Labaran ƙarya na son kawo cikas ga zaman lafiya a zaɓukan Nijar

Wata matsala da ke mamaye fagen siyasar Jamhuriyyar Nijar a yayin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓe ita ce ta yawaitar labarun ƙarya a shafukan sada zumunta.
Wasu na amfani da kafofin na zamani don yaɗa labarin da suke so don ɓata suna ko ma aibata wani, abin da ake gani zai iya kawo cikas a ƙoƙarin da ake na shimfiɗa zaman lafiya a lokacin zaɓe.
Lamarin na ci wa al'ummar ƙasar tuwo a ƙwarya musamman a ƴan kwanakin nan da ƙasar ke tunkarar babban zaɓen 2020. Ƴan siyasa na amfani da matasa da dama don yaɗa munanan manufofinsu tsakanin al'umma.
Masu sharhi na ganin cin zarafi ko ƙasƙanci ko aibata wani ɗan siyasa abokin hamayya su ne muradun da ake son cimma ko da kuwa hakan zai kawo ruɗani da ma hargitsi cikin ƙasar.
Wani labarin da ake ta yaɗawa tun a ranar Litinin shi ne na cewa kotun tsarin mulki ta soke takarar Mohamed Bazoum, har labarin ke cewa kotun ta umurce shi da ya katse yaƙin neman zaɓen da yake yi ya dawo Yamai.
Sai dai Waziri Idrissa kakakin ɗan takara Bazoum Mohamed ya ce labarin ƙarya ne, ɗan takarsu na cikin jihar Damagaram yana tafiyar da yaƙin neman zaɓensa kamar yadda doka ta tanada.
Abdoulkadri Omar Alfa, shi ne ɗan takarar shugabancin ƙasar ne da shi ne ya shigar da ƙarar a kotun tsarin mulki ya ce zancen ƙarya ne ake yaɗawa, don kawo yanzu kotun ba ta kammala aikin binciken da take kan wannan ɗan takara ba.
Matasan dai sun ce irin waɗannan halaye da ƴan uwansu ke nunawa duk kuwa da ƙoƙarin da aka sha yi na wayar musu da kai da su daina zama karnukan farautar ƴan siyasa na ba su takaici, suna masu kira gare su da su guji ire-iren waɗannan wallafe-wallafe.
Ko baya ga kiraye-kirayen da ƙungiyoyi da dama ke yi na a zauna lafiya, hukumar zaɓen ƙasar mai zaman kanta ta CENI ta sha yin zama da masu amfani da shafukan sada zumunta inda suka sha nuna masu aibin yaɗa labarin ƙanzon kurege.











