Kotu ta haramta wa Hama Amadou takarar shugabancin Nijar

Kotun tsarin mulki a jamhuriyyar Nijar ta yi watsi da takarar madugun adawa na ƙasar Hama Amadou.
A wata sanarwa da ta karanto gaban manema labarai a Yamai ranar Juma'a, kotun ta bayyana sunayen ƴan takarar da suka cika dukkan sharuɗɗan da dokokin ƙasar suka shata.
Ƴan takara 30 ne suka yi nasarar ƙetara siraɗi daga cikin ƴan takara 41 da takardunsu suka je wa kotun.
Daga cikinsu akwai ɗan takarar jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarraya Bazoum Mohamed da yanzu haka wasu ƴan adawa suka shigar da ƙararsa kotu, suna kalubalanta takardarsa ta zama cikakken ɗan kasa.
Sai dai 11 daga cikin ƴan takarar har da ɗan takarar jam'iyyar adawa ta Moden Lumana kuma madugun adawar ƙasar Hama Amadou.
Matsalar safarar jarirai daga tarrayar Najeriya da wata kotu a Yamai ta kama Hama Amadoun da laifin aikatawa, ta kuma yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara ɗaya ce ta zama ummul'aba'isin rashin sa shi daga kotun tsarin mulkin.
A tsarin mulkin Nijar rashin amincewa da takarar ta Hama Amadou da sauran ƴan takarar 10 na nufin ba za su je zaɓe ba, ta hakan kuma jam'iyyun su ma ba za su je zaɓen shugaban ƙasa ba.
Ranar 27 ga watan Disamba mai zuwa ne ake gudanar da zaɓen shugaban ƙasar zagaye na farko da ƴan takara 30 za su fafata.











