Zaɓen Ghana: Ƴan hamayya sun yi fatali da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa

Babbar jam'iyyar hamayya a Ghana NDC ta yi shuri da sakamaon zaben shugaban ƙasa da aka gudanar ranar Litinin, da ya bayyana shugaba mai-ci Nana Akuffo Dankwa Addo a matsayin wanda ya samu nasara.
Ya samu kuri'a 6,730,413, kaso 51 cikin 100 na yawan ƙuri'un da ake son ɗan takara ya samu kafin yin nasara, yayin da abokin karawarsa John Dramani Mahama, wanda tsohon shugaban ƙasar ne ya samu ƙuri'a 6,214,889, wato kaso 47 cikin 100.
Wani na hannun daman John Mahama wato Haruna Iddrisu, ya ce jam'iyyarsu ba za ta karɓi sakamakon zaɓen ba saboda yadda aka samu shaidu da dama da ke nuna an yi maguɗi a zaɓen.
"Muna sa ran ɗaukar mataki kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisa, da zummar kawar da wannan abin kunya da ke zaman wani hari ga dimokraɗiyyarmu," in ji shi.
A jawabinsa na samun nasara a ranar Laraba, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Nana Akufo Addo, ya yi kira ga yan ƙasar su haɗa ƙarfi da gwamnatinsa don ciyar da ƙasar gaba.
Masu sanya ido na ƙasashen waje na kallon zaɓen a matsayin wanda ya gudana cikin lumana, ko da yake an kashe mutane biyar tare da raunata 19 a tashin hankalin da ke da alaka da zaɓen da ya gudana.
Al'amura sun sake dagulewa bayan da ɗan takarar jam'iyyar hamayya John Dramani Mahama ya zargi gwamnati da kokarin sace zaɓen.
Mahama mai shekaru 62, ya zargi shugaba Akufo Addo da amfani da sojoji a aniyarsa ta murde zaben, abin da gwamnatinsa ta musanta.
"Ba daidai ba ne ka yi amfani da sojoji don sauya sakamakon zaɓen a wuraren da kasan ba ka samu nasara ba, don haka ba za mu nade kafa muna kallo a kwace al'ummar Ghana hakkinsu ba.

Asalin hoton, Getty Images
Ba safai aka fiye samun zargin magudi a Ghana ba, kasar da ke kan gaba wajen samar da zinare kuma daya daga cikin kasashen da suka fi karko da tsarin dimokiradiyya.
A kuri'ar karshe da aka kada a shekarar 2016, Mahama ya amince da shan kaye a hannun Shugaba Nana Akufo-Addo kafin a sanar da kidayar karshe.
Hukumar zaben Ghana ta ce ta jinkirta fitar da sakamakon a hukumance zuwa ranar Laraba ne saboda kokarin kawar da duk wata matsala da ka iya tasowa.
Ana kallon Ghana a matsayin daya daga cikin kasashen Afrika da Dimukradiyya ta samu gindin zama a cikinsu.
Har kawo wannan lokaci magoya bayan shugaba mai ci na ci gaba da murna a sassan ƙasar, inda suke kiran hada kan kasa da kuma samar da karin ayyukan ci gaba.
A yanzu shugaban da aka zaba na fuskantar gagarumin kalubale musamman ta fuskar tattalin arzikin kasar da annobar korona ta lahanta, da kuma samarwa matasa aikin yi.
Tun 1992 da aka sauya kudin tsarin mulkin kasar ake mika mulki cikin lumana a Ghana duk da akan samu masu sukar sakamakon da ake samu.











