Fargabar tashin hankalin zabe ya zaburar da 'yan Ghana

There were long queues at some polling stations, like this one in Accra

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dogayen layukan masu zabe a Gaana

Yayin da al'ummar kasar Ghana ke shirin fita ranar Litinin domin zaben shugaban kasa da 'yan majalisa, hankula sun karkata ga yadda za a gudanar zabukan cikin kwanciyar hankali.

Hakan dai ya biyo bayan da Hukumar 'yansanda kasar ta fitar jerin sunaye wurare fiye da 6,000 a duk fadin kasar inda ta ce za a iya samun tashin hankali lokacin zaben.

Bayanin wanda hukumar 'yan sandan kasar ta fitar tun a makonni bayan na nuna cewa jihar Ashanti wanda garin Kumasi ke zaman babban birninta, ita ce ke da adadi mafi yawa na wuraren da ake jin za a iya samu tashin hankali daga cikin jihohin kasar 16 da kuma birnin Accra.

A cewarta akwai wurare 975 da za a iya samu tashin hankali a wannan jihar yayin da kuma bayan zabukan na gobe.

Wakilin BBC Haruna Tangaza ya ziyarci unguwar Abuabo da ke cikin birnin Kumasi, daya daga cikin wuraren da ake jin za a iya samun tashin hankalin.

Sai dai ya ce ya taras da matasa daga manyan jam'iyyun kasar biyu na NDC da NPP, da ma wasu kananan jam'iyuun zaune a cikin rumfa daya kowanne sayen da alamar jam'iyyarsa suna raha.

Kwanakkin ukun da suka wuce sun yi tattaki a unguwar da suka kira zaman lafiya duk domin ganin wannan has ashen da ake bai zama gaskiya ba.

Ahmed Tijjani Happy shi ne ya jagoraci tattakin:

"Saboda maganganun da muke ji wai za aiya samun rikici, kuma an ce unguwar Abuabo na cikin wuraren da rikici ka iya barkewa, shi yasa muka fito domin nuna wa duniya mu ba haka muke ba."

'Ba a bar manya a baya ba'

A yayin da matasa ke wannan su kuma dattawa a birni Kumasi sun shirya zaman addu'oi ne na ganin an yi zabuka lami lafiya.

Khalifa Abdurahman Ibrahim Ahmed Uda na daga cikin malaman suka halarci zaman addu'o'in da aka yi a jiya:

"Malumanmu sun duba halin da ake ciki, shi ne suka ga bai kamata su zauna haka ba kawai. Ya kamata su tattara kan dukkan Musulmin Ghana wuri guda domin yin addu'a, da komawa ga Allah. Wannan zabe da za a yi, Allah ya sa a gama shi lafiya."

Sarkin Zangon Kumasi Sultan Umar Faruk Saed ya ce da irin wadannan matakan da aka dauka akwai kyakkyawan fatan za a yi zabukan lami lafiya.

"Ina jin abin da mutane ke tsoro ba zai faru ba, domin idan ka duba, lokacin da ake rajistar masu zabe garin ya dauki zafi, amma yanzu komai na lafawa."

Su ma dai 'yan sandan kasar ta Ghana sun ce ba su yi sakaci ba bayan fitar wadannan bayanan.

Sun ce ko a baya sun jibge jami'ansu sun kuma shiga fadakawar ta kafafen watsa labarai kan illolin tayar da hankali a lokacin zaben.