Al-Shabab: Yadda tsoffin dakarun ƙungiyar da ke iƙirarin jihadi ke rayuwa bayan fitarsu daga cikinta

school bus with tank
    • Marubuci, Daga Mary Harper
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service, Mogadishu

Ƙungiyar al-Shabab mai iƙirarin jihadi na ɗaukar dubban dakaru sannan kuma tana buƙatar mutanenda za su yi aiki a wuraren da take mulki. Duk wanda aka kama yana ƙoƙarin guduwa kashe shi ake yi. Duk da haka, gwamnati na ƙarfafa wa waɗanda ke son tserewa gwiwa.

Ga uku daga cikinsu zaune tare da ni; Ibrahim mai shekara 35 da Moulid mai shekara 28 da kuma Ahmed mai 40.

Dukkaninsu ba sa ƙaunar abincin karin kumallo. "Ba abincin da muka saba da shi ba ne, kamar fanke ko wake. Ba ma shan ruwan roba. Mun fi son rayuwa mai sauƙi da ruwa mai sauƙi," in ji Ahmed.

Ibrahim ya ce: "Ba ma tsoron mu bayar da labarimmu, ki tambaye mu duk abin da kike so. Za ki iya ɗaukar hotunanmu kuma ki rubuta sunayenmu na gaskiya."

Sai dai na yanke shawarar ba zan ɗauki hotunansu ba kuma ba zan yi amfani da sunayensu na gaskiya ba. Saboda sun fita ne daga ƙungiyar da ta shafe fiye da shekara 10 tana saka tsauraran dokoki a Somalia.

Ƙungiyar ta kafa wata gwamnati mai ma'aikatau da 'yan sanda da tsarin shari'a. Tana kula da makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya, tana noman rani, tana gyara tituna da gadoji, kuma tana buƙatar mutanen da za su gudanar waɗannan ayyuka.

insurgents

Hukuncin wanda ya gudu shi ne kisa. Al-Shabab ta faɗa mani cewa ana yanke hukuncin ne ga duk wanda ya gudu ba tare da umarni ba.

"Ni fa saboda kuɗi na shiga Al-Shabab," in ji Ahmed, wanda ya fi sauran yin magana. "Sun biya ni dala 200 zuwa 300 a wata. Ni ne mai kula da harkokin sufuri a yankinmu."

Shi ma Ibrahim ya bi sahun Ahmed: "Ni ma saboda kuɗi na shiga har tsawon shekara uku. In kana ciki ba za ka so ka fita ba.

"Abin da kawai ban ji daɗinsa ba a Al-Shabab shi ne yadda suka yi ƙoƙarin sauya tunanina. Duk mako za su turo tawagar sauya tunani zuwa rundunarmu, su yi ta karanta Ƙur'ani da kuma nanata cewa gwamnati da ƙasashen duniya kafirai ne.

"Yadda ka san sun saka wani layin wayar salular Al-Shabab a ƙwaƙwalenmu."

putting sim card in brain

Mutanen uku sun ce duk da cewa zukatansu sun rufe a lokacin amma sun gano cerwa ƙungiyar ba jihadin gyara addinin Musulunci take yi ba, sai dai wani karkataccen tsari. Daga baya ma suka daina sha'awar kuɗin da ake biyan su.

Da farko dai sun fita daga ƙungiyar Al-Shabab, yanzu kuma suna son fita daga yankin da ƙungiyar ke iko da shi.

"Cikin dare, nakan yi tafiya har sai ƙafata ta gaji da sukar ƙayoyi," a cewar Ahmed. "Na yi sa'a wayata na tare da ni, sai na tuntuɓi 'yan uwana. Sun haɗa ni da wani da zan iya amincewa da shi. Na shafe kwanaki da yawa sannan kuma tsoro ya mamaye ni a duk taku ɗaya idan na yi. Ina ta tunanin za a kama ni a kashe ni a gaban al'umma, saboda haka Al-Shabab ke yi wa waɗanda suka tsere."

walking on thorns

Kazalika, akwai tsoron cewa idan jami'an tsaron Somalia suka kama 'yan Al-Shabab suna yi musu azaba da wutar lantarki.

