Coronavirus: 'Masu zuwa masallacina 60 na yi wa jana'iza a cikin wata ɗaya'

BBC Africa Eye

Asalin hoton, BBC Africa Eye

Cutar korona a yanzu na iya zama ɗaya daga cikin manyan sabubban mutuwa a ƙasar Somaliya, wadda ta yi fama da rikice-rikice tsawon shekaru gommai.

Alƙaluman hukuma sun ce ƙasa da mutum 100 ne suka mutu sanadin cutar korona. Sai dai shaidun da Sashen Binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya tattara sun nuna haƙiiƙanin adadin ya yi matuƙar fin haka,

A ziyarar da Jamal Osman ya kai ya gano cewa a fuska dai, sashen kula da majinyatan da jikinsu ya yi tsanani guda ɗaya ƙwal a Somaliya, da ke karɓar masu cutar korona, sambarka.

Akwai shuɗin labulaye mas haske sun kewaye gadaje, an yi sabon fenti a bangon ɗakin, kayan aikin idan ka gansu na zamani ne, ga ma'aikata dukkansu sanye da tufafin kare lafiya.

Sai dai sashen na da gado 20 ne kacal ga al'umma miliyan 16. Yana cikin asibitin Martini, a birin Mogadishu. Wasu ma'aikatan lafiya sun ce hatsarin aikin ya fi ƙarfinsu. Wasu kuma sun yi imani nauyi ne a kansu su tsaya.

Ɗaya daga cikinsu, Dr. Hilwa, Daud Ibrahim wata matashiyar uwa. A ƙarshen watan Afrilu, mutum 32 ne suka mutu a asibiti, wasunsu saboda ƙarancin kayan aiki.

Dr Hilwa ta ce Marasa lafiya da dama na mutuwa ne saboda rashin iskar oksijin (oxygen).

Jamal ya kuma ga lokacin da aka shigo da wani matashi cikin wannan sashe.

Tuni likitoci sun yi rashin marasa lafiya biyu da safe don haka yanzu suka tashi ba-ji-ba-gani kada wani ya sake mutuwa.

BBC Africa Eye

Asalin hoton, BBC Africa Eye

Bayanan hoto, Dr Hilwa da waɗansu ma'aikatan lafiya ƙalilan ne suka tsaya tsayin daka wajen yaƙi da cutar korona a Somaliya

Daga cikin takunkumi wata abokiyar aiki ta kokawa Dr. Hilwa game da rashin kayan aiki. "Wannan abin kunya ne. Ba ma samun horo".

Ma'aikaciyar wadda ba ta so a ambaci sunanta ba ta ce ɗaya daga cikin marasa lafiyan da ke kwance ba a sa masa na'urar taya numfashi ba, kawai an zura masa waɗansu abubuwa, ana yi masa ci da ƙarfi

Ba tare da ingantacciyar na'ura taya numfashi ba, likitocin sun gaza kuɓutar da rayuwarsa. Shekararsa 34 kuma ya bar 'ya'ya har 11.

Dr. Hilwa dai ta bayyana tababa kan alƙaluman yawan mutanen da suka mutu na hukuma, ta ce tana jin ainihin yawan mamatan ya zarce 100 matuƙa gaya. A cewarta, mutane da dama na ƙin zuwa asibitin Martini.

"Mutane sun ɗauka cewa asibitin wata lahira kusa ce, ko kuma wani gidan yari da ba a fita. Sukan ce kada ku kai ni Martini. Kada ku kai ni wannan asibitin. Na gwammace mutuwa a gidana da a kai ni wannan wuri," ma'aikaciyar lafiyar ta ruwaito.

BBC Africa Eye

Asalin hoton, BBC Africa Eye

Duk da wannan annoba, masallatai a Somaliya sun ci gaba da kasancewa a buɗe. Masu ibada da dama sun yi imani Allah ne garkuwarsu.

A tsawon abin da bai fi wata ɗaya ba, wani limami ya faɗa mana cewa ya jagoranci jana'izar mutum 60 da ke zuwa masallacinsa ibada.

Ya ce a kwanakin goman farko na watan Ramadan, da kuma rabin kwanakin watan jiya, sun yi wa mamata da dama jana'iza. Kuma a gaskiya suna da yawa.

Akasarin mutane ba sa son zuwa asibiti(n Martini) saboda tsegunguma masu yawa da ake yaɗawa. Kuma mutane sun yi imani da wasu abubuwa don haka ba sa zuwa asibiti, in ji limamin.

A lokaci guda kuma maƙabartu na cika cikin sauri. Sashen binciken ƙwaƙwaf na Africa Eye ya kai ziyara ɗaya daga cikin manyan maƙabartun birnin Mogadishu, mai suna Barakat.

BBC Africa Eye

Asalin hoton, BBC Africa Eye

Tun a watan Janairu, aka buɗe wani sabon ɓangare makeke, yana ƙunshe da sabbin kaburburan da aka haƙa layi-layi.

Akwai wahala haƙa kabari a wannan ɓangare. Ka ga wannan sashe? Taɓo ne. A kullum muna haƙa kaburbura, cewar Adan, ɗaya daga cikin masu aikin haƙar kabari.

Ya ce suna haƙa kaburbura fiye da yadda aka saba a baya. "Muna nan sama da wata huɗu ke nan yanzu, yawan mace-macen da aka samu ya zarce dubu biyu".

Gawawwaki na ci gaba da shigowa, mafi yawa ba daga asibitin Martini ba ne, mutane na ci gaba da harkokinsu kamar zuwa sallah ba tare da ba da tazara ba.

Kuma mutanen da cutar ke yin ajalinsu ba su taƙita kawai ga babban birni Mogadishu ba. Akwai ma labarin mace-mace da yawa a sauran yankunan Somaliya su ma.

Abin takaici, yaƙin gomman shekaru, ya sa mutuwar yawa ta zama ga Somaliyawa. Sai dai a wannan karo, makashin kisan mummuƙe yake.

Karin labarai da za ku so ku karanta: