Zaɓen Nijar na 2020: Me ya sa babu mace a takarar shugabancin ƙasar?

Aichatu Kane

Asalin hoton, Gov Maryama Facebook

Bayanan hoto, Aichatu Kane tsohuwar gwamna ce a Yamai

Bisa dogaro da takardun takara 41 da ofishin ministan cikin gidan Jamhuriyyar Nijar ya karɓa na neman takarar kujerar shugabacin ƙasar, za a iya cewa babu mace ko ɗaya a jerin masu neman takarar.

To sai dai ana sa ran a sauran kujerun da ba na shugaban ƙasa ba za a iya samun jerin mata a ciki.

Duk da cewa babu mata a jerin 'yan takarar amma abun da ake ganin ya sa ba a damu da rashin iyaye mata ba shi ne yadda matasa suka mamaye takarar a zaɓen Jamhuriyar ta Nijar na 2020.

Alƙaluma dai na nuna cewa kaso uku cikin huɗu na 'yan takarar duk matasa ne.

'Yan takara 41 ne za su kara ne a zagayen farko na zaben shugaban kasar da za a gudanar ranar 27 ga watan Disamba.

Wannan shi ne karo na farko a tarihin siyasa kasar da aka samu irin wannan adadi na masu zawarcin kujerar shugabancin Nijar.

A zaben da ya gabata, 'yan takara 16 ne suka fafata a zagayen farko na zaben shugaban kasar.

Shugaba Mahamadou Issoufou da ke ƙarshen wa'adin milkinsa ya nanata aniyarsa ta miƙa milki ga sabon shugaban da 'yan kasar za su zaɓa.

Abin da shi ma zai zamo a karo na farko da shugaban farar hula zai miƙa milki ga wani zaɓaɓɓen shugaban ƙasa farar hula.

Ga baki daya dai za a ce duka manyan 'yan siyasar kasar ta Nijar na daga cikin 'yan takarar 41 da ke neman kujerar da kuma takardunsu na takara suka isa ofishin ministan na cikin gida.

'Yan takarar sun hada da:

  • Bazoum Mohamed na jam'iya mai milki ta PNDS Tarraya
  • Hama Amadou na jam'iya Moden Fa Lumana
  • Mahamane Ousmane
  • Seyni Oumarou na MNSD Nasara
  • Ibrahim Yacouba na MPN Kishin Kasa
  • Albadé Abouba na MPR jamhuriya
  • Janar Salou Djibo na Dubara
  • Sheikh Boureima Daouda, limamin babban masallacin Juma'a na Yamai .
mace na kada kuri'a a Nijar

Asalin hoton, Getty Images

Kawo yanzu dai takara biyu ne ake ta ce-ce-ku-ce kansu, wato ta Bazoum Mohamed wanda masu hamayya ke ganin da wuya kotun mulki ta amince da takararsa bisa dogaro da wata doka a kundin tsarin milki da ke cewa mutum ba ya zama shugaban kasa sai dan kasar wanda aka haifa a Nijar tare da iyayensa duka biyu.

Su kuma masu mulki cewa suke kasancewar madugun adawar, Hama Amadou ya fuskanci hukuncin daurin shekara daya kotun tsarin milkin za ta yi watsai da takarar tasa.

Bayan ajiye takaradun takarar wanda ke zaman mataki na farko na shiga takarar mataki na biyu shi ne binciken kwakwaf da za a yi wa kowane dan takara .

Ayar doka mai lamba 134 ta kundin zaben ta ce: "Babu wanda ya cancanci shugabancin kasar sai wanda , ke cikin koshin lafiyar jiki da ta kwakwalwa, da kuma kyawawan halaye."

Bayan Ofishin ministan cikin gidan ya cika duk waɗannan ƙa'idodin, zai miƙa waɗannan takardun takarar 41 zuwa Kotun Tsarin Mulki wadda ke da makonni biyu don tantancewa.

Kowane ɗan takara dai zai biya kudin ajiya na CFA miliyan 25, a matsayin gudunmowarsu ta zaɓe.

Aichatu Kane Facebook

Asalin hoton, Aishatu Kane Facebook

Masu jefa ƙuri'a kimanin miliyan 7.4 ne aka yi wa rijista a kan rajistar zaɓe na zamani.

Yaƙin neman za be na zagayen farko na majalisar dokoki da na shugaban kasa zai fara a ranar 5 ga watan Disamba, kuma ya ƙare a ranar 25 ga Disambar 2020.

Yanzu dai za a iya cewa mata sai dai su kasance masu kaɗa ƙuri'a a Jamuriyar ta Nijar kasancewar duk wannan faɗi-tashi da za a yi babu su a ciki.

Kusan wannan abu ne ba sabo ba a jamhuriyar sakamakon tasirin al'ada da addini da suka mamaye mafi yawancin kasashen Afirka.

To sai dai ana sa ran matan za su nemi takarar a sauran matakan zabe da ba na shugabancin kasa ba.