Rufe shagunan 'yan Najeriya a Ghana: Najeriya ta gargaɗi Ghana

Lai Mohammed

Asalin hoton, @FMICNigeria

Bayanan hoto, Ministan Yaɗa Labaran Najeriya - Lai Mohammed - ya ce Najeriya na duba hanyoyin ɗaukar matakan martani ga Ghana

Najeriya ta zargi Ghana kan abin da ta kira "cin zarafin 'yan kasarta a Ghana da kuma yadda hukumomin Ghanar ke ƙara matsa wa 'yan Najeriya lamba".

Wata sanarwa daga ministan yada labaran kasar, Lai Mohammed, ta ce an mayar da 'yan Najeriya a Ghana "wasu abin yi wa ba'a".

Lai Mohammed ya ce gwamnatin Najeriya na duba hanyoyin da za ta bi domin yi wa tufkar hanci, sai dai bai bayyana matakan ba.

A cewarsa, rashin kyautawar da Ghana ta yi wa Najeriya sun hada da: rushe wani gini na ofishin jakadanacin Najeriya a birnin Accra da iza ƙeyar 'yan Najeriya zuwa gida da rufe shagunansu.

Tun a farko wannan makon ne ministar harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey ta kira jakadan Najeriya a Ghana domin yi masa ƙorafi kan wasu kalamai da aka ce Najeriya ce ta yi.

An rawaito cewa ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama na cewa farmakin da ake kai wa masu kasuwanci ba bisa ƙa'ida ba a Ghana ana yi ne saboda ƙoƙarin cimma manufar siyasa.

A cikin jerin saƙonnin da ta wallafa a shafin Twitter, ministar ta bayyana kalaman a matsayin "abin takaici" sannan ta bayyana cewa gwamnatin Ghana ba ta da nufin cuzguna wa 'yan wata ƙasa.

Dokokin Ghana dai sun haramta wa 'yan ƙasashen waje buɗe shagunan sayar da ɗaiɗaikun kayayyaki, musamman ma a yankunan da ake kasuwanci.

'Yan kasuwa na cikin gida na matsa wa gwamnati lamba kan ta tabbatar an yi aiki da dokokin, kamar yadda wakilin BBC a Accra, Thomas Naadi ya bayyana.

Hulɗar difilomasiyyya tsakanin ƙasashen biyu ta taɓarɓare a 'yan watannin nan, bayan saɓani kan rufe shaguna da kuma rushe gini mallakin ofishin jakadancin Najeriya.