Amsoshin tambayoyinku kan labaran bogi kan coronavirus

Lokacin karatu: Minti 11

Idan har kana shiga shafukan sada zumunta, lallai ka yi kicibus da daya daga cikin wadannan labaran:

"Tsuntsaye na dawafi a Ka'aba saboda an hana mutane yi dalilin coronavirus; Idan kuka dage da shan ruwan zafi ko shayi mai zafi coronavirus ba za ta iya kama ku ba; makiya addinin Musulunci ne suka kirkiri cutar don su hana Musulmai ibadah; Shan ruwan dumi na hana kamuwa da coronavirus…"

Kadan kenan daga cikin irin labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta da muhawara a duniya bayan barkewar daya daga cikin annoba mafi girma a tarihin duniya.

Sai dai duk da hankali ya karkata wajen shawo kan annobar, wani abu da ke kawo cikas ga jami'an lafiya da sauran hukumomi shi ne yadda labaran karya ko na bogi ke daukewa mutane hankali daga abin da ya kamata- wato sahihan hanyoyin kare kansu daga kamuwa da cutar da kuma hanyoyin kula da kansu a lokacin da su ko wani nasu ya kamu.

BBC ta hada kai da likitoci da malaman addini da sauran masana wajen bambance aya da tsakuwa, cikin wadannan labarai da ke yawo a shafukan intanet a sigar makala ko bidiyo ko hoto.

Haka kuma, mun amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana don sanin sahihanci wasu labaran da kuka ci karo da su a shafukan sada zumunta.

Ga wasu daga cikinsu:

Wai da gaske ne tsuntsaye na dawafi bayan da aka hana mutane yin dawafi a Ka'aba?

Jim kadan bayan da hukumomin Saudiyya suka sanar da hana yin dawafi a daf da dakin Ka'aba saboda bullar coronavirus a kasar, wani hoton bidiyo ya bayyana, wanda ke nuna wani gungun tsuntsaye yana kewaye ka'aba da daddare.

Babu mutane da yawa a harabar masallacin a lokacin da aka dauki bidiyon, kuma an kange dakin Ka'abar da wani shinge don hana mutane zuwa kusa da ita.

An jiyo mai daukar bidiyon yana magana da wani yare mai kama da harshen Hindi kuma jefi-jefi ya kan ce 'Subhanallah, Allahu Akbar, Masha Allah'.

Binciken da BBC ta yi ya nuna cewa ba sabon abu ba ne yadda aka ga wadannan tsuntsaye na kewaye Ka'aba.

Wani fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya Ibrahim Disina ya ce wadannan tsuntsaye ba lallai dawafi suke don mutane sun daina dawafi ba. Idan ka kalli bidiyon za ka ga suna tashi har zuwa nan da can ne.

''Wanda duk ya san wannan wajen ya san tsuntsaye na yawan yin hakan a ciki da wajen masallacin. Da yake shari'ar Musulunci ta hana kashe dabbobi da tsuntsaye a wannan wajen ya sa suke shawaginsu sosai.

''Amma hakan ba ya kore cewa suna iya yin ibadar, tun da Allah a cikin Kur'ani mai girma ya fadi cewa: 'Ko wane abu da ka gani yana iya yin tasbihi ga Allah SWT amma ba lallai mu 'yan adam mu gane ba.' Allah ne ya bai wa kansa sani.''

Haka kuma, a shafin Facebook na hukumar masallacin mai suna Haramain Sharifain, an wallafa bidiyon da sako kamar haka:

"Wani mai ziyarar Masallacin Makka ya dauki wani hoton bidiyo da ke nuna gungun tattabaru na kewaye Ka'aba, sai dai yadda tattabarun ke kewaye dakin ba iri daya ba ne da yadda mutane ke yin dawafi a Dakin Ka'aba."

Wannan ya nuna cewa hukumar masallacin ta yi fatali da batun da wasu ke yi na cewa wata mu'ujiza ce yadda tattabarun ke dawafi saboda an hana mutane yi, ganin cewa su tattabarun suna kewaye Dakin Ka'aba ne ta hannun dama, yayin da mutane masu yin dawafi na kewaye dakin ne daga hannun hagu.

