Zaben Amurka na 2020: Ta yaya Biden zai sauya hulɗar ƙasar da ƙasashen waje?

Democratic presidential nominee Joe Biden delivers remarks in the parking lot of the United Food and Commercial Workers International Union Local 951

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Barbara Plett Usher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC State Department Correspondent

A wajen Shugaba Trump duniya ba ta wuce kishin Amurka ba, shi ya sa ya yi watsi da yarjeniyoyin kasa da kasa da aka cimma, da ba su yi wa Amurka dadi ba.

Abu ne na kulla hulda, da zai iya janyo ce-ce-ku-ce da kuma bai wa Amurka dama ita kadai. A wajen Trump komai na Amurka ne wanda hakan abu ne da ba a saba gani ba, wanda kawai yake tafiyar da shi da son zuciyarsa da kuma alakarsa da shugabannin duniya, kuma yake wallafa shi a Twitter da ya ga dama.

Amma a wurin Joe Biden duniyar ta fi karfi kan rawar da Amurka ke takawa da kuma muradunta, wadanda aka cimma da cibiyoyin duniya bayan yakin duniya na biyu. Kuma ya mayar da hankali kan manufofin dimokradiyyar kasashen yamma.

Daya daga cikin kawancen duniya da Amurka ke jagoranta, domin tabbatar da 'yancin kasashe da kuma kubuta daga barazana.

Wanne irin sauyi za a samu karkashin shugabancin Biden? Abubuwa kadan za mu iya hasashen - sauyin alaka da kawayen Amurka, sai maganar sauyin yanayi, da kuma rikicin gabas ta tsakiya.

Alaka tsakanin Amurka da ƙawayenta

Trump ya yi ta goyon bayan 'yan kama karya da kuma haɗa hannu da su. Cikin manyan manufofin Joe Biden akwai sake sabunta alaƙa, musamman kungiyar tsaro ta Nato, da kuma sauran kasashen duniya.

Gwamnatin Biden za ta sabunta alakarta da Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma jan ragamar yaki da annobar korona a duniya.

Babban ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke New York, an dauki hoton a ranar 22 ga watan Satumba 2019.

Asalin hoton, VIEW press

Bayanan hoto, Ana sa ran Biden zai nemi hukumomin duniya domin ci gaba da aiki da su.

Tawagar Biden ta sanya wadannan abubuwa a gabanta domin ceto Amurka daga mummunan tabon da ta samu, tare da ci gaba da wayar da kai game da dimokradiyya kan abin da tawagar ta kira farfadowar mulkin kama-karya a duniya.

Amma yin hakan wani salo ne na mulki ba wai domin a burge mutane ba, Danielle Pletka ta cibiyar kasuwanci Amurka ta soki wannan mataki. Wadda ta ce gwamnatin Trump ta cimma abubuwa da dama a matakin duniya, kuma da kyakkyawan salo.

"Mun rasa abokan da za mu yi farin ciki da su ne? ina tambaya," in ji Pletka. "Babu wanda ke son zuwa casu da Trump. Shin mun rasa iko ne a ma'aunin shugabanci na akalla shekara 70? A'a."

Sauyin yanayi

Da yake bayani, Joe Biden ya ce zai mayar da yaƙi da sauyin yanayi babban abin da ya sanya a gaba, tare da sake komawa yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, wadda tana cikin manyan yarjeniyoyin da aka cimma na duniya wadda Trump ya yi watsi da ita.

Wannan hoton na wata tattaunawa ce ta musamman da aka yi da shugaba Trump da jaridar Bild ta Jamus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Trump ya yi amfani da tsarin kama karya a matsakin duniya

Mutanen biyu sun yi hannun riga da juna. Mista Trump na ganin yaki da sauyin yanayi wata barazana ce ga tattalin arziki.

Mista Biden na da shirin ware dala tiriliyan biyu domin daƙile hayakin masana'antu. Ya ce zai yi wannan domin gina tsaftataccen tattalin arziki ta hanyar amfani da makamashi. Zai kirkiri miliyoyin ayyuka.

Iran

Joe ya ce yana kokarin sake komawa wata yarjejeniya ta kasa da kasa da Trump ya yi watsi da ita - wata yarjejeniya da ta sassauta takunkumin da aka sanya wa Iran domin ta dakatar da shirinta na kera makamai.

Yarjejeniyar da Trump ya fice daga cikinta a 2018, yana cewa yarjejeniyar dakatar da kera makaman ta yi sauki da yawa idan aka yi la'akari da barzanar da Iran ke da ita, kuma ta yi rauni da aka iyakance ta kan lamarin nukiliya, ga shi za ta kare zuwa wani dan lokaci.

Ta yi ta sake sanya takunkumi tare da ci baga da matsin lamba kan tattalin arzikin kasar Iran, a baya-bayan nan kuma ta yi ta sukar kusan duka cibiyoyin hada-hadar kudi na Iran. Kan haka ita kuma Iran ta watsar da wasu takunkuman da aka sanya mata na kera nukiliya.

Biden ya ce wannan "matsin lambar" bai yi ba, domin kuwa ba bu a bin da ya haifar sai karin zaman dar-dar, wanda kuma kawayen Amurka suka yi watsi da shi, kuma hakan ya sanya Iran ƙara samar da nukiliya yayin mulkin Trump.

