Liverpool ta ci gaba da jan jarenta bayan tisa Arsenal 3-1

Lokacin da Salah ya ci Arsenal ta biyu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mohamed Sala ya fi taka rawa wajen cin Arsenal fiye da duk wata kungiya a Premier ( kwallo 8)

Kociyan Liverpool Jurgen Klopp ya ce ba lalle ba ne sai sun burge kowa da kowa a kowane lokaci, bayan da kungiyar ta lallasa Arsenal, ta ci gaba da rike matsayinta na daya a teburin Premier.

Kungiyar ta ci gaba da karsashin da ta fara gasar ta Premier ta bana da shi inda Mohamed Salah ya daga raga sau biyu kari a kan bal din da Joel Matip ya ci tun a kashin farko na wasan wanda Liverpool din ta mamaye a gidanta Anfield.

Ana shirin kare kashin farko na wasan ne a minti na 41 Matip ya ci Arsenal da ka, da wata bal wadda Trent Alexander-Arnold ya dauko kwana.

Fatan da bakin suke da shi na ganin sun farke bal din ya gamu da cikas minti hudu kacal da dawowa daga hutun rabin lokaci, sakamakon wata kasassaba da sabon dan wasan Arsenal din David Luiz ya yi, inda ya rike rigar Salah a da'irarsu, abin da ya sa ba wata-wata alkalin wasa ya ba Reds fanareti.

Bayan da dan wasan na Masar ya ci fanaretin, ya kuma sake kunyata tsohon dan bayan na Chelsea, Luiz, mai shekara 32, a minti na 58, inda ya kara daga ragar Gunners din, bayan da ya yi masa wani yanka ta can gefen dama na filin ya ja bal din har ya dangana ta da raga.

Arsenal ta samu ladan gabe a minti na 85, ta hannun Lucas Torreira wanda ta sako daga baya, amma hakan bai zama wata barazana ga nasara ta 12 a jere da Liverpool din ke samu ba a gasar ta Premier.

Daman Arsenal ta saba shan kashi a kusa-kusan nan a Anfiels, inda a kakar da ta wuce ta kwashi kashinta a hannu da ci 5-1, da kuma 4-0 a kaka ta karshe ta Arsene Wenger a kungiyar.

Liverpool ta ci gaba da zama ta daya a tebur da maki tara, da yawan kwallo shida a wasa uku, yayin da Arsenal din ke bi ma ta baya da maki shida ba kwallo ko daya.

Leicester na matsayi na uku bayan wasan na mako na uku inda take da maki biyar da kwallo daya kawai, sai Manchester City wadda take matsayi na hudu da maki hudu, da yawan kwallo biyar, amma a wasa biyu.

Wasu Alkaluma kan haduwar kungiyoyin biyu:

Tun bayan da Jurgen Klopp ya zama kociyan Liverpool a watan Oktoba na 2015, kungiyar ta zura kwallo 26 a ragar Arsenal a wasa takwas na Premier.

Liverpool ta ci bal 22 da ka a gasar Premier tun daga fara gasar kakar da ta wuce, inda ta wuce dukkanin kungiyoyin Premier da bal bakwai.

Kociyan Liverpool Jurgen Klopp

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Mun mamaye wasan, kuma daman haka ya dace ka yi idan za ka kara da kungiya kamar Arsenal - Klopp

Kociyan Liverpool Jurgen Kloop ya kara da Arsenal sau takwas ba tare da Gunners din sun doke shi ba a gasar Premier, inda ya yi galaba a kansu a wasa biyar, suka yi canjaras sau uku.

Mohamed Salah ya fi taka rawa wajen zura kwallo a ragar Arsenal fiye da a kan kowace kungiya a gasar ta Ingila, inda ya ci su shida ya kuma bayar aka ci biyu. Kuma ya daga ragarsu a dukkanin wasa hudu da suka kara a Anfield.

Wasannin Kungiyoyin na gaba:

Liverpool za ta je gidan Burnley a wasansu na Premier na gaba ranar Asabar 31 ga watan Agusta da karfe 5:30 na yamma agogon Najeriya.

Ita kuwa Arsenal za ta karbi bakuncin Tottenham ne a karawar hamayya ta arewacin Landan ta farko a bana, ranar Lahadi 1 ga watan Satumba da karfe 4:30 na yamma agogon Najeriya.

Sakamakon Sauran Wasannin na Premier na Asabar:

Norwich 2-3 Chelsea

Brighton 0-2 Southampton

Manchester United 1-2 Crystal Palace

Sheffield United 1-2 Leicester City

Watford 1-3 West Ham

Ci-gaban Wasannin Premier na mako na uku, ranar Lahadi:

AFC Bournemouth da Manchester City (karfe 2:00 na rana agogon Najeriya)

Tottenham Hotspur da Newcastle United (4:30 na yamma agogon Najeriya)

Wolverhampton da Burnley (4:30 na yamma agogon Najeriya)