Da gaske ne shan ruwan dumi ko yin sirace da ruwan zafi na maganin coronavirus?

Dakta Nasir Sani-Gwarzo wani fitacce kan harkar lafiya a Najeriya, ya ce yin sirace da ruwan zafi ba ya hana kamuwa da coronavirus amma zai iya taimakawa wajen jika makogwaro.

"Ita coronavirus cuta ce da take yaduwa ta hanci ko baki sai ta gangara makogwaro inda za tai ta hayayyafa har ta shiga huhu" a cewarsa.

Dakta Sani-Gwarzo ya ce idan ana yawan yin sirace, makogwaro zai zama a wanke ba tare da wata majina ba kuma wannan na iya taimakawa wajen hana cutar yaduwa, amma yin siracen ba ya maganin cutar.

Haka kuma shan ruwan dumi na taimakawa makogwaro wajen tsaftace shi da wanke shi yadda ya kamata ko da mutum ba ya dauke da wata cuta, amma Dakta Sani-Gwarzo ya ce ''wannan ba shi zai hana kamuwa da cutar ba kuma ba zai yi maganin cutar ba ga wanda ya kamu.''

Da gaske ne cin kayan abinci masu inganta garkuwar jiki ba zai hana kamuwa da covid-19 ba?

Dakta Sani-Gwarzo ya ce wannan haka yake. Don mutum ya ci kayan abinci masu kara wa garkuwar jiki karfi, wannan ba zai hana cutar ta shiga jikin mutum kuma ta yi tasiri ba.

Sai dai ya ce garkuwar jikin za ta samu karfi da karsashin yaki da cutar idan an gina ta da sinadaran abinci masu kyau.

"Kamar mace ce ta haihu, ai ana dafa mata nama da sauran kayan abinci masu kyau, ko kuma dan-shayi da ake yi ko farfesu duk don su mai da karfin jikinsu, to kamar haka ne da garkuwar jiki."

Cin kayan abinci mai kyau ba zai hana kamuwa da cutar ba kuma ba zai warkar da cutar ba amma zai agaza wa garkuwa jiki," in ji Dakta Sani- Gwarzo.

Akwai sakonni da yawa a shafukan sada zumunta da ke cewa cin tafarnuwa na hana kamuwa da cutar coronavirus.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce duk da cewa tafarnuwa na kara lafiya, babu wata shaidar cewa za ta hana kamuwa da coronavirus.

Babu shakka cin kayan marmari da kayan lambu da shan ruwa a kai a kai na da muhimmanci ga lafiya, amma babu sahihiyar shaida da ke nuna cewa akwai abincin da zai iya hana coronavirus yaduwa a jikin mutum.

Wani sako da ke cewa shan lemon tsami da bakar hoda, wato baking powder na maganin coronavirus ba gaskiya ba ne.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce "kawo yanzu babu maganin wannan cuta kuma idan mutane suka yi hakuri, wannan cuta ce da ba ta da saurin kisa kuma ana warkewa idan aka kamu da ita."

Karin labarai masu alaka

Da gaske ne Dr Li Wenliang, wanda ya fara gano cutar ya yi wani bincike cewar akwai wasu sinadarai a shayi da ke maganin coronavirus?

A 'yan kwanakin nan, an yi ta yada wani sako musamman a shafin Whatsapp wanda ya fara da bayani kamar haka:

"Breaking News from CNN…", wato labarai da dumi-duminsa daga kafar sadarwa ta CNN.

A cikin sakon, an rubuta cewa akwai wani likita mai suna Dakta Li Wenliang wanda shi ne ya fara gano coronavirus, kuma wai kafin rasuwarsa ya yi bincike ya gano cewa sinadaran Methylxanthine da Theobromine da Theophyline da ake samu a cikin shayi suna maganin kwayar cutar coronavirus.

