Zaɓen Ghana: Ƴan ƙasa na kokawa kan rashin morar romon dimokraɗiyya

    • Marubuci, Haruna Shehu Tangaza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Abuja

Haruna Shehu Tangaza Na Sashen Hausa na BBC ne ya rubuto mana wannan labarin daga ƙauyen Abrim jihar Ashanti a Ghana.

Wata mace a Ghana

Kimanin shekara 28 kenan da kasar Ghana ta koma kan turbar dimokradiyya a jamhuriyya ta hudu. Kamar yadda batun yake a kasahe da dama na Afrika, masu zabe a yankunan karkara na kan gaba a Ghana wajen jefa wa 'yan siyasa ƙuri'un da ke kai su ga dare madafun iko.

To sai dai galibin yankunan karkarar masu zaben sukan tura mota ne ta baɗe su da ƙura.

Alhassan Adamu mai shekara 64, na sana'ar tuƙa babur mai taya uku ne a ƙauyen Abrim na jihar Ashanti.

Ita ce dai ya dogara da ita wajen ci da kansa da iyalansa bayan durƙushewar sana'arsa ta kawata riguna.

Ya ce tun komawa kan tsarin dimokradiyya a 1992 yake jefa kuria, amma duk haka ƙauyen nasu na kamfar muhimman ababen more rayuwa.

"Hanyoyi dai ba su da kyau a nan saboda yanzu haka ni kaina ban da lafiya saboda yadda hanyar take girgiza ni yayin da nake gudanar da sana'ata'' in ji shi, yayin da zantawa da BBC a lokacin da yake jiran fasinja a wata tasha da ke ƙauyen.

Ya ƙara da cewa ko baya ga rashin hanya suna fama da rashin wasu muhimman ababen more rayuwa kamar ruwan famfo da wuraren zubar da shara; abin da ya ce taimakawa wajen yaɗuwar cututtuka.

Wata matashiya a Ghana

Sai dai ba masu sana'ar sufuri irin su Malam Alhassan ne kawai ke damuwa da rashin kyawun hanyoyi a wannan gari ba.

Ga alama masu maƙwataka da hanyoyin marasa kyau irinsu Zainab Ahmadu sun fi fusata da yadda ta ce shugaba bayan shugaba ke shuɗewa ba tare da cika musu alƙawarin gyara musu hanyoyi ba.

"Shugaba Rawlings ne ya yi wannan hanyar sai ta lalace. Sai aka ɓamɓare ta da sunan za a gyara. Yau shekara 16 kenan tun zamanin John Kufuor bai gyara ta ba. Atta Mills ya zo bai samu gyarawa ba har ya rasu."

Wani mutumin Ghana

Ta ce haka dai shugaban bayan shugaba ke alkawarin gyara hanyar mai muhimmanci a gare su amma ba su yi ba har zuwa wannan lokaci. Tare da haka inji ta an bar sub a ruwan fanfo da asibiti da makarantu.

Sulaiman Yunus wani matashi a kauyen na Abrim ya ce tun tashinsa bai taba ganin ruwan fanfo a kauyen nasu. A wajensa karan dimokradiyar kasar ta Ghana bai kai tsaiko har yanzu duk da kwashe shekaru kusan talatin ana yi babu katsewa.

Motoci na wucewa a wata hanya a Ghana

Wakilin BBC da ya ziyarci yankin ya kuma yi kicibis da Raula - a bakin wata rijiya inda take zuwa kullum domin samun ruwan sha da amfanin yau da kullum.

Duk da shekarun ta 15 kawai a duniya ta ce tuni ta fara fama da ciwon jiki saboda jan ruwa daga rijiya.

"Muna wahala wajen samun ruwa domin rijiyar akwai zurfi sosai; don haka idan kana ɗibar ruwa bayanka da kuma hannuwanka duk za su rika yi ma ciwo," in ji wannan budurwar.

Ko da yake shekarun ba su kai na jefa ƙuri'a ba Raula na fatan shugabannin za a zaɓa a wannan karon za su saka wa ƙauyen nasu ruwan famfo domin sun dai wannan wahalar.

Tare da waɗannan matsalolin dai, ga alamu al'ummomi yankunan karkara a nan Ghana a shirye suke su shiga a yi dasu a wannan zaben da ke tafe bisa fatan cewa wadanda suka zaɓa za su share musu hawayensu.

Wata yarinya na diban ruwa a rijiya a Ghana