An kama masu yunkurin juyin mulki a Ghana

Asalin hoton, Getty Images
Dakarun gwamnatin Ghana sun dakile wani yunkurin juyin mulki a fadar shugaban kasar.
Jami'an tsaron kasar sun tsare wasu mutum uku da wasu tulin makamai a wani samame na hadin gwiwa da aka yi ranar Juma'a, in ji ma'aikatar yada labaran kasar.
Ma'aikatar ta ce hukumomin tsaron sun gudanar da aikin ne bayan wata 15 ana tattara hujjoji da bin diddigin manyan wadanda ake zargi.
Sanarwar da ma'ikatar da fitar ta ce daya daga cikin mutanen da ake tsare da su din makerin makamai na cikin gida ne.
Masu yunkurin juyin mulkin sun shirya karbe ikon wasu muhimman wurare, da kuma samo kudin da za su yi amfani da su wurin kifar da gwamnatin kasar, a cewar sanarwar.
Gwamnatin kasar na zargin daya daga cikin mutanen da hada baki da wasu jami'an sojin kasar kan yadda za su yi juyin mulkin da inda za su samu makamai a tsakanain watan Yuni zuwa Agustan shekarar da ta gabata, in ji sanarwar.
Ghana na cikin kasashen Afirka ta yamma da ba a samun rikici wurin mika mulki tun da kasar ta fara amfani da tsarin jam'iyyu da yawa a 1992.
A watan Dismaban 2016 shugaba Nana Akufo-Addo ya lashe zaben kasar inda ya kayar da shugaban mai ci na wannan lokaci John Mahama wanda ya amince an kayar da shi.