Haka kuma, sakon na dauke da bayanin cewa yanzu a China likitoci na bai wa masu dauke da cutar shayi sau uku a rana kuma shi ya sa har aka samu saukin yaduwar cutar a Wuhan, inda cutar ta samo asali.

Lallai sunan likitan da ya fara gano yaduwar coronavirus a birnin Wuhan na Lardin Hubai a kasar China, Li Wenliang kamar yadda aka rubuta a sakon na shafukan sada zumunta.

Dakta Li ya mutu a farkon watan Fabrairu bayan ya kamu da cutar, yana mai shekara 34.

Binciken BBC ya gano cewa babu shakka akwai sinadaran methylxanthines a shayi har ma da gahawa da cakulet.

Amma babu wata hujja da ke nuna cewa Dakta Li Wenliang ya yi bincike kan wadannan sinadaran da tasirinsu kan coronavirus- asali ma, Dakta Li likitan ido ne kafin rasuwarsa ba kwararre kan cutuka ba.

Sannan babu hujjar cewa likitoci sun fara bai wa marasa lafiya shayi sau uku a rana, kamar yadda sashen bincike na BBC na Reality Check ya gano.

Da gaske shugaban Rasha ya saki zakuna a tituna don hana mutane fita a matakin hana bazuwar cutar?

An yi ta yada wannan hoton na sama ana cewa shugaban Rasha Vladmir Putin ne ya saki zakuna har 500 a titunan kasar a wani mataki na hana mutane zirga-zirga don hana yaduwar coronavirus.

Watakila wasu da zummar wasa suke yada hoton amma tuni wasu sun yarda cewa da gaske ne.

Wannan labari karya ce tsagwaronta. Gwamnatin Rasha ba ta sanar da matakin rufe kasar baki daya wajen hana zirga-zirga ba. Hoton zakin an dauke shi ne tun a shekarar 2016 a Afirka Ta Kudu.

Da gaske an gano riga-kafin coronavirus kuma za a fara bayar da ita nan kurkusa?

An ci gaba da yada wani hoto a shafukan sada zumunta na wasu magunguna da allurai wadanda a jikinsu aka rubuta covid-19 vaccine. Daga saman hoton an rubuta sakon cewa "An gano riga-kafin coronavirus kuma nan da karshen mako za a fara yi wa mutane allurar".

Dakta Sani- Gwarzo ya ce wannan ba gaskiya ba ne.

"Samar da riga-kafin cuta ba karamin aiki ba ne. Ko da an gano riga-kafin, akwai gwaje-gwaje na musamman da ake yi kafin a fara bai wa mutane kuma a kan kwashe tsawon lokaci, watanni ma kafin a gama gwajin"

"Amma batun a ce za a fara bayar da shi nan kusa ba gaskiya ba ne," a cewarsa.

A wata makala da ya rubuta, Wakilin BBC kan harkokin lafiya James Gallagher ya ce ana nan ana bincike mai zurfin gaske don gano riga-kafin coronavirus.

Ya ce sama da riga-kafi 20 ake hadawa a yanzu, kuma a cikinsu akwai wadda aka fara gwada ta a kan mutane don gane ingancinta da girman tasirinta.

Yayin da wasu daga ciki kuma aka fara gwadawa kan dabbobi.

James Gallagher ya ce samar da riga-kafi na da matakai iri-iri shi ya sa ake daukar lokaci kafin a sami daya kwakkwara kuma mai inganci.

Haka kuma, idan aka yi dacen samar da riga-kafin kwanann nan, za a dauki tsawon lokaci kafin a iya samar da ita da yawa har ta isa duka kasashen duniya da ke bukatarta.

Hakan na nufin cewa ba za a samu riga kafin coronavirus ba sai a kalla nan da tsakiyar shekarar 2021.

Wasu sakonnin da ake ta yadawa na cewa Chloroquine, wani maganin zazzabin malariya, na maganin cutar kuma an amince a fara amfani da shi a matsayin riga kafi.

Wannan batu ba gaskiya ba ne, kuma sanarwar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi, mai cewa an amince a fara amfani da maganin a kan masu coronavirus ba daidai ba ce.

