Al-Shabab: Harin bam ya kashe mutum 14 a barikin sojan Somalia

Asalin hoton, Reuters
Wani hari da aka kai kan sansanin sojoji a Mogadishu, babban birnin Somalia ya yi ajalin aƙalla mutum takwas tare da jikkata wasu 14.
Waɗanda suka shaida lamarin sun shaida wa kafafen yaɗa labarai a ƙasar cewa wata mota ce da aka cika ta bamabamai ta tashi ginin, wanda ke kusa da filin wasan ƙwallon ƙafa.
An jiyo ƙarar fashewar mai ƙarfin gaske a ɗaukacin birnin.
Ƙungiyar masu ikirarin jihadi ta al-Shabab ta ce ita ta kai harin. Ta sha kai harin bam, inda take harar jami'an tsaro da manyan jami'an gwamnati.
Kanar Ahmed Muse ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa fashewar ta faru ne a mashigar barikin soja na 12th April, wanda ke kusa da wani sabon filin ƙwallo da aka buɗe a unguwar Warta-Nabadda.
A watan Yunin da ya gabata aka buɗe filin wasan, wanda ake yi wa kallon wata hanya ce ta farfaɗowar da birnin ya yi bayan kasancewa a cikin rikici na tsawon shekaru.
Halima Abdisalan, wata uwa da ke zaune a kusa da inda lamarin ya faru, ta faɗa wa Reuters cewa sojoji sun buɗe wuta jim kaɗan bayan fashwar. "Mun shige cikin gida cikin firgici," in ji ta.






