Tsaro a Najeriya: Ko Buhari zai iya garambawul ba tare da sauya manyan hafsoshi ba?

Asalin hoton, Buhari Sallau
A makon nan ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umurnin a yi garambawul ga baki daya tsarin tsaro a ƙasar. Sai dai da dama daga cikin 'yan ƙasar na saka ayar tambaya kan me shugaban ƙasar ke nufi da garambawul da kuma manufarsa a wannan karon.
Wasu na ganin cewa ta ya za a yi garambawul da manyan hafsoshin tsaron Najeriya da suka shafe sama da shekaru biyar kan muƙamansu ba su sauka ba? Ko a kwanakin baya sai da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma 'yan majalisar tarayyar ƙasar suka nemi shugaban ya sauke manyan hafsoshin tsaron ƙasar.
A wannan dalili ne ya sa 'yan Najeriya da dama suka kasance cikin duhu da kuma laluben bayanai kan me wannan garambawul ɗin ke nufi a halin yanzu da kuma ko ƙasar na buƙatarsa a halin yanzu?
BBC ta tattauna da Group Captain Sadik Garba Shehu mai ritaya, wanda mai sharhi ne a kan harkokin tsaro a Najeriya:
Me Buhari ke nufi da garambawul
'Yan ƙasar da dama na cikin duhu kan ta sigar da za a ɓullo wa garambawul din da Shugaba Buhari ya bayar da umarnin a yi wa shugabannin tsaro a ƙasar, sai dai Group Captain Sadik, cewa ya yi:
Abin da ake nufi da garambawul a harkar tsaro, wata manufa ce da ake so a duba sha'anin tsaro na ƙasa gaba ɗaya a ga ya wannan abu yake aiki? nawa ne ake kashewa a kai? kuɗin da ake kashewa ya yi daidai da tattalin arziƙin ƙasar.
A cewarsa, za kuma a duba yanayin irin kayayyakin aikin da jami'an tsaro ke da su a ƙasa.
Ya ce akwai zargin rashin haɗin kai tsakanin sojan sama da na ƙasa, "akwai yiwuwar za a duba wannan", in ji shi. Ya kuma ce akwai kuma batun ƙarfin ministan tsaro da majalisa kan tsaro da sojoji wanda shi ma abin da za a duba ne.
Ya kuma ce garambawul ɗin ba sojoji kaɗai zai shafa ba, har da 'yan sanda da kuma wasu ma'aikatu da ke da ruwa da tsaki kan sha'anin tsaro.

Asalin hoton, NTA
Shin wannan ne abin da Najeria ke bukata a yanzu?
Duk da cewa 'yan ƙasar na cikin duhu kan ko wannan garambawul ɗin zai yiwu ko kuma shin ƙasar na buƙatarsa a halin yanzu? Group Captain Sadik cewa ya yi, ya kamata a ce tun tuni an yi wannan garambawul ɗin.
A cewarsa, "yanzu ga yaƙi ana yi, ga kuma garambawul ana so a yi, gaskiya hakan ya sa garambawul ɗin zai yi wuya, amma kuma abu ne wanda ya kamata a ce tun kafin wannan tarnaƙin ya zo an yi".
Ya ce an yi jinkiri wurin yin wannan garambawul ɗin, amma duk da haka dole a yi.
Group Captain Sadik ya ce "Amma abu ne mai kyau idan za a yi shi ɗin, saboda akwai abubuwa da yawa da babu su a maganar yadda za a duba aikin soja da aikin 'yan sanda da aikin tsaro gaba ɗaya".
Ko wannan garambawul zai yiwu idan hafsoshin tsaro na kan muƙamansu?
Tun kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga wa'adinsa na biyu na shugabancin ƙasar a 2019 ake ta kiraye-kiraye kan sauya manyan hafsoshin tsaron ƙasar sakamakon gazawar da ake zargin sun yi a daƙile matsalar tsaro a ƙasar.
Wannan na daga cikin dalilan da ya sa wasu 'yan ƙasar ke ganin buƙatar da shugaban ya yi na yin garambawul ɗin tamkar neman yin wani sabon damu ne a tsohuwar ƙwarya.
Group Captain Sadik ya ce ba ya tunanin cewa ci gaba da zaman manyan hafsoshin sojin kan muƙamin su zai kawo cikas ko kuma wata matsala ga yin wannan garambawul ɗin.
A cewarsa, shugaban ƙasa ke da wuƙa da nama a hannunsa, idan yana so a yi wannan garambawul ɗin ko hafsoshin suna kan muƙaminsu hakan zai yiwu.
Ya ce "soja a dimokradiyya, gaskiya a ce mashi ya je ya yi ne kawai, ko waɗannan mutane suna nan, ko ba su nan za a yi, su an ɗauke su aiki ne.
"Idan shugaban ƙasa da ministan tsaro da ma'aikatar 'yan sanda suka ce ana so a yi wannan garambawul ɗin, a gaskiya zamansu ko rashin zamansu ba zai hana a yi wannan aikin ba."











