Coronavirus: Yadda annobar ta shafi tattalin arzƙin wasu ƙasashen Afrika

Taswirar Afrika
    • Marubuci, Imam Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Bayan kasancewarta a matsayin cuta, annobar korona babban ƙalubale ce ga tattalin arziƙin duniya, musamman a Afrika inda yawancin ƙasashen nahiyar masu tasowa ne.

Tuni ta riga ta janyo wa tattalin arzikin nahiyar gagarumin naƙasu, kama daga kan harajin da gwamnati ke samu daga masana'antu da shige da fice zuwa man fetur da tafiye-tafiye da sauran hanyoyin samun kudin shiga.

Dalili kuwa shi ne, matakan da ƙasashen duniya daban-daban suka ɗauka na hana annobar bazuwa kamar dokar zaman gida da aka kafa da rufe kasuwanni da kuma tsayar da harkokin kasuwanci da na shige da fice.

Ƙasashen duniya da dama ciki har da Najeriya sun faɗa cikin masassarar tattalin arziki saboda korona, dalilin da ya sa ayyukan raya ƙasa ga jama'a su ma suka dakata.

Duk da cewa yawan waɗanda ke kamuwa da cutar a Afrika bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya, masana tattalin arziki na ganin cewa al'ummar nahiyar sun fi shiga tasku saboda yadda ta shafi tattalin arzikinsu.

Asusun bayar da lamuni na duniya IMF ya yi hasashen cewa zuwa ƙarshen 2020 tattalin arziƙin Afirka zai yi ƙasa da kusan dala biliyan 200.

Yayin da ake shirin bakwana da wannan shekara ta 2020, Imam Saleh ya yi duba tasirin da annobar korona ta yi ga wasu ƙasashen Afrika, musamman Najeriya da Nijar da kuma Ghana.

Wannan layi ne

Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, STATE HOUSE

Bayanan hoto, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

Bayan samun rahoton mutum na farko da ya kamu da cutar korona a Najeriya ne shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamiti na musamman da zai yi aikin yaƙi da annobar a Najeriya da kuma bijiro da matakan ganin ba ta shafi tattalin arzikin kasar ba.

Wasu daga cikin shawarwarin da kwamitin ya ba wa shugaban su ne na rufe wasu manyan filayen jirgin saman ƙasar domin hana shigowa daga waje, musamman ma ƙasashen da ake ganin cutar ta fi yaɗuwa a cikinsu.

Buhari ya gabatar da jawabi kai-tsaye ga ƴan ƙasar daga bisani, indda ya sanar da kafa dokar zaman gida wadda ta haɗa da rufe kasuwanni da filayen jirgin sama, domin hana yaduwar cutar.

Wane hali tattalin arzikin Najeriya ke ciki kafin zuwan korona?

A cewar Dr. Shamsuddin Muhammad, wani masanin tattalin arziki kuma malami a Jami'ar Bayero da ke Kano, tattalin arzikin Najeriya ya soma farfaɗowa dab da zuwan annobar korona, kamar a watan Oktoban 2019, inda cigaban ya kai kusan kashi 2.6 cikin 100.

''Hatta a farkon wannan shekara kafin rufe harkokin tattalin arziki, cigaban tattalin arzikin Najeriya na kan matakin ba yabo ba fallasa, ka ga kenan yana tsaka da yunkurin farfadowa daga kangin da ya shiga a baya'' in ji masanin.

Ya kara da cewa: "Amma kafin hakan, tattalin arzikin Najeriya ya fada cikin masassara daga 2017 zuwa 2018, kafin daga bisani ya fara farfadowa sannu a hankali a 2018 zuwa 2019,. Hatta a wata uku na farkon shekarar 2020 ma wato shekarar da annobar korona ta shigo, yana ci gaba da bunƙasa."

Ta yaya annobar ta shafi tattalin arziki?

A cewar Dr. Shamsuddin Muhammad, za mu iya kallon abin da cutar ta janyo wa Najeriya ta ɓangare biyu, ta fuskar 'ƴan kasa da kuma ta ɓangaren masana'antu masu zaman kansu.

''Ta fuskar ƴan ƙasa mutane da yawa sun rasa ayyukansu a dalilin wannan annoba, misali waɗanda suke ma'aikatan kamfanoni masu zaman kansu sun rasa ayyukansu domin kamfanoni da dama sun rufe saboda dokar kulle, sannan ba su da abin da za su ci gaba da biyansu da shi''. inji shi.