Hukumar da ke kula da ingancin magunguna ta Amurka ta musanta ikirarin Shugaba Trump, ta kuma ce ba ta kammala bincikenta ba kan tasirin maganin ga masu cutar.

Da gaske ne idan aka bude Kur'ani za a ga wani silin gashi, kuma idan aka jika gashin a ruwa aka sha yana maganin coronavirus?

An yi ta yada wani sako musamman a shafin Whatsapp da ke cewa wani ya yi mafarki da Annabi Muhammadu (SAW) kuma ya ba shi umarnin cewa ya bude Kur'aninsa a daidai Suratul Bakara, zai ga wani silin gashi guda daya, ya jika gashin a ruwa ya sha don yana maganin coronavirus.

Wannan sako ya yadu sosai har zuwa wasu shafukan kamar Twitter da Facebook kuma mutane da yawa sun yi ikirarin cewa sun yi kamar yadda mutumin ya ce an umarce shi da yi kuma sun ga silin gashin, sun jika sun sha.

Malaman addinin Musulunci da dama sun yi tsokaci kan wannan al'amari inda suka yi jan hankali da a yi watsi da wannan sako.

Abu Jabir Penabdul, wani malamin addinin Musulunci a Najeriya mai ba da fatawa musamman a shafin Twitter ya ce, shaidan kan zo wa mutane a mafarki kuma ya ce shi Annabi ne.

Malamin ya ce maganar gaskiya ita ce labarin wannan mafarki ba gaskiya ba ne, siddabaru ne na shaidanu.

"Ya ce ba abin mamaki ba ne saboda ko a lokacin yakin Badar shaidan ya yi wa Musulmai siddabaru, don haka kai wane ne da ba zai yi maka siddabaru ba? Dole ne mu zama masu mayar da hankali kan addini."

"Kuma kai wane ne za ka fito ka ce an yi maka wahayi a mafarki? Har kake kokarin karkatar da hankalin Musulmai a fadin duniya? Wannan ba daidai ba ne," a cewar Abu Jabir Penabdul.

Ya kuma yi kira ga Musulmai da su daina saurin biye wa jita-jita musamman kan abin da ya shafi lafiya da addini.

Baya ga malaman addini, wasu da yawa sun fito sun nuna cewa gashin da mutane ke ikirarin gani a cikin Kur'ani ba komai ba sai zaren da aka dinke Kur'anin da shi, ya ke zamewa ya shiga tsakiyar Littafin.

Da gaske sunan coronavirus ya samo asali ne daga Kur'ani, wato 'Kur'ani-virus don a ci mutuncin Al-Kur'ani?

Wani sakon murya da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta inda wani wanda bai bayyana sunansa ba, ke bayani kan asalin sunan coronavirus ya ja hankali sosai.

A sakon, mutumin ya ce malaman China sun yi kira ga mutanen kasar masu cin naman alade su daina saboda babu kyau.

Sai ya ce mutanen sun tambayi malaman a ina suka gano babu kyau cin naman alade sai malaman suka ce a cikin Al-Kur'ani, kamar yadda mutumin ya bayyana.

"Daga ambatonsu haka sai suka ce ai Qur'an virus ne, yana yi wa jikin mutum ta'asa. Ai an wulakanta littafin Allah, sannan ana tunanin Allah zai kyale mutane? To ai dole Allah ya saukar mana da masifa," in ji mutumin.

Sai dai binciken da muka yi ya nuna mana cewa wannan magana ba gaskiya ba ce.

Coronavirus ta samo sunanta ne daga kalmar harshen Latin inda 'corona' ke nufin hular sarki.

Kuma an sa wa kwayar cutar sunan ne saboda yadda idan aka haska ta a karkashin na'urar ganin kwayoyin halitta wato microscope, take da kamanceceniya da hular sarki, kamar yadda aka wallafa a Mujallar Nature.com.

Virus kuwa wata kwayar cuta ce da ke janyo rashin lafiya a jikin mutum da dabba kuma akwai virus iri-iri a duniya.

