Masana kimiyya sun yi katarin samun hoton duniyar jupiter

Asalin hoton, Gemini Observatory/M.H.Wong et al
- Marubuci, Daga Jonathan Amos
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Science Correspondent
Masana ilimin taurari sun samar da wani sabon hoto na Jupiter da ke bibiyar yankuna masu dumi da ke buya a saman giza-gizai.
Kamfanin Gemini North Telescope mai sanya ido kan taurari ne ya dauki hoton a Hawaii, wanda wannan ne sanya ido ne mafi daidai da aka yi a duniya da aka taba yi tun daga tushe.
Domin cimma wannan buri na dauko hoton, masana kimiyya sun yi amfani da wata dabara da ake kira "lucky imaging" wanda ya nuna yadda duniyar take cikin yanayin dishi-dishi.
Wannan hanyar ta hadar da samar da kariya daga abin da aka hara tare da tarrara bangarorin hoton inda iska ke matsakaiciyar kadawa.
Yayin da aka dauki duka hotunan an hada su waje daya cikin wani zane, wanda ya samar da wani abu da ya fi hoto guda daya.
Hoton da aka dauka na zanen duniyar, ya fi irin wanda aka saba gani na (Hubble telescope) taurari tsayi. Ana iya ganin wucewar hazo da kuma 'yan kanan giza-gizai a saman duniyar ta Jupiter, wanda zai bai wa masana kimiyya damar zurfafa bincike kan yadda cikin duniyar yake.
Masu bincike na son kara fahimtar mene ne ke samar da tsarin yanayin a duniyar, kuma takamaimai doguwar guguwar da ake samu da takan kai shekara 20 zuwa 100.
Cibiyar California da ke Berkeley ce ta jagoranci wannan binciken da ya samar da hoton zanen bakin wutar. Kuma wani bangare ne na wani shirin hadin gwiwa da ya hadar da Hubble da kuma Juno masu bibiyar sararin samaniya wadanda yanzu haka ke bibiyar duniya ta biyar daga rana.

Abin da za mu sani game da duniyar Jupiter
- Duniyar Jupiter ta fi wannan duniyar ta Earth fadi sau 11, kuma ta fi ta girma sau 300.
- Shekara 1 a Jupiter ita ce shekara 12 a irin wannan duniyar da muke ciki - kwana daya a wannan duniyar kuma shi ne awa 10 Jupiter.
- Abubuwan da suka hada duniyar sun yi kama da tauraro - kuma mafi yawanta sinadaran hydrogen da helium ne
- Idan ya ji wuta sosai, sinadarin hydrogen yana komawa kamar karfe

Asalin hoton, NASA/ESA/A.Simon

[email protected] and follow me on Twitter: @BBCAmos











