Coronavirus: Shin ya kamata matasa su damu?

    • Marubuci, Daga Rachel Schraer
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar Lafiya Ta BBC News

Kawo yanzu, bayanai kan lafiya a bayyane suke - hadarin kamuwarka da coronavirus ya danganta da yawan shekarunka. Amma Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi wa matasa gargadin cewa kar su yi wasa da lafiyarsu.

Dakta Rosena Allin-Khan, 'yar majalisa a jam'iyyar Labour kuma likita ta shaida wa BBC cewa coronavirus "ba tsofaffi da masu dauke da cutuka kawai take kamawa ba".

Tana magana ne bayan cutar ta kasha wani mai shekaru 18 wanda kuma ke fama da wata cuta a ingila. Yana daya daga cikin mutane masu karancin shekaru da cutar ta kasha a Burtaniya kawo yanzu.

Dakta Allin-Khan ta ce ta duba mutanen da a baya suke cikin koshin lafiya kuma wadanda shekarunsu bas u haura 30 ko 40 ba, da yanzu ke kwance a halin rai kwa-kwa, mutu kwa-kwai.

Ko ya hadarin yake ga shekaru daban-daban?

Tsofaffi sun fi shiga hadarin kamuwa da cutar. Masu bincike a Kwalejin Imperial da ke London sun gano wata alaka tsakanin yawan shekaru da yiwuwar tsananin cutar coronavirus. Kuma akwai yiwuwar cewa tsoffi za su bukaci kwanciya a asibiti idan suka kamu.

Kasa da kaso 5 cikin 100 na mutanen da shekarunsu ba su haura 50 ba ne ke bukatar kwanciya a asibiti saboda alamomin cutar amma ga 'yan shekaru 70 zuwa 79 alkaluman sun kai kaso 24 cikin 100.

Haka kuma, kashi 5 cikin 100 ne na 'yan kasa da shekaru 40 ne da aka kwantar a asibiti suke bukatar kulawa ta musamman, idan aka hada da kaso 27 cikin 100 na 'yan shekaru 60 da kashi 43 cikin 100 na mutanen da ke cikin shekaru 70.

Wannan ya karu zuwa kashi 71 cikin 100 na mutanen da shekarunsu suka haura 80, a cewar alkaluman da aka fitar a China da Italiya- kasashe biyu da cutar ta fi shafa.

Cibiyar kula da yaduwar cutuka ta Amruka ta ce bayanan farko-farko sun nuna cewa kashi 53 cikin 100 na mutanen da aka kwantar a asibiti sun haura shekara 55 inda hakan na nufin rabin kason matasa ne.

Amma idan aka duba wadanda aka kwantar a asibiti kuma aka ba su kulawa ta musamman, mafi yawansu tsoffi ne (kusan kaso 80 cikin 100 na wadanda suka mutu sun haura shekara 65).

Amma ba za a rasa matasa da cutar take yi wa mummunar illa ba, kuma wasu daga cikinsu sun rasa rayukansu.

A Italiya, kashi 0.4 cikin dari na mutanen da ke cikin shekaru 40 da suka kamu da cutar sun mutu idan aka hada da kaso 19.7 cikin dari na wadanda ke shekarun 80, yayin da a Amurka an yi kiyasin kaso 0.7 cikin dari na masu shekaru 40 suka mutu.

Darekta a Hukumar bincike kan cutukan da ake iya dauka na Amurka, Anthony Fauci, ya ce gaba daya mace-macen da aka yi a tsakanin tsoffi ne da kuma masu fama da wata cuta ta daban amma ya kara da cewa ita cutar 'virus' ba ta da alkibla.

"Akwai masu karancin shekarun da cutar za ta yi wa mummunar illa."

WHO ta ce "duk da dai akwai bayanan da ke nuna cewa wadanda shekarunsu suka haura 60 na cikin hadarin kamuwa da cutar, matasa, ciki har da kananan yara sun mutu".

Wani bincike da aka gudanar a China a kan kananan yara 2,000 da suka kjamu da cutar ya gano cewa, "duk da alamomin covid-19 ba su yi tsanani a kan yara ba, amma cutar ta bayyana karara a jikinsu".

Masu dauke da wasu cutuka na daban

Wasu cutukan na daban na tasiri a kan coronavirus komai yawan shekarun mutum.

Misali, akwai wadanda suka manyanta miliyan 4.3 a Burtaniya da ke da cutar numfashi ta asma, wacce ke kara jefa mutum cikin hadari idan ya kamu da covid-19- kuma wannan na shafar mutane da ke da shekaru daban-daban.

Wasu kuma na da cutukan da ba su ma san da shi ba.

Hana yaduwar cutar

Yayin da matasa ba su da hadarin shiga mawuyacin hali dalilin cutar, za su iya yada ta ga wasu.

Za su iya zama ba tare da wasu alamunta ba ko kuma alamomin ba za su fito sosai ba, amma kuma su iya yada ta.

Kuma da alama coronavirus ta fi kwayar cutar mura saurin yaduwa- duk mai dauke da cutar na iya yada wa tsakanin mutum biyu zuwa uku, a cewar kwararru.

Kowanne daga mutum biyu ko uku kan harbi mutum biyu ko uku, da haka har ta yi ta yaduwa.

Wannan na nufin mutane kalilan kan yada cutar ga dubban mutane.

Amma bayar da tazara na hana saurin yaduwar.