Coronavirus: Shin Najeriya ta shiga mataki na biyu na hauhawar cutar korona ne?

Mace da takunkumi a Legas

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Tun bayan da gwamnatin Najeriya ta yi umarni a sake buɗe wuraren killace masu ɗauke da cutar korona da ke faɗin kasar, mutane da dama ke tambayar ko dai cutar ta sake hauhawa ne a karo biyu.

Umarnin gwamnatin ya biyo bayan yadda ake ci gaba da samun ƙaruwar sabbin waɗanda suka kamu da cutar korona ne a ƙasar.

Rahoton hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya (NCDC) ya nuna cewar an samu ƙarin mutum 675 da suka kamu da cutar korona a ranar Alhamis.

Wannan shi ne karo na biyu da aka samu adadi mafi yawa na waɗanda suka kamu da cutar korona a ƙasar, baya ga wanda aka samu a cikin watan Yunin da ya gabata, inda aka sami mutum 745 da suka kamu da cutar a wancan lokaci.

A wani saƙo da NCDC ta wallafa a shafinta na Tuwita ya nuna cewar an samu sabbin waɗanda suka kamu da cutar a jihohi 16, kuma Abuja ce kan gaba da mutum 183 da suka kamu, sai Legas da ke biye mata da mutum 128.

Haka zalika a Kaduna mutum 85 suka kamu da cutar ta korona, sai Kwara mai mutum 57, da Katsina mai mutum 50, sannan ita ma jihar Kano an samu mutum 33, sannan Bauchi na da mutum 10.

Duk da ƙaruwar sabbin waɗanda suka kamu da cutar ta korona da alama har yanzu al'ummar kasar ba sa kiyaye matakan kare kai daga kamuwa da cutar.

Hakan tasa ƙwararru ke fargabar sake dawowar annobar a karo na biyu, da irin hadɗrin da za a iya fuskanta idan ba a kiyaye matakan kariyar ba.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Dr Nasiru Gwarzo wani ƙwararren likita ne a Najeriya kuma ya ce "shi ilimi na kimiyya ba mutum ɗaya ne ke bugar ƙirji ya ce zai yi bincike a kansa ba, sai an yi muhawara an dudduba abubuwan da suka yi cikakken bayani, na yawan adadin mutanen da yawan yaɗuwar, sannan sai a fitar da bayani da cikakkun hujjoji cewa lallai an shiga wannan mataki na hauhawar cutar a karo na biyu.

"Akwai haɗari babba idan aka ce an ɗauki abu da muhimmanci, to idan aka ce an samu sassauici na tunani da tsoro da damuwa, aka ƙi ɗaukar abin da muhimmanci, to idan ya tashi yin mamaya zai yi ɓarna mummuna.

Ko a ranar Larabar da ta gabata sai da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i ya ayyana yiwuwar sake rufe jihar ganin yadda adadin ke ƙara hauhawa.

Riga-kafi

Alamun cutar korona

Sai dai yayin da ake tsaka da wannan fargabar gwamnatin Najeriya ta ce tana ɗaukar matakai na yadda za ta ajiye riga-kafin cutar korona da ake shirin kawowa ƙasar miliyan 20 a farkon shekara mai zuwa.

Sannan ta ce za ta bai wa ma'aikatan ɓangaren lafiya da ƴan kasar marasa ƙarfi fifiko wajen bayar da riga-kafin cutar ta korona.

Sannan za ta kasance cikin shirin ko ta kwana, biyo bayan yadda ake samun ƙaruwar kamuwa da korona a yankin Turai da Amurka, tare da shawartar ƴan kasar da su gujewa tafiya-tafiye zuwa wasu ƙasashe saboda hadarin kamuwa da korona virus.

Birtaniya ce ƙasa ta farko da ta fara amfani da riga-kafin cutar korona a duniya.

A yanzu dai adadin waɗanda suka mutu sakamakon cutar korona ya kai 1,190 a ƙasar.