Sannan ya ce ko a ɓangaren ilimi ma makarantu da dama masu zaman kansu sun sallami malamai duk da cewa makarantu na cikin ɓangarorin da aka rufe, baya ga ɓangaren noma, waɗanda su ma duk an samu koma-baya.

A ɓangaren masana'antu kuma, a cewarsa an samu matsala biyu, ta farko masana'antun dokar kulle ta sa sun daina gudanar da al'amura, abin da ya jawo musu koma-baya, kamfanonin ma suka zama kamar kufai kamar ma ba'a shigarsu.

Sannan a ɗaya bangaren, masanin ya ce rashin zirga-zirga tsakanin ƙasashen duniya ya sa hatta kayan da za a sayo daga ƙasashen waje sai da aka dakatar da su sakamakon wannan annoba.

''Wadannan abubuwa sun jawo babbar matsala ga tattalin arzikin Najeriya, sannan ba wani abin mamaki ba ne don sun zamo silar faɗawar tattalin arzikin ƙasar cikin masassara a yanzu."

A halin da ake ciki, wani abu mai kama da zagaye na biyu na cutar ya kewayo, duba da yadda ake samun ƙaruwar waɗanda suke kamuwa da kuma mutuwa sakamakon cutar a kullum.

Wannan layi ne

Jamhuriyar Nijar

Shugaba Muhammadu Yusuf

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Nijar Mahamadou Isoufou

A Jamhuriyyar Nijar, ranar 19 ga watan Maris ne aka samu mutum na farko ɗauke da cutar korona a ƙasar.

Kamar Najeriya, ita ma ta dauki matakin hana tafiye-tafiye da kuma kafa dokar kulle a wani mataki na ƙoƙarin ganin an hana cutar yaɗuwa.

Kamar sauran ƙasashen duniya, tattalin arziƙin Nijar ya faɗa halin tasku sakamakon zuwan wannan annoba, kodayake tun kafin zuwanta da ma yana cikin wani yanayi.

Nijar na daga cikin ƙasashen Afrika masu tasowa da annobar korona ta janyo wa gagarumar matsala, ga kuma tarin matasa marasa aikin yi, kodayake adadin waɗanda suka kamu da cutar a ƙasar da ke shirin gudanar da zagaye na biyu na babban zaɓe, bai taka kara ya karya ba.

Wane hali tattalin arzikin ƙasar ke ciki kafin zuwan korona?

Tun kafin zuwan annobar korona Najeriya ta rufe iyakokinta da wasu ƙasashe da take maƙwabtaka da su ciki har da Nijar, abin da ya zaftare maƙudan kuɗaɗe daga ainihin harajin da ƙasar ke samu.

Soli Abdullahi, wani masanin tattalin arziƙi ne a ƙasar, ya bayyana mani cewa ''a lokacin, tattalin arziƙin Nijar ya shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi, halin bala'i da kuma ƙunci, abin babu kyawun gani kwata-kwata''. inji shi.

Baya ga haka akwai matsaloli waɗanda ba a rasa ba da korona ta tarar, sannan ta ƙarasa aikin.

Wane hali annobar ta jefa tattalin arziƙin ƙasar ciki?

A cewar masanin, shige da fice da aka dakatar da kuma hulɗar kamfanonin ƙasar da takwarorinsu na ƙasashen duniya ya jefa tattalin arziƙin ƙasar cikin halin ha'u'la'i.

''Hatta a cikin gida ma harkokin noma da masana'antun sarrafa kaya da kuma harkokin kasuwanci tsakanin 'yan kasa sun gurgunce.

''Kenan waɗannan duka al'amura suka sanya gwamnati ta daina samun kuɗin shiga, musamman waɗanda take samu ta hanyar kamfanoni da 'yan kasuwa masu kawo haja daga ƙasashen waje,

"Gwamnatin Nijar ba ta samun kuɗin shiga kuma ga shi ya zama dole ta biya bukatun jama'a ba tare da wani uzuri ba, nan kuɗi ba su shigo ba, nan kuma ya zama dole a kashe kuɗi, ka ga kenan an shiga halin gaba kura baya sayaki kenan."

Ya ƙara da cewa a lokacin da annobar ta shiga Nijar babu wani tsari da gwamnati ta yi na fuskantar ƙalubale irin wannan, ''Sai abu ya wakana ake ƙoƙarin a ga an cimma sa, da a ce mahukunta na da wani tsari tuntuni to da tasirin cutar bai shafi tattalin arziƙin kamar yadda ya shafe shi a yanzu ba."

