'Yan mata 3 aka yi wa fyade, da wadda ɗan sanda ya kashe a makon nan

    • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist

Masu bibiyarmu barkanmu da wannan lokaci, kamar yadda muka saba, mukan yi waiwaye kan muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya duk ƙarshen mako.

Wannan karon ma mun tsakuro muku wasu muhimman batutuwa da suka faru a makon jiya, ciki kuwa har da batun wasu 'yan mata uku da aka yi wa fyaɗe, da wata kuma da ɗan sanda ya kashe.

Bayan nan kuma akwai wasu muhimman labaran da za mu yi bitar su.

'Yan mata uku da aka yi wa fyade

TA FARKO

.

Asalin hoton, UWAVERA OMOZUWA/FACEBOOK

Lamarin farko dai, wata ɗalibar jami'a ce a jihar Edo wadda ta rasu bayan an yi mata fyade a wata coci da ke kusa da jami'ar Benin a jihar Edo kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Batun yi wa Uwavera mai shekaru 22 fyaɗe ya ja hankali musamman a kafofin sada zumunta inda aka ƙirƙiri maudu'in #JusticeForUwa wato tabbatar da adalci ga Uwa.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu gawar Uwavera cikin cocin Redeemed yashe a ƙasa kuma jina-jina.

An dai ce an rotsa kan Uwavera ne da tukunyar sinadarin kashe wuta bayan an yi mata fyade.

Ƴar uwar marigayiyar, Judith Omozuwa ta shaida wa BBC cewa sai bayan kwana uku ne ta cika a asibiti.

TA BIYU

..

Asalin hoton, AFP

Lamari na biyu dai ya faru ne a Jigawa inda wata yarinya mai shekara 12 ta tabbatar wa 'yan sanda a jihar cewa mutum 12 sun shafe tsawon wata biyu suna yi mata fyaɗe.

Rundunar 'yan sandan jihar ta shaida wa BBC cewa ta samu ƙorafin cewa wani mutum mai shekara 57 ya yi ta yaudarar yarinyar a wani keɓantaccen wuri don ya yi lalata da ita.

A yayin wata hira da 'yan sanda, yarinyar ta ce baya ga wannan mutumin, wasu mazan 11 sun shafe wata biyu suna yi mata fyade.

Tuni rundunar 'yan sanda ta kama dukkan mutanen da ake zargi.

Wani mai magana da yawun 'yan sandan jihar ya faɗa wa BBC cewa an kai yarinyar asibiti kuma binciken likitoci ya tabbatar cewa an yi mata fyade. Amma ana ci gaba da bincike.

TA UKU

Na uku ma batu ne mai kama da irin na yarinya ta biyu inda aka kashe wata matashiya 'yar shekara 18 mai suna Barakat Bello.

An kashe ta ne ranar Talata a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Barakat, ɗaliba ce a kwalejin nazarin lafiyar dabbobi kuma ta koma hutu gida sakamakon dokar kulle da aka saka saboda annobar korona.

A ranar Talata, an bar ta a gida ita kaɗai, amma ko da ƙaninta ya koma, sai ya gan ta kwance cikin jini kusa da bandaki.

Bincike ya nuna cewa an yi mata fyaɗe sannan kuma aka kashe ta.

Yarinyar da dan sanda ya kashe

.

Asalin hoton, OWOROTV

A wannan makon ne dai iyayen wata yarinya mai shekara 17 suka fito suna neman a gurfanar da wani ɗan sanda wanda ya kashe musu 'ya mai suna Tina Ezekwe a jihar Legas.

Ɗan sandan dai ya kashe Tina ne a ranar 28 ga watan Mayu yayin da yake ƙoƙarin kama wani direba da ya karya dokar kulle, lamarin da ya kai ga harbe marigayiyar.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce ta gano ɗan sandan da ya yi kisan kuma tuni suka kama shi.

Ɗan sandan ya yi iƙirarin cewa ya yi harbin ne saboda yana cikin maye.

An sassauta dokar kulle a Najeriya

.

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

A ranar Litinin ne gwamnatin Najeriya ta sassauta dokar kulle a ƙasar inda ta sanar da sabbin matakai da aka kafa domin daƙile yaduwar cutar korona.

Daga cikin sabbin matakan da kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da annobar korona a Najeriya ya sanar akwai ɗage haramcin tarukan ibadah a masallatai da coci coci.

Sannan an sassauta dokar kulle ta mako huɗu da shugaba Buhari ya saka a jihar Kano da zummar daƙile yaɗuwar cutar korona.

Amma dokar hana tafiye-tafiye tsakanin jihohi na nan za ta ci gaba da aiki, sai dai dokar ba ta shafi sufurin kayan abinci da man fetur da sauran muhimman kayan bukatun rayuwa ba.

'Yan bindiga sun kashe fiye da mutum 70 a Zamfara'

Bayanan sauti'Ƴan bindiga sun kashe fiye da mutum 70 a Zamfara'

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren tattaunawa da wani mazaunin ƙauyukan

A wannan makon ne kuma muka samu rahotanni cewa wasu 'yan bindiga sun kashe fiye da mutum 70 a wasu hare-hare da suka kai kan wasu kauyuka ranekun Talata da Laraba a jihar Zamfara.

Ganau sun bayyana cewa 'yan bindigar sun fara auka wa mutanen kauyukan ne a ranar Talata inda suka kashe mutum 15.

Haka zalika 'yan bindigar sun sake far wa mutanen yayin da ake jana'izar waɗanda aka kashe sa'annan 'yan bindigar suka kashe mutum 50.

BBC ta tatattauna da kwamishinan tsaro na jihar Zamfara Abubakar Muhammad Dauran inda ya tabbatar da kashe mutum 21 a halin yanzu, sai dai ya ce ana nan ana bincike kan asalin yawan mutanen da aka kashe.

Ya kuma bayyana cewa akasarin ɓarayin da suka kai harin sun gangaro ne daga jihar Katsina sakamakon fatattakarsu da ake yi kamar yadda suka samu rahoto.