Sufayen da ba sa azumi a Senegal

Mabiya darikar Sufi Islam ba sa azumtar watan Ramadan

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Mabiya darikar Sufi Islam ba sa azumtar watan Ramadan
Lokacin karatu: Minti 1

Mambobin wata kungiya ta Sufi Islam da aka fi sani da Bye Fall a kasar Senegal, basa yin azumtar watan Ramadan kamar sauran Musulmai.

A madadin azumin, wadannan mutane suna ciyar da wasu ne kawai.

BBC ta yi tattaki domin kai musu ziyara a Touba, wanda shine birni mai tsarki na mambobin 'yan uwa na Mouride, wanda wadannan mutane suke ciki.

BBCn ta kuma zanta da wani matashi mai suna Babakar Sec da kuma Malaminsa Cheik Fal kan wannan lamari: