Matar da ta gutsure mazakutar mutumin da zai yi mata fyaɗe a Ghana

Domestic violence victims don speak to BBC News Pidgin

Wata mata mai shekara 24 ta cizge wani ɓangare na mazakutar wani mutm wanda ake zargi ya yi yunƙurin yi mata fyaɗe a Ghana bayan ya nemi ta sanya bakinta a gaban nasa.

Wannan lamarin ya faru ne a Obuasi, da ke yankin Ashanti, yayin da wanda ake zargi da fyaɗen ya kutsa kai cikin ɗakin Huanita da tsakiyar dare. Kakakin 'yan sandan yankin Ashanti Godwin Ahianyo ya tabbatar da faruwar lamarin ga BBC.

Rahoton da 'yan sanda suka samu ya ce, "Mutumin ya nemi da ta sa baki a gabansa ne lokacin da ita kuwa ta cizge wani ɓangare na al'aurar tasa."

Mutumin da ake kira Emmanuel Ankron, mai shekara 23, ya faɗa ɗakin 'yar makarantar ne da adda a hannunsa da kuma wata bindiga ƙirar gida.

Bayan ya sace kuɗinta, ya ɗauke talabijin ɗinta da waya sai kuma ya nemi ta yi wasa da gabansa.Ana tsaka da hakan ne sai ta gartsa masa cizo. Sai jini ya fara fita daga jikin mutumin sai ya fice a guje daga ɗakin.

Juanita, cikin kaɗuwa ta garzaya wajen yan sanda don shigar da ƙara sannan ta wuce asibitin Anglogold na Ashanti don a duba lafiyarta.

Sai ta fahimci cewa shi ma wanda ''ya yi yunƙurin yi mata fyaɗen,'' wannan asibitin ya je don a duba shi, inda nan da nan ta yi kururuwa aka kama shi.

'Yan sanda sun nemo guntun mazakutar mutumin da Juanita ta gutsire, yayin bincike kan lamarin.

Hukumomi sun ce mutumin ya matuƙar jigata bayan da ya gama yi wa matashiyar fyaɗe a karon farko.