Wasiƙa daga Afirka: Soyayya da ƙiyayyar da ke tsakanin Ghana da Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Cikin jerin wasiƙun da muke samu daga ƴan jarida daga Afirka, marubuciyar Ghana Elizabeth Ohene ta duba girman dangantakar da ke tsakanin Ghana da Niajeriya, ta la'akari da halin da ake ciki a yanzu na rashin jituwa game da rufe wasu shagunan ƴan Najeriya a Ghana.

Mun ɗauke su masu yawan surutu da neman rikici kuma mun yi imanin suna tunanin sun fi kowa wayo, musamman ƴan Ghana.
Sun ɗauka cewa mun kasance masu miƙa wuya, waɗanda ba su da wayo, kullum muna ci gaba kuma babu abin da damunsu fiye da yadda Ghana ke shan gaban Najeriya a komi.
Tun kafuwar ƙasashen biyu ake takun-saka tsakanin Ghana da Najeriya.
Lokacin da ina ƙarama, akwai ƴan Najeriya a dukkanin birane da ƙauyukan Ghana.
Muna tafiya makaranta tare da su kuma akwai wata mata ƴar Najeriya - "Mami Alata" kamar yadda suke kiranta - wadda ke sayar da komai kuma ko tsakiyar dare za ka iya tayar da ita ko da a ce dunƙulen suga za ka saya a daren.
Ƴan Najeriya sun mamaye kusan harakokin cinikayya da kuma garuruwan da ke haƙar lu'u-lu'u.
Ƙasashen biyu ba su yi iyaka da juna ba, amma kuma kamar suna makwabtaka da juna. Ƙasashen Togo da Benin ne suka raba ƙasashen - amma muna ji kamar maƙwabta.
Amma, wani abu ne da ke da nasaba da ƙasashen biyu kasancewarsu suna magana da Ingilishi da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka a tsakiyar ƙasashe da ke magana da harshen Faransa.
A bayyane yake, wani abin da zai yi da ƙasashen biyu kasancewar Ingilishi da Britishan mulkin mallaka na Burtaniya a tsakiyar ƙasashe masu magana da Faransanci.

Kafin samun ƴancin kai. da kuɗi ɗaya muke amfani haka ma jirgin sama. Sannan kotun ƙoli ɗaya ke shari'a tsakanin ƙasashen biyu.
Akwai wasanni da ake yi tsakanin makarantar Achimota da kuma Kings College.
Nasan wani aure da aka yi ta hanyar haɗuwa a wasannin.
A 1955, da Ghana ta doke Red Devils kamar yadda ake kiran tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya a lokacin.
An shafe shekaru da dama, ana muhawara tsakanin kasashen biyu kan ko wane fanni, abin da ya shafi ƙasa ko tsakanin al'ummar ƙasashen biyu.

Asalin hoton, Getty Images
Ghana ta samu ƴancin kai a watan Maris na 1957, yayin da abokiyar wasanmu Najeriya ta samu ƴanci a watan Oktoban 1960.
Wannan bai yi wa yan Najeriya da dama daɗi ba, suna ganin su ne manya su ya kamata ace sun samu ƴancin kai kafin ƙaramar ƙasa Ghana.
Za su iya kasancewa manya, amma a lokacin Ghana na ganin ta fi Najeriya arziki - kafin samun arzikin fetur.
Korar jama'a
Mun ci gaba da makwabtaka ta hamayya da kuma abota.
Sai kuma ga dokar gwamnatin jam'aiyya mai mulki a Nuwamban 1968, da ta buƙaci duk baƙin da ba su da takardu su fice Ghana
Duk da cewa akwai ƴan Togo da Burkina Faso da Ivory Coast da Nigeria da sauran ƴan ƙasashen yammacin Afirka, ƴan Najeriya yawancinsu Yarabawa daga kudu maso yammacin Najeriya su ne al'ummar ƙasashen waje da suka fi yawa a Ghana a lokacin.

Asalin hoton, Getty Images
Wasunsu sun shafe shekaru a Ghana, sai ake tunanin dokar ta shafi ƴan Najeriya ne.
Sai dai da Najeriya ta samu mai, ƙasar ta yi arziki, tattalin arzikin Ghana kuma ya taɓarɓare kuma daga 1974 komawar ƴan Najeriya na nan.
Malaman Jami'a da injiniyoyi da kafintoci da teloli kuma azuzuwanmu suka kasance wayau ba malamai a makarantun firamare da sakandare da makarantun gaba da sakandare.

Idan ka ga gida da ya kai wata daraja, dole ne ka samu mai aikin gida ƴar Ghana, ƴar Ghana mai dafa abinci, ɗan Ghana mai ban ruwa kuma malami ɗan Ghana a makarantun gwamnati da na masu zaman kansu.
A 1983 gwamnatin Najeriya ta sanar da korar duk baƙi waɗanda ba su da takardun zama a ƙasar.

Asalin hoton, AFP
Tun da ƴan Ghana suka fi yawa, sai ana ganin saboda su aka ɗauki matakin.
Sunan da ake kiran matakin da kuma jikar da yawancin ƴan Ghana ke ɗaukar kayansu, sai ya koma ana kira da "Ghana Must Go".
Ba makoma ba ce mai kyau komawa Ghana. Mun kasance cikin yanayi mafi ƙasƙanci yayin da muke sayen tolet fefa da man girki da za mu ɗauka zuwa gida.
Ƴan Najeriya ba za su taɓa yarda ba, tabbas, amma hakan da zafi kamar dokar korar baƙi ta Ghana a 1969.
Hulɗar Diflomasiyya
A hankali, mun koma mun sake gina dangantakarmu, saboda ba za mu iya yi ba sai da juna.
An kafa Ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka, Ecowas, 1975 kuma a matsayin manyan ƙasashen da ke magana da harshen Ingilishi muna buƙatar juna domin samun nasara.

Asalin hoton, AFP











