Yadda Ghana ta kayar da Najeriya a gasar shinkafa dafa-duka

A karon farko, kasar Ghana ta lashe gasar iya dafa shinkafa dafa-duka da aka gudanar tsakanin Najeriya da Ghanar a dandalin taro na Cressal Park da ke birni Accra.

Madam Sika ce dai ta lashe wannan gasa inda ta samu kyautar tsabar kudi har dalar Amurka 2000.

Shinkafa dafa-duka nau'in abinci ne mai farin jini a kasashen nahiyar Afrika da dama.

Akwai dadaddiyar hamayya ta raha tsakanin Najeriya da Ghana a kan wai wace kasa ce a cikinsu dafa-dukarta ta fi dadi, musamman a kafafen sada zumunta.

Wadanda suka shirya gasar dai sun ce sun yi ne domin kyautata alaka tsakanin kasashen biyu sannan suna fata gasar ta dore a nan gaba.