Zaben Nijar: Bazoum Mohamed ya naɗa ɗan Mohammadou Issoufou shugaban yaƙin neman zaɓensa

Asalin hoton, @Mohamed Bazoum
Ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyya mai mulki a Nijar Mohamed Bazoum, ya naɗa ɗan shugaba Mahamadou Issoufou, a matsayin jagoran yaƙin neman zabensa.
Wakiliyar BBC a Nijar ta ce Bazoum ya sanar da naɗa Sani Mahamadou Issoufou a matsayin jagoran yaƙin neman zaɓensa a wani taron yaƙin neman zaɓensa.
Sai dai babu wata sanarwa a hukumanci daga Jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya kan nadin ɗan shugaban ƙasa a matsayin jagoran yaƙin neman zaɓen Bazoum.
Bazoum Mohamed shi ne ɗan takarar jam'iyyar PNDS tarayya ta shugaba Mohammadou Issoufou a zaben Nijar da za a yi watan Disamba a Nijar.
Bazoum ya bayyana Sani Mahamadou Issoufou wanda mahaifinsa ya ba muƙami a fadarsa a 2016 a matsayin ɗansa.
Sai dai masu sharhi na ganin ba ya ta wata ƙwarewa ta siyasa, kuma matakin na iya haifar da saɓani tsakanin shugabannin jam'iyyar.
Bazoum ya fuskanci ƙalubale kafin amincewa da takararsa tsakanin jiga-jigan jam'iyyaryayin da wasu kusoshin jam'iyyar suka nemi ƙalubalantarsa.
Wasu na ganin nada ɗan shugaba Mohammadou Issoufou matsayin jagoran yaƙi neman zaben Bazoum mataki ne na kokarin hada kan sauran mambobin jam'iyyar.
Kamar yadda wasu ke alakanta nadin da wata hanyar yin watsi da jita-jitar cewa shugaba Mohammadou Issoufou yana marawa tsohon shugaban kasa na mulkin soja Salou Djibo baya











