'Yan ƙwallon ƙafa a Ghana na 'tsoron' komawa fili saboda korona

Asante Kotoko v Inter Allies

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kocin Inter Allies ya ce 'yan wasansa "ba su shirya" komawa taka leda ba
    • Marubuci, Juliet Mafua
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa, Nigeria

Wasu 'yan wasa da masu horarwarsu a gasar ƙwallon ƙafar ƙwararru ta ƙasar Ghana sun shaida wa BBC cewa "a tsorace suke" da su koma ci gaba da taka leda kuma ma "ba a shirye suke ba".

Wannan na zuwa ne duk da yadda hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar take zumuɗin komawa filayen wasanni, inda har ma ta yarda a koma a tsakiyar watan Agusta.

Sai dai Ghana Football Association (GFA) za ta fi son a ci gaba da murza leda a watan Oktoba.

An dakatar da ƙwallon ƙafa a Ghana tun a watan Maris sakamakon annobar korona, wadda ta kama mutum fiye da 32,000 a ƙasar.

Sai dai wasu 'yan wasa da kociyoyinsu sun faɗa wa Sashen Wasannin Afirka na BBC cewa suna tsoron kada wasu 'yan wasa su kamu da cutar.

"Ba mu shirya komawa taka leda ba," in ji Tony Lokko, kocin ƙungiyar Inter Allies.

"Ina ta yin magana da 'yan wasana kuma suna ce mani a tsorace suke. Ku duba yanayin, dukkanmu a tsorace muke da cutar.

"Kayayyakin lafiyar da ya kamata mu yi amfani da su ba a kawo ba kuma shi ne abin da kowa yake jin tsroro a yanzu."

Har zuwa yanzu GFA ba ta bayyana yadda za a koma ci gaba da wasannin ba kuma har yanzu ba ta amsa buƙatar BBC ba game da damuwar da ƙungiyoyin suka nuna.

Yayin da ƙungiyoyin ƙasashen Turai ke ɗaukar matakai na lafiya domin komawa wasanni - Premier League kaɗai ta kashe fan miliyan huɗu don sayen kayayyakin gwajin cutar da kuma yi wa 'yan wasa da kociyoyi 40 gwaji sau biyu a kowane mako - Ghana ba ta da kuɗin da za ta yi hakan.

Lokko ya ce: "Ba mu da kayan aikin da aka sharɗanta domin kare kai daga na ɓangaren 'yan wasa da kociyoyi."