Sojoji sun 'kashe' wani babban kwamandan al-Shabab

.

Asalin hoton, AFP

Wani harin sama da sojoji suka kai ya kashe wani babban kwamandan kungiyar al-Shabab a Somaliya.

Tun a 2008 Amurka ta saka tukwicin dala miliyan biyar ga duk wanda ya yi hanya aka gano Bashir Mohamed Qorgab.

Amurka na yawan kai hare-hare ta sama kan masu tayar da kayar baya a Somaliya. Iyalan Qorgab sun tabbatar da mutuwarsa.

Shi ne ya jagoranci kai hare-hare a wasu sansanonin soji kuma ya jagoranci kai wasu hare-hare a Kenya kamar yadda rahotanni suka bayyana.

An kashe Qorgab a ranar 22 ga watan Fabrairu a kauyen Sakow da ke kudancin Somaliya yayin wani samamen hadin gwiwa da sojojin Somaliya da na Amurka suka kai.

Sai dai ba a san dalilin da ya sa ake bada rahoton mutuwarsa a yanzu ba bayan makwanni.

A watan da ya gabata, wasu rahotannin da ba a tabbatar ba sun bayyana cewa Qogab ya fice daga al-Shabab bayan rashin jituwar da suka samu da wasu shugabannin kungiyar.

Kungiyar al-Shabab na da alaka da al-Qaeda kuma tana da iko da garuruwa da dama da ke kudanci da kuma tsakiyar Somaliya.

Kungiyar kuma ta kai hare-hare da dama a Kenya da ke makwabtaka da Somaliya.