Ita kanta coronavirus tana da rabe-rabe da dama kuma Hukumar Lafiya Ta Duniya, WHO, ta yi wa coronavirus wadda ta zama annoba a halin yanzu lakabi da covid-19.

Da gaske ne an kirkiri coronavirus don a hana Musulmai ibada?

Coronavirus cuta ce da ake dauka idan mai dauke da ita ya yi tari ko atishawa, kuma idan ya shafi hancinsa ko bakinsa sannan ya shafi wani wuri zai iya goga kwayoyin cutar misali a teburi ko kofa ko bango.

Nau'ukan ibada a addinin Musulunci kamar sallah a masallaci ko yin dawafi sun kunshi cakuduwa ko matsuwa a kusa da juna a wuri guda.

Dakta sani-Gwarzo ya ce "Ba aikin ibada ba kawai, duk abinda zai kawo cunkoso na dan Adam a wuri guda ba tare da tazara ba, akwai barazanar kara yaduwar wannan cuta."

Ko a cikin gida ne tsakanin ma'aurata ko 'yan uwan juna, idan ba su ba da tazarar a kalla mita biyu ba daya na iya sawa dayan cutar.

Dakta Sani- Gwarzo ya ce "kamar gobara ce, idan wuta ta tashi a gida sai labule ya kama ai idan da darduma ko wani labulen a kusa da shi duk zai harba masu wutar. Kan a ce mene ne gaba daya gidan zai kama da wuta.

"Ita ma wannan cutar haka take, muddin za a rika zama kusa da juna babu abin da zai hana ta yaduwa, dama haka ta ke so," a cewarsa.

Amma ya ce idan mutane za su hakura da wasu abubuwan da suka saba yi na cuduwa a wuri guda kamar sallah a jam'i ko zuwa kasuwa mai cikowar mutane da dai sauransu, lallai za a shawo kan cutar nan ba da jimawa ba.

Dakta Sani- Gwarzo ya ce "Ita dama abin da take so shi ne mutane da yawa a wuri guda sai tai ta yaduwa, daga jikin wannan ta fada jikin wannan."

Don haka hikimar hana sallar jam'i da dawafi da yin musabiha ba salo ne na hana Musulmai ibada ba, illa dai kawai hanya ce ta hana yaduwar cutar a tsakanin mutane.

Haka kuma, ba a addinin Musulunci ba ne kawai aka dakatar da ayyukan ibada na taron jama'a, Fafaroma Francis ya daina gana wa da mabiya darikar Katolika a birnin Vatican saboda hana yaduwar coronavirus.

A yanzu ta wata katuwar talabijin da aka kafa a farfajiyar St. Peter's da ke Vatican yake gudanar da wa'azinsa.

Manyan malaman addinin Musulunci kamar Sheikh Dakta Ahmad Gumi da Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Sheikh Ali Isa Pantami duk sun fito sun yi kira ga Musulmi da su bi dokokin da hukumomin gwamnati da jami'an lafiya suka bayar kan hana yaduwar cutar. Asali ma, malaman sun ce wajibi ne bin doka a lokacin annoba.

Da gaske ne hukumar UNICEF ta Majalisar Dinkin duniya ta ce zafi na kashe coronavirus?

Wani hoto da ake ta yadawa wanda ke da tambarin Asusun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, na cewa shan ruwan zafi na kashe kwayar cutar coronavirus haka nan zama a karkashin rana.

Charlotte Gornitzka, wata jami'ar UNICEF ta ce duka wannan bayanin ba gaskiya ba ne.

Mun san cewa kwayar cutar da ke janyo mura ba ta cika rayuwa ba a waje lokacin zafi, amma ba mu san yadda abin yake da wannan sabuwar cutar.

"Zafin da zai iya kashe kwayoyin cutar nan kan kai maki 60 a ma'aunin celcius, wannan ba karamin zafi ba ne.

Amma wanke zannuwan gado da tawul da ruwan zafi na iya taimakawa wajen kashe kwayoyin cutar, amma ba zai yiwu a yi wanka da ruwa mai wannan zafin ba," a cewarta.