Ya ce zai sake komawa yarjejeniyar da Iran - amma ba zai janye takunkumin ba har sai lokacin, wanda haka zai ba yu zuwa ga yagga suka kulla yarjejeniya.

Yemen

Mista Biden kuma zai kawo ƙarshen goyon bayan da Amurka ke yi wa gamayyar sojin da Saudiyya ke jagoranta da ke yaki a Yemen. Mutuwar fararen hula da aka rika samu ta janyo nuna adadwa da Amurka da kuma shigarta cikin yakin, daga kasashen gefe da ba su da ruwa cikin yakin.

Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman ya na gaisawa da shugaban Amurka Donald Trump a taron G20 a Osaka da ke Japan

Asalin hoton, Reuters handout

Bayanan hoto, Saudiyya da Amurka kawaye ne na kud-da-kud

Saudiyya kawar shugaba Trump ce, ku,ma masu adawa da Iran da kawayenta. Masu sharhi na ganin Biden zai fice daga cikin wannan alaka da Trump ya kulla.

"Ina tunani game da gabas ta tsakiya, za a samu wani sauyi," in ji Misis Pletka," wadda ta fi karkata ga manufofin Iran sama da Saudiyya."

Rikicin kasashen larabawa da Isra'ila

Biden ya yi maraba da sabunta alaka tsakanin Isra'ila da Hadaddiyar Daular Larabawa. Kamar Trump shi ma na da ra'ayin kare Isra'ila tun da jimawa - kuma ba a sanya matsalar mamayar da Isra'ila ke yi wa muhallan Falasdinawa ba cikin sabbin manufofin kasashen waje da Amurka.

Da yiwuwar ya tafi da tsarin Trump kan matsalar mamayr da Isra'ila ke yi a yankin Yamma da Gabar Kogin Jordan. Ciki kuma har da cewa mazaunan da Isra'ila suke da su ba su sabawa dokokin kasa da kasa ba.

Sai dai masu burin kawo sauyi a jam'iyyar Democrat na fatan ganin an kawo gagarumin sauyi kan 'yancin Falasdinawa.

Ganuwar gabar yamma da kogin jordan da ke tsakanin Isra'ila da Falasdinawa a Bethlehem. Ranar Talata 13 Maris 2018.

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images

Bayanan hoto, Joe Biden mai kare Isra'ila ne tun da daɗewa, da alamun kara zurfafawa kan tsarin da Trump ya yi game da yakin Yamma da Gabar Kogin Jordan

"Ina ganin muna da manufofi masu kyau kan 'yancin Falasdinawa, in ji Matt Duss, mai ba da shawara na musamman ga Biden kan al'amuran kasashen waje. " Amma yahudawan da suke 'yan asalin Amurka da ke yankin suke da matukar mahimmanci a wannan tafiyar."

To wannan ne babban abin duba.

Menene ba zai sauya ba?

Kamar shugaba Trump shi ma Biden na fatan ganin ƙarshen yakin Afghanistan da Iraƙi, duk da cewa dai zai bar wasu tsirarin sojojin Amurka a yankin domin taimaka wa yaki da 'yan ta'adda. babu kuma tabbacin ko zai taba kasafin kudin ma'aikatar tsaro ta kasar ko kuma dakatar da hare-haren saman da jirage marasa matuka, duk da cewa ana fuskantar matsin lamba daga masu adawa da hakan.

In kuma ana maganar fadada manufofin siyasa a yankuna, wata kila ba za a samu wani banbanci ba kamar yadda ake zato.

Rasha

Alaka dole za ta sauya. Shugaba Trump a kashin kansa na da ra'ayin yi wa Vladmir Putin ahuwa game da karya ka'idojin kasa da kasa.

Sai dai gwamnatin Trump na yi wa Rasha kallon hadarin kaji, tare da kara sanya mata takunkumi. Da kuma alamun Trump zai ci gama da tafiya akan hakan, ba tare da ya cakuɗa al'amura ba.

Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin yayin wani taro ta bidiyo

Asalin hoton, TASS via Getty Images

Bayanan hoto, Za a iya samun sauyi game da alakar Amurka da sauran kasashen duniya ciki kuwa har da Rasha.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce, ya yi amannar Rasha abokiyar hamayya ce. Ya kuma yi alkawarin yin amfani da karfi wajen gano bahasin tsoma baki da ta yi kan harkokin zaben Amurka, da kuma zargin da ake mata na bai wa mayakan Taliban kudi domin kai hari kan dakarun Amurka a Afghanistan, wasu abubuwa da Trump ya ki mayar da hankali kansu.

China

A 2017, Mista Trump ya bayyana shugaba Xi Jinping a matsayin wanda tayar da jijyar wuya kan alawa. Tun bayan nan kuma alakarsu sai ta yi tsami da China yana mai zargin ta kan annobar korona da matakan da China ta dauka, hakan ya haifar cacar baka tsakaninsu.

Mista Biden zai ci gaba kan manufofin Trump game da Tattalin arzikin China, amma tare da kawayen Amurka, dan kaucewa zargin da aka yi wa Trump na shiga yarjejeniya shi daya a baya.

Kiran da Trump ya yi na a kauracewa sayan kayayyakin sadarwar China ya samu karbuwa a duniya. Wannan wani bangare ne na kokarin Amurka na ganin ta mayar da China baya.