Da yawa daga cikinsu ba su san cewa akwai shirin afuwa na gwamnatin Somalia, inda ake ba su ilimi sannan a mayar da su cikin al'umma.

An yi ta ƙoƙarin yaɗa wannan shirin a wuraren da Al-Shabab ke mulki. An tsara hotuna da zane-zane saboda waɗanda ba da ilimin karatu da rubuta su gane abin da ake faɗa da kuma lambar wayar da za su iya kira. Hakan ya sa an samu ƙarin masu barin ƙungiyar. Fiye da mutum 60 ne suka bar ƙungiyar a cikin wata biyu.

leaflet

Ibrahim ya shafe shekara uku a Al-Shabab, ya ce ba zai taba komaa ƙauyensu ba, zai yi ta ƙoƙarin sajewa da mazauna birnin Mogadishu.

Dukkanin mutum ukun tsinci kansu a sansanin gyara hali na Serendi da ke Mogadishu. An tsaurara tsaro sosai a inda suke domin kuwa sanda na je na tarar da jami'an tsaro 80 na gadin tubabbu 84.

Short presentational grey line

Amfanin sansanin Serendi shi ne sauya halin tubabbun 'yan Al-Shabab da zukatansu da ma tunaninsu sannan a koya musu yadda za su yi mu'amala da mutanen gari idan sun koma garuruwansu.

"Na tuƙa wata mota cike da makamai da muke kira 'Volvo', a lokacin da nake Al-Shabab ba na jin tsoron komai," in ji Moulid.

"Lokacin da na je Serendi, sauran mutane sun ga ƙwarewata a tuƙi. An ba ni muƙamin koya wa sauran tubabbun yadda tuƙin mota. Yanzu ni direban motar 'yan makaranta ne. Ina fatan wata rana na kafa nawa kamfanin na koyar da tuƙi."

Shi kuwa Ahmed, yanzu yana samun kuɗi ne ta hanyar dillancin fili.

Ibrahim ma ya bayyana yadda ya koyi sana'ar aski a Serendi kuma babu daɗewa ya fara samun kuɗi da yi wa sauran tubabbu aski da ma masu gadinsu.

Yanzu yana da shagon aski a Mogadishu, har ma ya ɗauki mutum uku aiki. "Ina samun kuɗin da zan iya ciyar da matana biyu da 'ya'ya takwas," in ji shi, yana mai cewa ya dawo da su birni domin su zauna tare da shi.

barber shop

Moulid ya ce wasu daga cikin 'yan uwansa ba su yarda da shi ba, sun tsangwame shi.

Ibrahim ya ce ba zai koma garinsu ba ko da kuwa ba za su tsangwame shi ba ko kashe shi. Duk da cewa danginsa sun yafe masa, maƙwabtansa ba su yafe ba.

Ya ce har yanzu yana jin haushin zamansa a Al-Shabab - abin na hana shi barci.

"Ina ta faman ƙoƙarin cire layin wayar Al-Shabab daga ƙwaƙwalwata; hotunan abubuwan rashin kyautawa da na yi da kuma waɗanda aka yi mani," a cewarsa.

Short presentational grey line

A cikin Serendi kuma, dandazon tubabbu ne ya cika azuzuwa domin ɗaukar darussan Turanci da lissafi da sauransu. Wasu kuma na koyon kanikanci da tuƙi da sauran sana'o'i.

Defectors learn how to fix cars

Wasu daga cikin tubabbun na shan kiɗa da rawa da waƙa - abin da Al-Shabab ta haramta kwata-kwata.

Wani kocin ƙwallon ƙafa kan zo Serendi, inda yake haɗa kan tubabbun da masu gadi su yi wasa tare da a wani fili mai kyawun gaske.

Malaman addini kan shigo domin tallafawa wurin sauya tunanin tubabbun daga tsaurin addini, su faɗakar da su cewa akwai wani Musuluncin ba iirn wanda Al-Shabab ta koya musu ba.

Reading the Koran