Yadda Ghana ta kayar da Najeriya a gasar shinkafa dafa-duka

Ghana

Asalin hoton, Ghana

Bayanan hoto, Madam Sika ta samu kyautar dalar Amurka 2000

A karon farko, kasar Ghana ta lashe gasar iya dafa shinkafa dafa-duka da aka gudanar tsakanin Najeriya da Ghanar a dandalin taro na Cressal Park da ke birni Accra.

Madam Sika ce dai ta lashe wannan gasa inda ta samu kyautar tsabar kudi har dalar Amurka 2000.

Shinkafa dafa-duka nau'in abinci ne mai farin jini a kasashen nahiyar Afrika da dama.

Akwai dadaddiyar hamayya ta raha tsakanin Najeriya da Ghana a kan wai wace kasa ce a cikinsu dafa-dukarta ta fi dadi, musamman a kafafen sada zumunta.

Wadanda suka shirya gasar dai sun ce sun yi ne domin kyautata alaka tsakanin kasashen biyu sannan suna fata gasar ta dore a nan gaba.

Ghana

Asalin hoton, Ghana

Bayanan hoto, 'Yar Najeriya ce ta zo ta biyu a gasar, inda ta samu kyautar dala 1000
Ghana

Asalin hoton, Ghana

Bayanan hoto, Madam Siki ke nan 'yar kasar Ghana wadda ta lashe gasar dafa-dukar
Ghana

Asalin hoton, Ghana

Bayanan hoto, An dai baje dafa-dukar domin alkalai sun dandana su ji
Ghana

Asalin hoton, Ghana

Bayanan hoto, Ana ganin dai wannan gasar za ta raba tsamar da ke tsakanin Najeriya da Ghana