Zaɓen Ghana na 2020: Bambanci tsakanin zaben Najeriya da na Ghana

Buhari da Addo

Asalin hoton, Other

Za a iya cewa Ghana da Najeriya su ne kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a yammacin Afrika. Ko baya ga ci gaban tattalin arzikin kasashen biyu sun yi kama da juna ta wasu fuskoki da dama tun ma ba fuskar siyasa ba, kamar tarihin mulkin mallaka da samun 'yancin kai da juyin mulki soji da kuma komawa kan tsarin dimokradiyya.

Amma ko da yake kasashe biyun kan gudanar da zaben sabbin shugabanni bayan ko wadanne shekaru hudu, akwai wasu abubuwa da suka bambanta tsarin zabe a kasashen biyu.

Matakan Zabuka

Najeriya dai na bin tsarin tarayya ne wato Fidraliyya. Tana da matakan gwamnati uku wato tarayya da jihohi da kuma kananan hukumomi.

A kowane mataki akan zabi shugaba da 'yan majalisa; wato shugaban kasa da 'yan majalisar tarayya, gwamnoni da 'yan majalisar jiha da kuma ciyamomi da kansiloli.

To amma Ghana ana bin wani tsari ne na jamhuriyya inda ake zaben shugaban kasa da 'yan majalisar tarayya da kuma kansiloli na kananan hukumomi kawai. Ba a zaben gwamnoni da 'yan majalisar jiha da kuma shugabannin kananan hukumomi, ko da yake kasar na da jihohin da kananan hukumomi.

Wanda ya lashe zaben shugaban kasa ne ke nada gwamnonin da kuma ciyamomi a kowace jiha ko kuma lardi kamar yadda ake kiransu a nan.

Tsarin lashe zabe

Yayin da a Najeriya ana bukatar dan takara ya samu kashi 25% na kuri'un a kashi biyu bisa uku na jihohin kasar da kuma ƙanƙanin rinjaye kafin ya lashe zaben shugaban kasa, a kasar Ghana ba haka tsarin yake ba.

Dan takarar shugaban kasa na bukatar samun kashi 50% na kuri'u da kuma rinjayen kuri'a daya ne kacal kan abokan karawarsa ya ci zabe. Wannan na nufin ko da kuwa a jiha daya ne ya samu dukkan kuri'u.

Zabuka na musamman

Yayin da a Najeriya akan yi manyan zabuka farat daya, a Ghana akwai tanadin zabuka na musamman wato special elections.

A kan gudanar da su ne kamar mako daya kafin gudanar da zabe domin bai wa jami'an tsaro da 'yan jarida da sauransu damar jefa kuri'unsu. Wannan saboda yadda suke zama cike da shugulla a ranar zabe.

Jefa kuri'a ta hannun wakili

matan ghana

A tsarin zaben Najeriya; dole wanda zai yi zabe ya je da kansa a rumfar zabe kuma da katinsa na jefa kuri'a sannan a bari ya yi zabe. Sai dai idan yana da wata lalura kamar ta rashin gani ko kuma tsufa da makamantansu zai iya kiran wanda ya yarda da shi ya taimaka masa wajen dangwalawa jam'iyyar da yake so.

Amma a tsarin zaben Ghana akwai abin da ake kira proxy voting. Tsari ne da ya amince mai zabe ya tura wani da katinsa a rumfar don ya jefa kuri'a a madadinsa ba tare da shi ko ita sun je rumfar zaben ba.

Wadannan dai su ne manyan bambance-bambancen da ke tsakanin wadannan manya kasashen biyu na yammacin Afrika masu gasa da juna.

Sai dai kuma ba a rasa wasu ƙananan bambance da ke tsakanin zabuka kasashen ba wadanda ba mu bayyana a cikin wannan sharhin ba.

Tambayar da za mu bar mai karatu da ita ita ce: Ko akwai abubuwan ya kamata kasashen biyu su kwaikwaya daga juna ta fuskar zabe?