Coronavirus: Aurarrakin da cutar korona ta kashe a faɗin duniya

- Marubuci, Daga Emma Ailes
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
A faɗin duniya kama daga Kudancin Amurka zuwa Yammacin Afrika - iyalan da a baya suke zaune cikin farin ciki a yanzu suna rabuwa wasu ma abin yana kai wa ga saki.
Wasu na ɗora alhakin haka kan wahalhalun da annobar cutar korona ta janyo, wasu kuma na cewa ta bankaɗo wasu matsaloli da aka manta da su a baya.
"A lokacin annobar cutar korona na gano mijina yana da budurwa," Reni ta gaya mana ta waya daga gidanta a Najeriya. Mun yi ta jin hayaniyar iyalanta da ƙarfi a ɗaya ɗakin, suna ta buga kwanuka da zummar jiran abincin dare.
"Na same shi gaba da gaba a kanta, ya tambaye ni da ya yi mani me ya sa kika taɓa wayata?'' Wannan ba ƙaramin cin fuska ba ne. Ina ganin kawai so yake ya sake ni. Bai ma san muna magana ba yanzu, shi ya sa ba zan iya nuna fuskata ba."
Zama a ɗan ƙaramin waje tare ko da yaushe, da yawanmu sun gaza yin haƙuri da juna, musamman lokacin rainon yara da yadda ake rarrashinsu, da kuma ayyukan cikin gida ko kuma daga gida.
Ga damuwa game da harkar lafiya, matsalar kuɗi da kuma yanayin da duka duniya ta samu kanta ciki, matsalar korona da ta'addabi duniya ta bar mu cikin fama da rikicin gida.
A wajen wasu da dama, kamar Reni, wannan zaman kulle na nufin bankaɗo wani sirri- kuma na nufin za ta janyo matsalar da ba a yi zato ba.
Annobar ba ta yaɗa komai ba
Adadin ma'auratan da suka rika neman shawarwari kan zamansu ya ƙaru a lokacin kulle.
"Mafi yawan masu zuwan ɗaiɗaiku ne," in ji Rebecca Baum da ke shugabantar wajen. "Tun daga lokacin da aka fara kulle aka riƙa fargarwa daga mutane kuma mafi yawa ma'aurata."
Dakta Marni Feuerman, ƙwararriya ce kan halayyar ɗan adam, ta ce: "Babban abun da na riƙa ji a tsakanin ma'aurata shi ne gardama kan yadda za a raba ayyukan gida tsakaninsu," in ji ta. "Mutane na ƙoƙarin aiki tare da kula da yara a gida - komai yanzu ya koma faɗa."
Damuwar kowa da kowa
Wani bincike da wata kungiyar taimako ta Burtaniya ta yi ya gano cewa, kashi daya cikin huɗu na waɗanda suka yi zaman kullen sun ƙara samun damuwa sama da wadda suke da ita a baya.
Irin wannan adadi sun ce abokan zamansu na ɓata musu rai a lokacin da suke tare a gida, mata da yawa kuma sun koka kan mazajensu.
Dokar kullen ta ƙirƙiro rabuwar muhalli in ji ƙungiyar ba da agajin, yayin da mutane ke ƙara gano wasu ɓoyayyun abubuwa da ke cikin zamantakewarsu - masu kyau da munana.
Wani binciken da kungiyar dai ta yi a watan Yuli ya gano kashi takwas cikin 100 na mutane na cewa sun gano akwai buƙatar su rabu da abokan zamansu - yayin da kashi huɗu cikin ɗari ke cewa dokar kusanci ta ƙara musu.
A wajen Reni, dokar kullen ta yaye wani labule da ya rufe alaƙar aure, ta ce a mafi yawan lokuta tana bibiyar mijinta ne kuma ta gano sabbin halayya tare da shi, wadda hakan ya sanya ta duba wayarsa.
Haka ya janyo tambayoyi shi ko "Ina san shi? ba na zaton haka gaskiya. Ina dai fatan ya daina kula ta kwata-kwata. Amma dai ina jin daɗi na gano komai, na samu kwanciyar hankali kan cewa mummunar halayyarsa ba laifina ba ne."
Shawarwarin zamantakewa yayin kullen korona
Kate Moyle, wata kwararriya a bangaren sanin halayyar ɗan adam ta ce"
- Yayin kullen, in muka lura da wata baƙuwar halayya da ke ɓata mana rai, in za mu yi magana a kai mu guji cewa, "NI" ko "INA" a maganganunmu, kamar "Na ga ka sauya halaye, Ina jin ba ka sona" gwara a rika cewa "Kamar ka sauya hali".
- Da yawan ma'aurata na ƙorafin zama tare da abokan zamansu - amma kaɗan ne ke zaman lafiya. Yana da kyau a ce a matsayin ma'aurata ana rayuwa tare, amma yana da muhimmanci kuma a riƙa bai wa juna iska, ko da kuma ana zaune gida ɗaya.
- Wannan lokacin bai dace da rabuwa ba, yana da kyau a riƙa tuntuɓar 'yan uwa da abokan arziƙi don neman taimako, da kuma gwada yadda za ka rika sanya kanka da kanka farin ciki.
Bayanan da aka samu a farkon wannan shekarar daga Saudiyya da Indonesia da birnin Xi' na China da Dzahou sun nuna ƙaruwar neman sakin aure a hukumance.
Sai dai a gefe ɗaya Farfesa Brad Wilcox na jami'ar Virginia ya yi gargaɗin a rika yi wa wannan abu kuɗin goro ana cewa an samu ƙaruwar a ko ina.
Bayanan da muka samu daga jihohi hudu cikin biyar kan matsalar saki a wannan lokaci - Arizona da Florida da Missouri da Rhode Islanad fa Oregon - sun nuna an samu raguwar sakin sosai," in ji shi.
Wani magidanci a Amurkan ya ce yana ganin wannan dokar kullen da ƙara matso da lokacin rabuwar aurensu da matarsa, da suna maganar sayan gida tare, amma daga baya ta ji ba ta buƙatar hakan, ta fi son zama ita kaɗai.
Duk da cewa Kieron ya sanya kansa a harkar atisaye a kullum amma raɗaɗin rabuwarsu na damunsa, hakan kuma ya so taɓa kwakwalwarsa.
"Bayan mun rabu, Melbourne ta nemi a dawo a zauna tare cikin dokar kullen. Amma duka tunaninmu kar abin ya ƙara munana a nan gaba, sai da ya kasance ina kuka da idanuna."
'Ba rabuwa nake buƙata ba'
A Brazil Richard da Rafaela sun yi ƙoƙarin lulluɓe matsalarsu da kuma kawo ƙarshen aurensu cikin ruwan sanyi suka amince su zama abokai. Rafaela ta koma wani gida a kusa. Suna ganin juna kullum, tare da jin halin da yaransu biyu ke ciki.
"Dokar kullen ta sanya mu tunkarar matsalolinmu tare da kawo ƙarshen aurenmu ba tare da hayaniya ba," in ji Richard.
Rafaela tana wurin sai ta girgiza kai ta ce, "Ba rabuwa ba ce buƙatata". Amma fa ba ni da wani zaɓi da ya wuce hakan, mu biyun duka mutanen kirki ne, ina ganin dukanmu mun cancanci zama cikin farin ciki."
Mun yi amfani da wasu sunaye ne na daban don ɓoye sirrin waɗanda muka yi magana da su.











