Hotunan yadda magoya bayan Donald Trump suka kutsa majalisar Amurka

Dubban magoya bayan Shugaban Amurka Donald Trump sun kutsa cikin ginin majalisar kasar da ke birnin Washinton DC, matakin da ya tilastawa 'yan majalisar neman mafaka da dakatar da muhawarar da su ke yi ta tabbatar da nasar Joe Biden a hukumance a maytsayin zababben shugaban kasar.

Supporters of Donald Trump clash with police officers in front of the US Capitol

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dare ya fara sauka a birnin Washington yayin da masu zanga-zangar ke ci gaba da mamaye ginin majalisar Amurka
A protester carries the Confederate flag into the US Capitol building

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan hoton na nuna wani mutum dauke da tsohuwar tutar 'yan aware ta 'confederate' bayan ya kutsa cikin ginin majalisar
Pro-Trump protesters break in to the US Capitol

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mai goyon bayan Trump sanye da kayan kamfen din shugaban yana daukan hotuna cikin ginin majalisar
One protester carries a plinth from a room in the US Capitol

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan mai zanga-zangar yana dauke da wani teburin yin jawabi daga wani daki a cikin ginin majalisar
Capitol police point guns at a protester from inside the Senate chamber

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan sandan majalisar Amurka sun fitar da bindigogi domin hana wasu masu zanga-zanga kutsawa cikin babban zauren majalisar
A protester hangs from the wall of the US Senate chamber

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani cikin magoya bayan Mista Trump yana kokarin yin haure domin kutsawa cikin ginin majalisar
US lawmakers and staff wear protective gear amid protests inside the Capitol

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda 'yan majalisa da ma'aikatan majalisar su ka sanya kayan kariya yayin harin da magoya bayan shugaba Trump suka kai a cikin ginin majalisar Amurka
A protester carries a flag that reads "Trump is my president"

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ga kuma wata mai zanga-zangar tana rike da tutar da ke cewa "Trump ne shugaba na"
A supporter of US President Donald Trump sits at the desk of US House Speaker Nancy Pelosi

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Bayan wannan mutumin ya kutsa cikin ofishin Nancy Pelosi, shugabar majalisar wakilai, ya bar ma ta wani sako da ke cewa "ba za mu ja da baya ba".
Capitol police detain protesters inside the building

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan sandan majalisar sun kama masu kutsen da dama kuma sun tsare su
Pro-Trump protesters break in to the US Capitol

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda aka rika sa-in-a tsakanin masu kutsen da jami'an 'yan sanda a cikin ginin majalisar
A US Capitol police officer shoots pepper spray at a protester attempting to enter the Capitol building

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ga kuma wani dan sanda na fesa wa wani mai kutse hayaki mai sa hawaye yayin da ya ke shiga ginin ta wata taga da ya fasa
Supporters of US President Donald J. Trump in the Capitol rotunda after breaching security

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Gomman masu kutsen suna cashewa bayan sun isa wani babban dakin majalisar
Trump supporters pose for pictures on the Senate dais

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Magoya bayan Mista Trump yayin da suka mamaye zauren majalisar, har suna daukan hotuna
A Trump supporter wears face paint at a protest in Washington, DC

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu cikin masu kutsen sun shafa wa fuskokinsu launi, kuma sun sanya kayan gargajiya
Leigh Ann Luck dressed up as the Statue of Liberty shouts as supporters of President Donald Trump gather near the Capitol building in Washington

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan matar mai goyon bayan Trump ta yi shigar mutum-mutumin nan na Statue of Liberty
President-elect Joe Biden speaks amid protests in Washington

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Zababben shugaba Joe Biden ya gaya wa Donald Trump ya "dauki matakin dakile" tashin hamkalin da ke faruwa
Twitter flags Donald J Trump's response to the protests as posing a "risk of violence"
Bayanan hoto, Twitter ya kulle shafin Twitter na Mista Trump saboda yana baza labaran bogi cewa an yi magudin zaben shugaban kasa
Supporters of US President Donald Trump protest outside the Capitol building

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Gabanin kutsawa majalisar Amurka, magoya bayan Donald Trump sun taru a gaban a cikin ginin majalisar

Duka wadannan hotunan akwai hakkin masu mallakar su.