RealDonaldTrump na tsawon sa'o'i 12 masu zuwa saboda yadda yake amfani da shafin yana yada labaran karya da su ka jibanci zaben shugaban kasa na 3 ga watan Nuwamba.
Twitter ya sanar da sauke wani bidiyo da shugaban ya wallafa, wanda da a ciki ya ke ikirarin an "sace" ma sa zabe.
Twitter ya kuma gargadi shugaban cewa za ta rufe shafin nasa idan ya sake taka dokokin amfanin da shafin.
Facebook ma ya dauki irin wannan matakin na sauke wannan bidiyon.
Amma duk da hargitsin da ya faru, 'yan majalisar sun ce za su ci gaba da aikin da su ke yi na tabbatar da Joe Biden a matsayin zababben shugaban Amurka, zaman majalisar da gungun masu zanga-zanga su ka tarwatsa domin su hana majalisar sauke wannan nauyin da tsarin mulkin kasar ya rataya a wuyanta.