A halin da ake ciki dai Nijar na daf da gudanar da zaben shugaban kasa a zagaye na biyu bayan jam'iyyu sun gaza samun kashi 50 cikin 100 na ƙuri'un sannan batun farfado da tattalin arzikin kasar da annobar korona ta kassara na daga cikin muhimman batutuwan da sabon shugaban ƙasar zai fuskanta.

Wannan layi ne

Ghana

Nana Akudo Addo

Asalin hoton, NANA AKUFO ADDO

Bayanan hoto, Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo

A ranar 11 ga watan Maris ne ma'aikatar lafiya ta Ghana ta sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar korona a ƙasar.

A ranar 30 ga watan Maris, ministan kuɗi na Ghana Hon Ken Ofori-Atta ya gabatar wa majalisar dokokin ƙasar jawabi game da tasirin da annobar ka iya yi wa tattalin arziƙin ƙasar da kuma irin matakan riga-kafi da gwamnati ta dauka na ganin cewa hakan ba ta faru ba.

Daya daga cikin matakan sun haɗar da bayar da tallafi iri-iri ga 'ƴan kasuwa ciki har da kafa wani shiri na tallafa wa waɗanda annobar ta fi shafa da zummar kare ayyukansu.

To sai dai kamar Najeriya da Nijar, ita ma Ghana ta rufe filayen jirgin samanta da kuma hana shiga daga kasashen waje, abin da ya gurgunta harkokin cinikayya da kasuwanci tsakanin kasar da sauran duniya.

Ko yaya tattalin arzikin ƙasar yake kafin korona?

Tambayar kenan da na yi wa Dr Shamsuddin Muhammad na Jami'ar Bayero, wanda ya ce da ma can tattalin arziƙin ƙasar na cikin halin ni-'ƴasu kafin ma zuwan annobar.

Ya ƙara da cewa rashin aikin yi tsakanin 'yan ƙasar ya ƙaru sannan harkokin cinikayya sun ja baya ba kamar da ba.

''Yawancin bashin da Ghana ke ci ya yi matuƙar ƙaruwa domin maganar da ake yi ita ce kasar ta ci bashin da ya kai dalar Amurka biliyan 43 - fiye da rabin tattalin arziƙin ƙasar baki ɗaya.

A cewar masanin, Ghana ta ci bashi iya wuya, domin har ta kai ga ƙasashen duniya na ɗari-ɗarin mu'amala da ita.

Yanzu wane hali tattalin arzikin ƙasar ke ciki?

Wani bincike da ya bibiyi naƙasun da annobar korona ta haifar musamman ta fuskar aikin yi a Ghana da aka gudanar da haɗin gwiwar Hukumar Raya Ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) da Bankin Duniya. ya gano ma'aikata kusan 770,000, wato kashi 25.7 cikin 100 na kasar ne aka zaftare wa abashi.

Baya ga haka, kamfanoni da masana'antu masu zaman kansu sun kori aƙalla mutum 22,000 daga aiki baki ɗaya saboda kasa biyansu albashi.

Binciken ya nuna cewa dokar kullen da aka kafa don yaƙi da bazuwar annobar ne ta taka gagarumar rawa wajen rasa ayyukan mutanen, da kuma rage albashin waɗanda abin ya shafa.

Ƙarƙarewa

Asusun bayar da lamuni na duniya IMF na rokon manyan ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziƙi su dubi halin da ake ciki su yafe ko da wani kaso ne na bashin da suke bin ƙasashen Afrika da annobar korona ta fi shafa.

Sai dai babu wata ƙasa daga cikinsu da ta sanar da ɗaukar irin wannan mataki har kawo yanzu, yayin da su kuma matalautan ƙasashen ke ta ƙoƙarin ganin sun tafiyar da harkokin mulki a haka.

Har yanzu kuma cutar korona na ci gaba da yaɗuwa a ƙasashen Najeriya da Nijar da Ghana da wannan tsokaci ya mayar da hankali kansu, kodayake hukumomi na cewa suna iya bakin kokarinsu don daƙile yaɗuwar annobar.

Dukkanin masanan da muka zanta da su yayin shirya wannan muƙala sun yi imanin cewa da ace ƙasashen Afrika na da wani shirin ko-ta-kwana na tarar irin wannan annoba, da kuwa tasirin da za ta yi bai kai wanda ta yi a yanzu ba.